← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 117

Sashe 83

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya gyara tsayuwan shi a gefen ta kafaɗan su na gogan na juna aka dallare su da flash na farko. Sai kawai jin hannun shi tayi a gadon bayanta, lokaci ɗaya wani abu ya tsirga daga bayan yayi hanya biyu, ɗaya ya sauƙa zuwa ƙafafunta ɗaya ya tafi sama har tsakar kanta. Da sauri ta juya ta dube shi tana ware Ido lokacin da shima ita yake kallo a cikin ido.
Mai hoto has found his moment don haka ya fara dalle musu fuska da haske ba sararawa, Yaseer ya sake mata kasalallen murmushi tare da janyo ta jikin shi a sukwane ta daɗa mannuwa da shi "welcome into my life umry, welcome to Forever" ya raɗa mata cikin kunnen ta sannan ya mayar da idanun shi jikin Camera.

"Amarya baki kallon nan, angon ki haɗaɗɗe ne mun yarda" cewar mai hoto don haka a kunyace ta mayar da idanunta gaba yaci gaba da ɗauka haka ma sauran ƴan parlon suka cigaba da ɗaukan su a wayoyinsu su samu na ɗaurawa kafin na mai hoto ya zama ready.

Hoton lokacin da aka ɗauka da kawayen amarya da wanda suka kalli juna Safina ta ɗaura a Whatsapp status da Instagram feed with the caption _" "Behind every king and queen, there’s a kingdom that rejoices 💃🏽🕺🏽.
Alhamdulillah for family and friends who made today beautiful."
#SquadGoals #REINAWedding #LoveStoryMadeInHeaven

Tana ɗaurawa ta tura ma Muhammad hoton shi kuma ya tura ma Yaseer da Suhail da Aicha kafin ya ɗaura a nashi status ɗin.
.
.
A gidan Umma yanda ake kan karɓan baƙi suma, Aicha ta kashe wayanta ta rufe kanta a ɗaki shiyasa bata san wainar da ake toyawa a gidan da online da ma can nasu gidan ba.

Ana yin La'asar kuma aka tattari gungun jama'ar da zasu je ɗauko amarya.

Ita kuma tana gaban Alhaji Tahir dake ƙoƙarin hana kan shi taya ta kukan da take yi.
"...Allah ya jiƙan Fauzah, Hafsatu mahaifiyar ki macen kirki ne gaba da bai, itace abinda ake kira da mata ta gari. A zama na da ita na shekaru goma sha ɗaya zan iya ƙirga miki sau nawa ta ɓata min. Ina so idan da hali ki fita, yanda kika kasance sanyin idaniya na ina so ki cigaba da faranta min ta hanyar yiwa mijin ki biyayya da iyakar iyawar ki, ina so Yaseer yayi alfahari dake fiye da ni kaina. Ki daure, ki jure, zaman aure haƙuri ne. Allah yayi muku albarka baki daya." Daga haka yayi alama da hannu masu jira su zo su ɗauke ta su tafi.

Aka miƙar da ita a gaban shi tana kuka tana sheshsheƙa amma tashin da zata yi sai ta ranƙwafa ta rungume shi da kyar aka raba su.

Da aka fito waje Maama ma tana nata kukan ta ƙaraso suka rungume juna suna ƙara sauti. Safina dai a wannan karon bata zubda hawayenta ba tunda gidan ƙauna da mutunci zata raka ta kuma duk lokacin da tayi kewarta zata iya zuwa ta ganta.

Mutanen da suka sha mamakin yanda ta ɓare baki take kuka da yawa suke.
Wa'inda suka zo ɗauka kuwa tana kukan da komai suka dannata a cikin mota suka tafi da ita.

Gidan Umma aka kaita aka basu tsohon ɗakin Yaseer ita da ƙawayen ta. Haka ta kwanta a kan gadon shi tana sheshsheƙa tare da shaƙar ƙamshin shi da ya kama pillown da yake kwanciya a kai. Ganin abun nata ba na ƙaran bane ƙawaye suka fita sha'anin ta suka cigaba da hirar su abun su.
Kafin maghriba sai gashi har ta ware ta tsomo bakinta a ciki Maama ta dinga mamaki don ta ɗau kwana zata yi tana yi yanda ta faro shin nan.

Aka basu abinci da kaji da kayan motsa baki masu rai da lafiya suka kora suka yi Sallah sannan mai kwalliyan amarya ta ƙaraso aka fara shirin dinner.
.
.
.
Ana buɗe bayan motar ta jiyo kamshin sa amma yafi wanda ta saba ji daɗi. Safina ta gyara mata ƙasan gown ɗinta bayan ta shiga sannan ta gaida Yaseer dake zaune a ɗaya ɓangaren ya amsa ta rufo musu ƙofa.

Suhail yayi saurin zuge glass ɗin window yana tambayar ta ina Maama? Kafin ta wuce.

Ta gwada cikin gida da hannunta da ya sha lalle itama "yanzu zata fito"

"Okay ke a wani mota zaki tafi?" Tayi masa nuni da motar Muhammad dake gaban nasu "na Abban sabrina" ganin Maaman da yake nima tana fitowa ta wuce ta shiga gaban motan Muhammad ta rufo ƙofa.

Babu jimawa suka ɗauki hanyar tafiya, har lokacin Reina bata juya ta kalli Yaseer ba, ta kafe idanunta ta jikin windown da ya kasance tinted amma presence ɗin shi take ji ya cika motan, ga Maama da Suhail suna zaman kurame suma sai ɗan sautin waƙar Hafsah na ali jita dake tashi.

Hannunta da ta ajiye a saman cinyar ta kawai ta ji ya kamo yana murzawa cikin nashi ai kuwa babu shiri ya samu ta dube shi.
"Wifey, ina wuni"

Mayar mishi da gaisuwan tayi tana ƙoƙarin janye hannun ta daga riƙon shi amma sai ya sarƙafe yatsun su waje guda kana ya sunkuyo ya sumbaci bayan hannunta.

"Daman na sani, lallen amarya domin ke aka ƙirƙire shi" yanda yake magana da wani muryar da bata san shi da shi ba duk munafurcin Maama da Suhail basu isa su jiyo shi ba.

"Please ka sake ni yaya Yaseer" tace tana cigaba da ƙokarin zame hannunta daga nashi ganin har sun iso hall ɗin event ɗin.

"Saboda me? Yau ranar riƙe hannu na duniya ne, kowa ya riƙe halalin shi"

Bata san da gaske yake yi ba sai da taga sun fito daga motan a haka sannan yana riƙe da hannunta har suka nufi cikin hall ƙawaye shida da abokai kwatankwacin haka na biye da su. wannan ankon dai su Zaheera basu samu daman yi ba don na safiyan ma dake a nan kasuwa suka cire shiyasa suka je suka nimo suka ɗinka.

Suka yi musu rakiya har wurin zaman su sannan aka fara gabatar da taro. Kallon girma da tsaruwan wurin da kuma adon mutanen cikinta yara da manya Reina take yi lokacin da aka kira su tsakiyar fili a karo na farko ango yayi ma amaryar sa manni kaman ba zai bari ba, yana gamawa ya sake riƙe hannun kayan shi.

Aka kira dangin amarya da ango su zo kowa ya gwada tashi bajintar, aka cigaba da gabatar da taro yanda ya kamata.

Sosai kuma aka ci aka sha cikin farin ciki, Ganin taro ya gagara ƙarewa har wuraren sha biyu ango ya ja hannun amarya suka ƙara gaba idan sauran sun gama sa biyo su daga baya.

~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

99

Bayan sabuwar motar shi da Suhail ya kawo su ya buɗe ya saka ta sannan ya durkusa ya gyara mata ƙasan riganta ya shiga ciki da kyau kaman yanda yaga Safina tayi mata ɗazu. "Wifey bari na dubo ƙannen ki suzo mu tafi ko?" Ta ɗaga mishi kai domin ta gaji ga tsinin takalmin ƙafarta ya saka sai ciwo suke mata.

"Menene?" Ya tambaya ganin yanda take yamutsa fuska.

Cikin ƴar murya tace "da muka tsaya sosai ne shine kafan yake min zogi"

Ya ɗan ɗaga rigan da ya rufe takalmin sannan ya riƙo ƙafanta yana zare mata takalmin don ya duba.
Ta yi ƙoƙarin jan baya da ƙafan amma ko gezau. Ya san dama zata yi ƙoƙarin ƙwacewa shi yasa bai mata riƙon wasa ba ba kuma yanda zai yi mata zafi ba.

Ya saka tafin ƙafanta a cikin hannun shi kana ya shiga matsa mata, musamman zara-zaran yatsun ta da suka daɗe suna ɗaukan idanun shi, yau gashi sai yanda yayi da su.

Har wani lumshe idanu take yi Saboda yanda take jin daɗin tausar to shi, ta kwantar da kanta a jikin seat ta yi shiru.

"Umry, ko zamu wuce gidan mu ne kawai kiyi hutawar ki a bar sauran bikin nan? Daman ni ba so nake yi ba"

Ta ware ido tana mamakin yanda yake zancen nan da iya gaskiyar shi.
"Ka rufa ni ka saya ni yaya Yaseer, dama sun ce bani da kunya yanzu sai ayi mana kuɗin goro"

"Kina so mu wuce ko baki so? Shine kawai damuwa na, mutane ba zaka iya hana su magana ba"

Ta samu ta zame ƙafanta daga hannun shi tana furta kalmar godiya kana tace "a can ɗin ma zan huta kaga mun tara mutane idan muka tafi haka nan zai yi wani iri.

Ya miƙe tsaye da "toh, anything you say my queen. Barin je in dubo Suhail sai ya zo mu tafi ko?" Ta gyaɗa kai ya jira ta gyara zamanta da kyau ya rufe mata ƙofar Sannan ya nufi hall ɗin. A daidai mashigar ya gamu da Suhail yana fitowa Maama na biye da shi.

"Amma baka ga ka aje mutane bane zaka yi zaman ka? Idan kuma wani abun kake yi ka bani key ɗina in kai Matata gida".

Suhail wanda shima kaman ran shi a ɓace yake ya danne ya bashi haƙuri yayi gaba ya bar Yaseer da Maama a wurin wanda tabi bayan shi da kallo.

"Wuce muje" Yaseer yayi mata nuni ta fara takawa kafin ya taho a baya Amma a haka sai da ya riga ta shiga cikin motar ya samu Reina tana barci daga zaune.

Bayan sun ɗauki hanya Ya ɗan taɓata ta buɗe ido. "Zo ki kwanta a nan" ya buɗe mata hannun shi sai ta samu kanta da murmushi yaya Yaseer dai idan yaso wasa abun sai shi.

Bata gama tunanin ba taji hannun shi a gefen kunkumin ta ya janyo ta suuu a kan leather seat ɗin shi mai tsantsi kaman gown ɗin jikin ta ma. "Ki kwanta kiyi barci Idan muka isa zan tashe ki"

Tuni idanunta suka soye kaman tasoyu. Ita fa ta lura kaman a yanda ta ɗauki yaya Yaseer shi ba a haka ya ɗauke ta ba. Shi da a lokacin kallon da ya wuce iyaka ma bai iyata ba Amma daga Safiya zuwa yanzu kawai ya taɓa ta yafi sau biyar.
Chapter 83 · 0% Book details