← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 117

Sashe 58

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hello uncle Bilal"

"Yauwa doll ga yaron ki nan da mummyn shi zaku gaisa" muryar shi ya dawo, Amma kafin tace wani abu sai jin muryar Mufid tayi yana "Aunty good afternoon"

"Murmushin ƙarfin hali Reina tayi ta ɗan daga karsashin muryar ta tana amsawa da "Afternoon my boy, how are you"

"Fine", ya amsa sannan taji muryar shi da nisa alaman ya ɗaga wayan daga kunnen shi yana faɗin "ga mummy"

Abinka da harshen Balarabe har wani garɗi Reina taji muryar matar tayi mata a ɗan gaisawan da suka yi da turanci sama-sama ta mayar da wayar ma Uncle B.

"You were saying something?" Ya tabbatar mata bai ji abinda ta faɗa ɗazun ba don haka sai tace

"No shikkenan, ya wuce" a ranta tana Allah sarki bawan Allah ashe yayi niyyar faɗa mata taso katse masa hanzari, to ita ina ruwanta da matar shi ma tunda ba a kanta zata zauna ba?

"No doll, please ki faɗa mun, kin san bani son ganin ki a cikin damuwa"

"A gaban Mummyn Mufid ɗin?"

"na dawo ɗaki, moreover ba wani Hausa take ji ba Idan nayi a gaban tan ma, kaman yanda kema baki jin Larabci"

"Wa yace maka? Naje islamiyya nima fah"

Dariya mai sauti yayi yace "zaku iya karawa kenan, ni da har ina cewa zan raba muku gida? Amma tunda za'a yi min competition ɗin larabci zan haɗe ku wuri guda a sauƙaƙe"

Fisabilillahi ta ina za'ace zata iya karawa da masu abu? Yanzu ma ba wai ta gama nitsar da zancen tana da kishiya bane a ranta balle yana ƙara tuna mata kamanninta da kalaman shi. "Ni bautar auren ka dan zauna ba competition da matar ka ba"

"Hakane fa my dear Hafsah. Allah ya gwada mana ranar very soon, I'll be the happiest man on earth" yayi nasaran sanya ta murmushi sannan ya ɗora da "toh yaya program ɗin kun?"

Bai san cewa su Yaseer ne suka yi sponsoring ba shiyasa har yake tambayar ba'asi, tun da ya gwada ɓacin ran sa a kan contract ɗin snacks da ya bata ta zaɓi ta fara ɓoye mishi Abinda ya shafi yaya Yaseer, amma a hakan ma sai da ya ƙare yayi musu mummunan fahimta.

"Yau an gama"

"Aikin da ya saka kike share ni shima kin gama ko?"

"In sha Allah" ko ba komai zata huta da mita ya koma mata Uncle Bilal ɗin da ta saba da shi.

"Masha Allah and I hope this will be the last ba zaki sake karɓan wani ba. Ko ke kike son ci ki faɗa a siya miki amma zama snacks vendor ba girman ki bane Amaryar Doctor Bilal"

Tunani take yi shi daman sana'a har wani level yake da shi?

Yau dai sun ƙare wayan cikin girma da arziƙi, sun sha hira tama manta da yana gida tare da matar shi don sai da aka kira sallan la'asar ta tuna ko azahar bata yi ba.
.....

Yaseer ya dawo da fata mai karfi na cewa Reina zata fahimci abinda yake guje mata. Sabila da haka ana Isha ya ɗaga waya da kan shi ya kirata tazo ya ji yaya suka ƙare da Uncle B.

Da plate ta shigo wanda ta zuba meatpie da pepper chiken ɗin da Ummi ta turo mata a cikin abinda yayi saura. Ta ajiye masa a kan table da murmushi sannan ta zauna ta fuskace shi.

"Ga abun mun Yaya Yaseer na san baka ci ba, su Ummi kuma sun yi Godiya sosai"

"Na ci, amma Nagode. Kin tambayi Bilal a kan maganar da muka yi ɗazu?.

"Eh, yace mantawa yayi" ta amsa kanta tsaye da ƙarya.

"Ya manta da mene ɗaya?" Fatan goshin sa ya tattare a dalilin yamutsa fuska da yayi cikin rashin fahimta.

Sai ta fara kame-kame "no daman wai yana da shirin sanar da ni daman ya bari ne sai lokacin da ya dace"

"Sai lokacin da ya dace yaushe? Matar da ta kusa haihuwa Hafsat? Ko ce miki nayi jiya ya maida ita? Suna tare tun yana UK ya maida ita ɗakin ta kina nan kina shirmen banza. Idan kin ga dama kiyi wa kan ki ƙiyamul layli idan kika biyewa son zuciyar ki kuma ke ta shafa tashi ki bani wuri"

Jiki ba ƙwari ta fito daga study Room ɗin ɗauke da plate ɗin ta. Shikkenan zasu koma gidan jiya, yaya Yaseer zai sake fushi da ita, sai taji baki ɗaya itama abun ya fita mata a kai, kuma daman ta kai masa rabon ta ne idan yaci ya bar mata saura, tun da ta bawa sauran mutanen gidan ladan taya aiki shine bai samu ba.

Kitchen ta tafi ta ajiye sannan ta koma ɗakinta.

Ƙarfe 12 na dare ta samu kanta tana jiƙa rigan pillown ta da hawaye, zafi take ji a ranta wanda take ganin bata da dalili saboda ba auren Uncle Bilal tayi ba tukunna a wani dalili zata yi kishi da matar shi bayan ita tana can ta kwantar da hankalin ta? Amma da Uncle Bilal ya faɗa mata ta shirya ma zuciyar ta zaman su tare tuntuni da ta tabbata abun ba zai dame ta haka ba.

Washegarin kuwa sai gashi ya shigo gari. Kuma bayan ya zo gida sun yi hira ya matsa mata da sai sun fita da daddare.

Idan ta faɗa ma Umma ko Daddy na farko ma ba zasu barta ba idan da dare ne, kuma koda ace zasu bartan za'ace sai ta ɗauki Maama, ita kuma ko rakiyar ƙofar gida bata sake gayyatar Maama tunda ta ƙware a munafurci.

Yanzu damuwan shine yanda Za'ayi a barta ta fita daga gidan a cikin daren.
Ta ɗaura ta warware amma ta kasa samun mafita don haka ta ɗaga waya ta kira Safina ta zayyane mata abinda yake faruwa sannan ta nemi taimakon ta.

"Wonders shall never end!. na ɗauka idan kina tunanin aikata irin haka nice wacce zaki fara ɓoye wa, ashe kallon mutuniyar Banza kike mun Hafsatu Tahir Kamal. Yanzu har namiji ya kai kiyi dodorido ma iyayen ki?"

"Feenah Please, na yau kawai daga yau ba za'a sake ba dan Allah, Wallahi ran Uncle Bilal zai ɓaci ne sosai kuma tun daga Kaduna ya taso ya zo fa Saboda ni"

Safina tace Hmm "yanzu idan na biye miki muka yi ƙarya muka je wani ya gan mu yazo gida ya faɗa ko wani mummunan abu ya faru ko muka yi hatsari ko ma Allah ya ɗauki ran mu da wani baki zamu yi bayanin niyyar mu na yau ne kawai? Idan ran Uncle Bilal ya ɓaci sai me? Ubanki ne shi ko mijin ki? Da yana da wani matsayi a wurin ki ai ba zaku tsaya niman izini ko kame-kame ba sai dai a ganku kun je kun dawo. Shikkenan ki guji ɓacin ran Uncle Bilal ki jawo ma kan ki ɓacin rai kuma na samu labarin kin fita a daren nan sai na faɗa ma wanda kike tsoron wurin da kika je shashasha" daga nan ta kashe wayar ta, Reina kuwa ji take yi kaman ta ɗaura hannu a ka ta fasa ihu.

Har kayan da zata saka ta fito da shi escape plan kawai take nima dama ga kuma kiran Uncle B da ya fara ziyartar wayar ta.
A karo na farko da tana kallon kiran shi ya jero mata har guda 4 wani na bin wani suka gama ringing suka mutu.

Sai saƙo ya shigo a na biyar ɗin ta ɗaga ta duba abinda yake cewa "Nagode Hafsah" shine kawai abinda saƙon ya ƙunsa.

Tsoron sauƙa wurin Yaseer shima a yau ɗin ya saka ta kunna Kdrama din da Safina ta tura mata tayi WiFi casting tana kallo ta TV har ya ɗan ɗauke mata damuwa kaɗan saboda comedy drama ne wai Mr Queen. Ta sani cikin ƙanƙanin lokaci zasu shirya da Uncle B idan ya gama mitan shi, Amma yaya Yaseer fa? Kwata-kwata bata son tayi dalilin da zai saka ran shi ɓaci ya share ta koda na second ɗaya ko dan zaman da suke a gida ɗaya tana ganin shi tana jin nauyin laifin ta.
.....

Bayan Shari'a na farko a tsakanin mutanen da suka bawa Alhaji Tahir bashin kuɗi ,Alhaji Tahir da Alhaji Salisu a ɗaya bangaren, sai gashi wai Alhaji Salisu ya ɗauko Alhaji Kalabu sun zo wurin Alhaji Tahir.

A yau an bar su sun shigo gidan su Yaseer saboda shima Alhaji Tahir ɗin yana son ganin su dama, yana son ganin ɗan uwan shi da ya tura mutane su markaɗe shi da mota Saboda dukiya, yana so ya ga iya rashin kunyar Alhaji Salisu.

A ɓangaren Abbah aka sauƙe su, suka zauna su biyar suna fuskantar juna.

"Yauwa Tahir, nace mana mai zai hana mu haɗa kai domin muyi nasarar kayar da mugayen mutanen nan? Saboda sun shigo da cuta a cikin lamarin su, idan ba haka ba sun riɓa yawan kudin da ka karɓa sau goma kuma suna da audacity ɗin maka ka a kotu?" Alhaji Salisu kenan yake tada jijiyoyin wuya.

Alaji Abdou yace "toh idan sun maka shi a kotu kuma kai naka a wanne?"

"Ah ah! Nawa a wanda yayi mishi hanya mana saboda ban san su macuta bane ba, ko sai in zuba ido a cutar da ɗan uwana kake nufi?" Ya hayayyaƙo ma Alaji Abdou wanda yayi murmushi kawai.

"Yaya Salisu ina kwana, sai yau Allah ya haɗa fuskokin mu bayan shekaru 7, na san baku yi tsammanin sake ganina ba ko? Har kai yaya Kalabu"

Gwada Kamal Alhaji Salisu yayi "ka tambaye shi, mun zo ƙofar gidan nan yafi abinda yafi Amma haka yake shanya mu a bakin gate kaman wasu maroƙa, ka san shi matsiyaci daman bai iya samun wuri ba kuma ina da tabbacin wannan arziƙin da yake tutiya da shi taka ce. Kai Kamalu kaman ba jiya kake zuwa gidajenmu mu sallame ka da abinda ya samu ba, amma tunda ka samu Tahir ya sakaya ka shine har wuyan ka yayi kauri" ya karashe yana gwada Abbah da yatsa wanda shima murmushi kawai yayi.
Chapter 58 · 0% Book details