Sashe 84
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Barcin ya tafi ma" tace tana matsawa ta koma ɓangaren ta, tare da leƙen su Maama amma hankalin su bayi wurin gaba ɗaya ko haka suke ƙoƙarin nunawa.
Sai yaji kaman ya rungume ta yaga yaya zata yi. Amma gudun ta firgice mishi ya rabu da ita don a yanzu ma ya fahimci tsoron da take tattare da shi. Hannunta dai ba zata hana shi riƙewa ba don haka yana riƙe da shi har suka isa farfajiyar gidan Abbah.
Suhail ya fara ɓalle marfin motar ya fita sannan Maama ta fice itama suka rufo musu motar suyi sallama.
"Toh wifey saida safe ko? Ko in raka ki ciki ne?"
"A'a ka tafi kawai ga Maama nan? Zamu tafi tare." Tayi ƙoƙarin ɓalle marfin motan ta fice yayi saurin jawo hannunta da yake riƙe dashi ta dawo, amma har ƙofar ya rigada ya buɗu turawa kawai za'a yi ya wangale don haka ya ranƙwafa ya jawo ƙofar ya rufe ta kirif amma bai saki hannun kofar ba ga ɗaya hannunta na hagu cikin nashi na dama don haka ya zamto ya saka ta a tsakiya tana kallon shi a tsorace ganin kusancin dake tsakanin su shi kuma nashi idanun na kan laɓɓen bakin ta da ya sha jambaki yayi mishi kyau.
Numfashi ya ja ya saki hannun ƙofar ya koma ya zauna da kyau yana faɗin "bamu gama sallama ba saurin zuwa ina kike?"
"Ai na ɗauka shikkenan"
"Shikkenan? Haka aka ce miki mata da miji suke bankwana babu wasu kalamai masu daɗi yanda zai tsaya musu a rai su kwana da shi?"
Mata da miji! Ita har yanzu ji take yi a jikin a kaman ba gaskiya bane.
"Allah ya tashe mu lafiya yaya Yaseer, sweet dreams" tace tana ƙokarin ɗaura murmushi a saman fuskar ta.
"Sweet dreams my queen, I love you."
Haka ya tsura mata idanu yana mata irin kallon da yake jin yanzu an lamunce masa yayi mata, kallo har hanji. Har saida ta kasa jurewa ta mayar masa da "I love you too"
Ya sake sumbatan hannunta sannan yace "good night"
Sanin yanzu ya gama ta sake yunƙurin fita muryar shi ya sake dakatar da ita. "Baki ji ba"
Ta juyo ta dube shi tana kwaɓe fuska ita yanzu ko Maama da take tsaye take jiran ta bata san da wani ido zata kalle ta ba idan ta ga sun daɗe a mota, gashi ya saka glass ɗin munafukai sai ma ayi tunanin wani abun suke yi.
Kaman ya karanta abinda yake zuciyarta yace "sauran good night kiss ɗina"
Ta gwalale idanu kaman zata fiddo su waje. Ita dai ta shige su kodai wani abu ne ya sami yaya Yaseer?!.
Ɗan dariya yayi yace "just kidding, saida safe" ya daga mata hannu, wannan karon da tayi yunƙurin fita bai dakatar da ita ba.
Maama ganin tana fitowa ta wangale mata ƙofar da kyau ta fito sannan ta rufe tana binta a baya tana riƙe mata riga har ciki.
A can ma iyaye da goggoni na jama'are sai da suka tsayar da ita suka yi hoto, aka musu da Umma ma, goggo Halime da amarya sai ƴan uwan kakanta Kamalu wanda suke jini ɗaya da suka rage a duniya. Sai da suka ƙara gajiyar da ita sannan Umma ta janye ta zuwa ɗakinta ta bata abinci ta tabbatar taci sannan ta saka ta tayi wanka a ɗakin itama tayi mata amfani da tanadi na musamman da tayi mata sannan ta bata kayan barci da hijabi ta saka ta koma ɗakin da kawayen ta suke, sai a lokacin ta samu Safina ma ta dawo.
Suka ɗan taɓa hira kafin ta kwanta don haka da suka yi sallan asuba ma saida ta koma Kuma aka bar su suka yi barcin sai wuraren tara aka buga musu ƙofa aka shigo musu da abinci.
Zuwa 11 kuwa ta shirya cikin rantsatstsiyar leshin ta suka sake wasu hotunan da kawaye a ɗakin, kana aka rufe mata fuska suna zaune duk mai son ganin amarya sai ya leƙo. da ta gaji ta saka aka garkame ƙofar ta buɗe kanta ta sha Iska
Ta ɗauki waya tana leƙawa yanar gizo. WhatsApp ta fara shiga ta duba status ɗin Yaseer. Farko hoton shi ne shi kaɗai na ɗaurin aure ya rubuta Caption kamar haka _Not just dressed like a king, but also blessed with a queen. Alhamdulillah for today, alhamdulillah for her_
Tayi murmushi tana zooming hoton ta kare masa kallo tun daga sama har ƙasa kafin da kyar ta tsallaka hoto na biyu domin ba wai gajiya tayi da ganin shi ba.
Na biyun kuma hoton su tare ne wanda suke kallon juna tana jin hannun shi a bayanta kaman yanzu aka ɗauka. shima ya saka Caption kamar haka
_Two souls one heart one journey. Y'all meet my queen, rabin raina. Hafsatu Reina Gimbiya mai kwarjini, farin cikin da zuciyata ta daɗe tana nema. Reina, wadda idan ta yi dariya sai haske ya cika zuciyata. idan ta yi murmushi, sai nutsuwa ta ratsa raina."_
Ta kuwa kara faɗin murmushin dake kan fuskar ta.
Dake ma sun fara shirin buɗan kai tun da wuri sai babu wanda ya sake zuwa ya buga musu ƙofa har suma suka samu faragar shirin buɗan Kan.
Yaseer sai a lokacin ya ga Aicha da Umma ta sako ta a gaba su zo suyi manni, shi bai ma san tana gidan ba ya ɗauka ta tafi gida ne ko Niger tunda ta dauki hutu a office itama.
Bai bari an daɗe a buɗan kan ba ya saka Muhammad ya sallami masu ganga Safina kuma ya sakata ta shige da amarya kada a gajiyar masa da ita shima ya sulale ya gudu yana hamdalan daga yau dai Shikkenan an gama zasu huta.
Ana maghriba Umma taje da kanta ta ɗauko ta zuwa ɗakinta ta sake mata irin shirin jiya wanda ya fishi ma sannan ta shirya ta a cikin wani haɗaɗɗen yadi mara nauyi wanda aka yi masa ɗinki mai sauƙi amma ya karɓe ta sosai, ita ta ɗaura mata zani da ta fahimci ba iyawa tayi ba. Sannan ta rufata suka fito tana raɗa mata addu'o'in da zata ke nanatawa har su isa da kuma wanda zata shiga gidan da shi sannan ta zaunar da ita a tsakar carpet ɗin parlon ƙasa su goggo Halime da suka saka ta a gaba suka shiga ƙara mata nasiha har sai da suka ga tana niman saka musu kuka tace a ɗauke ta su tafi bata shirya mijin su yazo ya sake ta a daren nan ta saka masa amarya kuka ba.
Reina ta so ta lura bata ga su Zaheera ba, Bata sani ba ashe yau kam Alhaji Tahir ya hana a bar Zahra ko Zaheera ko iyayen su shigowa gidan baki ɗaya, domin ya san mutannen nan masharranta ne babu yanda za'a yi ace wai zuwa taya su murna shine suke ta sintiri.
Anyi a kan da Safina zasu tafi a mota ɗaya da Aunty Zeenat amma da Safinan ta leƙo taga Suhail ne mai tuƙi sai ta juya ta koma babu jimawa kuma Maama tazo ta shiga suka ɗauki hanyar gidan Yaseer, gidan Reina.
Har addu'an shiga banɗaki tayi kafin su isa tsabaragen fargaba. Da zata fito daga mota Aunty Zeenat tace tayi bismillah ta sauƙo da ƙafar dama kafin ta taka ƙafar ta a gidan. Da suka je shiga ma saida suka tsaya tayi addu'o'i sannan tayi bismillah ta shiga da ƙafar dama.
Daga nan ba zata ce ga abinda yake faruwa ba har su Safina suka rungume ta suna mata sallama zasu je a maida su gida, tana sauraron su tana biye musu har dariya ta san tayi amma abubuwan da ke faruwa bayi shiga kanta kuma ko a gaba aka ce ta tuna bata jin zata iya.
Aunty Zeenat ta raɗa mata wasu maganganu a kunne da take jin shi kaman kukan sauro kuma da ta tambaye ta wani abu ta samu kanta da gyaɗa kai.
"Good, idan akwai wani abun kada ki kira Ummi ko umman shi, ki kira ni zan zo in taimaka miki kin ji?" Ta sake gyaɗa kai.
Aunty Zeenat ta mike tsaye tana gyara zaman mayafinta. "Gidan ki yayi kyau Reina Allah yasa daga cikin sa sai kabarin ki"
" Fatan mutuwa kike mun?"
"Hmm ashe dai bakin bai gama mutuwa ba tukunna, babu komai idan na dawo zan tambayeki ki maimaita."
Ta saɓa jakarta tayi mata sai da safe tayi gaba.
Can jimawa wurin minti 20 taji shiru, yaya Yaseer bai shigo ba har yanzu gashi motsin da take ji na mutane a cikin gidan ma ya tsaya, kada dai ita kaɗai suka barta kafin ya samu isowa?.
Sauƙowa tayi babu shiri daga gadon, ta saka takalminta ta nufi ƙofa zata je nimo shi tunda ta manta ta bar Safina ta tafi da wayanta.
Buɗe ƙofar tayi ta saka ƙafa zata fita sai ji tayi tayi karo da ƙirjin mutum, bai ɓata lokaci ba ya zagaye ta da hannun shi ya ɗan rankwafo ya rungume ta da kyau sai a lokacin ƙamshin sa ya shiga hancinta Saboda nutsuwar da ya sauƙan mata ba tare da ta sani ba.
Tayi shiru tana sauraron bugun zuciyar shi.
"Reina". Ya kira sunanta.
"Uhmm" ta amsa.
"I made it. Finally" ya ɗago ta yana saka fuskarta cikin tafin hannuwan shi. "I Finally did it. Na mallaki wannan zinariyar" yace da wani murmushin da ya ƙawata fuskar shi sosai kuma bata taɓa ganin yayi irinta ba.
"Ina kaje ka barni toh?" Tace tana sauƙe hannun shi daga fuskarta gwamma dai ta rike masa su kaman yanda yake so ya sabar mata.
"Na sallame su ne na rufe mana gidan. Kina nima na ne?"
"Yanzu daga ni sai kai a ciki?"
"Yes, sai security daga ta waje."
Ta sauƙe numfashi kawai ba tare da tace komai ba sai shine yace " zo mu fara daren mu da abinda Allah yake so sai ki sauya kayan nan muci abinci."
"Ai babu nauyi" tace tana shafa zanin kayan.
"Still ba kayan barci bane za'a sauya shi."