Sashe 73
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tayi ƙwafa tana mika ma Safina wayanta. "Gashi dan Allah nima buɗe min wannan din har da tiktok ɗin ma"
"Ni?!! Ki je ki tada ma yaya Yaseer zaune tsaye yace ni na kashe mishi aure?"
"Please mana, gani kawai zan dinga yi nima"
zaman gidan Hajiya Hauwa shi ya cire mata sha'awar social media don ko datan da zata hau bata da shi, na WhatsApp ma uncles ɗinta ƙannen Aunty ko safinan ce ke siya mata, shiyasa yanzu da take samu a ɓagas har daga wurare biyu ma bata san yaya zata yi dasu ba tunda ba iyawa tayi ba, sai dai idan taga datan zai yi expire tayi kyauta dashi.
"Wani suna za'a saka miki?" Safina ta tambaya bayan tayi mata installing ɗin su.
"Ki saka Reina"
"An riga ki ɗauka"
Ta gwada mata wata mai irin sunan sai ta ɗan ware ido da mamaki.
"Ni da sunana? Kenan ba zan iya amfani da shi ba?"
"In saka miki Reina da ƙarshen numbern ki?"
"A'a ki saka Hafsat Reina"
Cikin Sa'a ta saka aka samu ya ɗauka.
"Gashi sai in gwada miki ki karasa sauran".
Ta miƙo mata wayan don ta zaɓi profile sai ta samu wani hoton Cartoon ɗin Masha a kusa don haka ta zaɓe shi.
"Ki bar sauran kiyi min searching ɗin yaya Yaseer Please"
Fasa saka mata bio Safina tayi tana dariyan ƙeta ta koma search bar ta rubuta username ɗin Yaseer sai gashi ya fito kuwa da verified badge ɗin shi.
Ta karɓa ta danna mishi follow. Ta mayar ma Safina wayan itama tayi following ɗin kanta. Reina tace ta buɗe mata tiktok ɗin ma, shi bata tsaya ma saka profile picture ba ta danna mishi follow.
"Tunda burin ki ya cika tashi muyi Sallah muci abinci mu cigaba da karatu tunda shi Ummah ta turo ki".
daga lokacin duk abinda take yi tana duba wayanta har suka ci abinci suka ɗora da karatu duk bayan minti sai ta duba wayan kaman mai jiran wani abu, ko itama bata san me take dubawa ba kawai gani take yi kaman Yaseer zai sake ɗaura wani hoton mata su sake yayyame shi sai ta gani idan zai faɗa musu yana da matan da zai aura ko ba zai faɗa ba.
Takaicin ta ya saka Safina ƙwace wayan tana gaya mata maganganu wai su sabon shiga ba'a iya samun abu ba.
Can bayan hankalin su ya koma kan karatun sun ɗan yi mai yawa Safinah ta ɗago wayan Reina duba lokaci Amma mai zata gani?
Yaseer yayi following ɗin Reina back.
Ihu ta saka ta miƙe a kan guiwowinta ta juya tana gwada mata.
"Ke gatan matasa yayi following ɗin ki back, har da saƙo ya turo!" Safina ta mata albishir tana diri.
Da mamakin yanda aka yi ya gane itace ta karɓa ta shiga don duba saƙon.
'ƴammata na' shine kawai abinda yace amma saida Reina taji wasu abubuwa masu fuka-fukai suna mata yawo a ciki. Ta saki murmushi tana tambayan Safinah "Amma ta yaya aka yi ya gane ni?"
"Ai zuciya tana gane ƴar uwarta a ko ina. But seriously tiktok zasu iya gwada mishi yana da contact ɗin ki, anyway yayi ƙoƙari Wallahi"
Rasa da me zata amsa mishi ya saka ta fita daga kan saƙon ta sake komawa kan shafin tana duba mutane nawa yake following. Duka-duka basu kai dari ba kuma yawanci shafin kamfanunuwa ne da suke aiki tare sai ƴan uwan shi su Suhail suma duka tayi following ɗin su Amma banda Aicha, bata ma ɓata lokacin ta a kanta ba ta fito ta koma kan saƙon da ya turo ta fara tuanin kalan reply ɗin da zata tura mishi. Koma ta gwada mishi kaman ba itan bace?.
....
Yau dai zasu yar da ƙwallon mangoro su huta da ƙuda, sun gama exams sauran ganin sakamakon abinda suka shuka kuma.
Ta riga Safina fitowa don haka ta samu bakin interlocks da ya dan yi tudu ta zauna Saboda bata son tayi mata nisa ta fito tayi ta niman ta tunda ga jakar ta da wayanta da ta kashe kafin a fara jarabawan a hannun ta.
Kunna nata wayan tayi tana ɗan duba social media da aka buɗe mata jiya tana ayyana aiki ya same ta cikin ranta.
Sallamar da aka mata ya saka ta ɗago kai tana amsawa, ƴammatan nan ne guda uku na ajin su. Suka miƙa mata hannu itama ta basu nata suka gaisa suna yiwa juna fatan ganin sakamako mai kyau amma a maimakon bayan sun gama ta ga sun ƙara gaba sai suka nemi wuri a gefe da gefen ta suka zauna suka saka ta a tsakiya.
Bata bi ta kan su ba ta cigaba da danne-dannen ta kafin ɗaya daga cikin su ta kira sunan ta don ta basu hankalin ta.
"Umm Hafsah nace ba. Wannan YK ɗin da yace ke ƙanwar shi ne kuna da alaƙa ne da gaske?"
"Mai ya faru?"
Ta tambaya don su kai inda suke son zuwa ba tare da sun ɓata ma juna lokaci ba.
Daman wani hoto ne muka ga yana ta yawo har a group ɗin department ɗin mu an turo kuma wasu suna cewa gaskiya ne.
Ta gwada mata hoton don yana kusa daman gulma ne ya kawo su ba komai ba. Reina ta karɓa tana gani, gashi hoton Yaseer ne wanda aka ɗauke shi lokacin da suka yi program a makarantar sai gefe kuma wani hoto ne da idan kayi wa kallo daya zaka ce mai ɗibi da shi ne amma ita ta riƙe kamannin shi a lokacin, shi ɗin ne. A ƙasan hoton kuma an rubuta bayanin da ya saka zuciyar ta dokawa.
"Ba yace an kore shi daga school ɗinnan ba? Wai ashe raping ɗin wata yarinya yayi har sai da ya tafi prison. Kuma har wani lecturer a botany department yace da gaske ne don suna aji biyu ya shigo a fresher lokacin kuma yana bin ƴammata musamman ma yaran masu kuɗi."
~~~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
93
~~~~~~~~~~
_Je me suis fait mal en m'envolant_
_(I hurt myself flying away)_
_Je n'avais pas vu le plafend de verre_
_(I had not seen the glass ceiling)_
~~~~~~~~~~
Ta tsaya da magana don taga yanayin Reina amma hoton kawai ta tsurawa idanu, ba kuma zaka iya karantar wani yanayi a fuskar ta ba. saidai da ace tsananin bugun zuciya na bayyana sauti mai ƙara toh da nata sai ya karaɗe kunnuwan duk wanda ke cikin makarantar.
Na biyun su tace "Ba da gaske bane ko? Muma dai bamu yarda ba tunda ana tare da gaskiya ne muna cikin wa'inda zasu fara sani."
Jin yanda kanta ya fara sarawa ya saka ta ɗago ta miƙa ma ɗayan su wayar ko ita ce mai shi ko ba ita bace idan basu karɓa da wuri ba abu na gaba da zata yi shine rotsa shi da ƙasa.
"Nima ban sani ba. Don Allah ku bani wuri" ba don tana jin kaman ƙafafuwan ta ba zasu ɗauke ta ba ita zata fara tashi ta bar wurin.
Zasu sake magana wayan ta ya fara vibration. Hawayen da ya fara kwanciya a idanun ta ya saka ta ganin 'My Fiancé' da ya bayyana a saman screen ɗin duru-duru, Tayi saurin ɗagawa tana kaiwa kunnen ta.
Kafin tayi wani magana ya kira sunan ta. "Reina, ga Malam Nuhu da motana a bayan ku, kada ki cewa kowa komai ki tashi kawai ki je ki shiga ku tafi"
Bata sauƙe wayan a kunnen ta ba ta miƙe tana raɓa jakarta ta wuce ta barsu a wurin, kuka ne yake taso mata amma bata son ta sake shi a idanun kowa. tana tunkaro motar malam Nuhu ya bude mata gidan baya ta shige kana ya koma gidan gaba ya jasu a saba'in suka bar makarantar, ta manta da Safina ma.
"Yaya Yaseer na shiga Uku..."
"No, kada kiyi kuka Please. babu abinda zai faru duk plan ɗin mu ne a kan mutanen nan . kuma kinga yanzu ina hanyan tafiya ne Idan kika ɗaga hankalin ki zaki saka in fasa in dawo"
Ta girgiza kai kaman yana gabanta sannan ta saka hijabinta ta share hawayen.
"Toh yanzu yaya zamu yi?" Ko ta ce yaya zata yi? Idan yace ma kotu zasu je ta bada shaidar da za'a wanke shi ko kuma tayi video ta ɗaura a yanar gizo cewa ita tayi mishi sharri yanzu-yanzun nan a shirye take.
"Kawai ki je gidan Ummi ki zauna, Ummah ta haɗa kayan ki an tura can. Abbah kuma sun yi magana da su baba nan da kwana biyu mutanen Jama'are zasu zo a kawo tambaya da sadaki sai a saka mana rana. za'a ɗaura mana Aure without failure in sha Allah kaman yanda nayi miki alƙawarin duk wuya duk rintsi Sarauniyar zuciyar Yaseer "
Sai ta saki murmushi tare da hawaye "Allah ya tsare gaban ka da bayan ka, Ubangiji Allah ya dawo min da kai lafiya cikin aminci"
"Ameen soon to be Mrs Yaseer. Ina dawowa dan zo, ki kula min da kan ki ba don hali na ba"
Ta sake murmusawa "an gama yaya Yaseer"
Sauƙe wayan yayi daga ɓangaren shi yana jan dogon numfashi ya furzar. Yanzu shi ta ina zai fara gyara wannan ɓarakar? Shiyasa tuntuni bai ɗago case ɗin nan ba saboda halin da zata iya shiga a sanadin hakan, Amma Koma waye wannan ya shammace shi tunda gashi yana shirin kawo masa Babban asara shiyasa wannan tafiya ba shiri ta kama shi, saidai shi ba kan shi yake ji ba, itace damuwar shi, in dai hankalin ta bai tashi ba komai mai sauƙi ne.
Godiya tayi ma Malam Nuhu cikin dasasshiyar murya sannan ta faɗa gidan Ummi ta tsaya kallon hidiman da ake a ciki yanzu wanda bayi ƙarewa, sai dai kaman na yau ɗin daban yake.
Aunty Aina da ta fara ɗaura idanu a kanta ta saki guɗa ayyiriri. Nan masu soye soyen kayan tsaraban da za'a tarbi dangin ango a tsakar wurin suka maido da hankalin su kanta.