← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 117

Sashe 40

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Seemahwrites ✨*
_Menene uzurin ki da ba zaki kasance cikin ƙamshi ba a koda yaushe? Rashin samun ingantattun turaruka ne ko kuma masifar tsadan su ke hana ki siya? Idan na kawo miki maslaha zaki gyara? To kizo ga Bakhoor by Seemah zata kawo muku haɗaɗɗun turaruka all the way from Maiduguri and at Fair prices._
_Ko sana'ar turaren wuta kike son farawa baki iya ba ko baki da lokaci? Toh Bakhoor by Seemah suna bada sari naki kawai siyan containers ki zuba idan hakan ma yayi miki wahala zasu iya packaging miki tsaff naki kawai kiyi sticker ki manna._
We have all the varieties of turaren wuta you'd like ranging from;
*Sandal chips*
*Sandal bange*
*Sandal flakes*
*Sandal balls*
*Kajiji*
*Hawi*
*Halut*
*Bayan Halut*
*Gabgab*
*Farce*
*Cotton*
*Dorot*
A ɓangaren turaren jiki akwai Kalolin *Black khumrah*
*White khumrah*
*Dufr khumrah*
*Oil perfumes*
*Kabbasa spray*
*Original and cream Kulecham*
Akwai kuma *wardrobe balls* ma kaya.
Muna da bridal packages *_bronze, silver, gold da diamond_* and it's customizable.
Za'a tsuma muku turaren amarya idan biki sauran wata biyu ko sama da haka.
Ku dai ku tuntuɓe ta a kan lambar waya 08021689184 domin ƙarin bayani.

70

Duba ya kai wurin ta lokacin da ya dire aya; tana shiru ta lume a cikin kujerar kaman wanda ruwa ya cinye, hawayen da suka gama bin idanunta sun bushe, tayi nisa a duniyar da mahaifin ta ya kaita, duniyar da yafi nata girma da ƙalubale.

"Sarauniya ta" Alhaji Tahir ya kira.

Dawo da dubanta tayi gare shi, rabin nutsuwar ta yana nazarin labarin da ya bata babi bayan babi.

"Na canza sarauniyata kuma na ɗauki darasi a kan rayuwata na baya. Da Tahir ɗin da dana yanzu babu wanda zai taɓa justifying zaluncin da aka yi miki amma Nagode ma Allah da ya ara mun tsawon rai na gane kura-kurai na a wurin da nake da ikon gyarawa, sannan ina gode masa da baki tashi a turban da na ɗaura ki ba, domin da na cuce ki kuma na cuci kai na"
.
.
.
.
Tsayawa tayi tana ƙarewa gidan kallon da bata yi mishi daga farko ba; kallo da buɗaɗɗiyar zuciya. Ƙofar wurin da ta same shi a ciki ɗazu ya buɗe, kaman yanda tayi tsammani shine ya fito idanunta suka shiga cikin nashi, sai ta shiga taryo rayuwar da yayi a cikin idanun ta, tana haka har ya zo zai gifta ta gaban ta.

"Ki shirya bayan La'asar zamu fita" shine Abinda yace da ita yayi wucewar sa, kafin ta ankara sai gani tayi ya shige ɗakin dake gaban na mahaifin ta ya rufo ƙofa.
.
.
.
Ta ɗauka su biyun su zasu fitan yanda zata samu damar da zasu yi magana a tsanake amma lokacin da suka ɗau hanya sai ta samu kanta a seat ɗin baya tare da Maama, domin sai da suka jirata ta dawo daga Islamiyya. Yaseer a mazaunin driver tare da Aicha a gefen mai zaman banza.

"Ai na ɗauka kin riga kin yi list yanda ba za'a manta da wani abun ba" Aicha ta juyo ta dubeta, dake ita ce a baya ɓangaren Yaseer kallon ƙurilla take ƙare mata har sai da Reina ta kasa jurewa ta ɗauke idanunta ta ƙara takure jikinta. Allah ya gani yaƙen da yake kan fuskar tan nan yana damunta, Ko dayake itama tarr take ganin ta tunda a gaban ta aka yi komai, itama kallon ta take yi da baƙin abinda ta aikata.

Haka har suka ƙarasa gaban wani babban shago Aicha ne kawai ke faman surutun ta ita kaɗai, idan tayi da Yaseer ya amsa ta da kai Maama kuma tace "Eh" ko "A'a" bata sake bin ta kan Reina ba ma.

Tsayawa yayi ganin tazarar dake tsakanin su da ita kaman ba tare suke ba, sai faman rakuɓe-rakuɓe take "Zo ki wuce gaba" yace da ita yana matsawa gefe ya bata hanya.

Sai ta kalle shi ta kalli Aicha da lokaci guda ta haɗe gabas da yamma.

Babu alamun wasa a tattare da yanayin shi don haka ta ƙaraso da ɗan hazari ta iske su, amma bata wuce gaban ba kaman yanda yace.

"Yayanmu nace yaya zamu yi da baƙin Cairo wanda zasu shigo cikin week ɗinnan?" Aicha ta sako zancen da take da tabbacin zata karkato da hankalin shi gareta.

Taci nasara kuwa domin ya juyo ya dubeta
"Kin san me? Ku wuce ke da Maama ta ɗaya bangaren ku zaɓa abinda ya dace kawai, muma hakan zamu yi in order to save time"

Cikin mamakin da tayi ƙoƙarin ɓoyewa kada ya fito a cikin muryar ta tace "In tafi da ita dai ku tsaya da Maaman"

"Ba haka naga dama ba Aisha"

Sai ta ƙaƙalo murmushi tace wa Maama "muje" idan ma burin Reina ta shiga tsakanin ta da Yaseer ne ba zata bata ƙofa ba balle tayi Nasara.

Saida suka wuce ya kalli agogo sannan ya dubeta. "I'll give you 20 minutes ki cika min nan wurin"

Ya gwada mata ƙaton shopping cart da Aicha ta janyo ta bari a wurin sannan ya koma gefe ya ciro wayan shi.

"Sauran 19 minutes 35 seconds" yace idanun shi a kan wayan hannun shi.

Kaman wanda ta dawo cikin hayyacin ta, cikin sauri ta shiga dudduba kayan, duk wanda yayi mata kyau sai ta duba size ɗin idan zai yi ma Maama ko zai yi mata sai ta ɗauko ta saka a cikin shopping cart ɗin.

"9 minutes more" yace idanun shi a kanta ganin ita nata nutsuwar ya tafi kan abinda take yi.

Sai ta sake susucewa kaman wanda take ɗakin jarabawa za'a ƙwace takardan ta bata gama rubutu ba.

Ma'aikatan wurin suka ƙaraso zasu taya ta, Yaseer ya girgiza musu kai kuma yaci gaba da ƙirga mata lokaci.

"3...2...1... Dakata!"

Cakk ta tsaya riƙe da abaya onion pink tana mayar da numfashi. Ya miƙe daga jinginen da yake ya koma wurin da ya ajiye mata shopping cart ɗin yana dubawa.

Hannu ya ɗaga ya saka yatsar shi ya ɗane mata goshi, ta saki rigan hannun ta a ƙasa ta riƙe wurin tana sakin ƙara.

"Haka ake cika abu a garin ku?"

Kallon kayan da yayi kaca-kaca Saboda yanda take wurga su ciki tayi idanun ta ya tara ƙwalla.

"Kuka zaki mun?" Ya ɗan ranƙawo yana kallon cikin idanun ta tayi saurin girgiza kai.

"Better" yace cikin raɗa domin ba'a zo gaɓar da zata fara kuka ba tukunna, wannan sharan fage ne.

Ya miƙe yana umartan ma'aikatan su kawo wani shopping cart ɗin,Ya sakata a gaba tana turawa har wani section na English wears, wancan kuma ya bar musu a lissafa ayi packing.

"Wannan minti 15 kike da shi, idan shima kika yi failing zan sake rage lokaci"

Bata bari ya rufe baki ba sai ganin ta yayi ta ɗiba a guje ta ɗauko wasu riguna ta dawo ta zuba.

"Idan kika ɗauki abinda ba zai yi sizing ɗin ku ba kika saka nayi asarar kuɗi na sai kin biya ni"

Kallon shi tayi fuska a kwaɓe kaman zata fasa Ihu, da murmushi a kan fuskar sa yace "13 minutes 12 seconds" yayi mata nuni da agogon tsintsiyar hannun shi alamun lokaci na kan gudu.

Wasu manyan rigan sanyi da jackets da ta gani su ta koma ɗibawa yanda zasu cika abun da wuri, tana zubawa yaseer ya saka hannu ya cire. "Ina zaki kai kayan sanyi a zafin nan?"

Bata ce komai ba taci gaba da ɗibo na kusa da su tana zubawa tunda bata ga alaman zai barta ta ɗaga cart ɗin daga gaban shi ba, sai ya shiga cire duk wa'inda basu mishi kyau ba yana tarawa a gefe.

"Yaya Yaseer!" Bai san ashe sunan shi yana da garɗi haka ba sai da ta sanya ya ji kiran har magudanan jinin shi.

Ya dube ta yana mai ciza laɓɓen bakin shi wurin tabon nan. "Na san ki ne? Your time is still ticking young lady, sauran ki minti 4"

Dogayen skirts, jeans da wandunan palazzo ta ƙaro musu sai English gowns yace time ya cika.

Ya dubi kayan bai kai na farko cika ba, ya ƙaraso gaban ta ya ɗaga hannu sai tayi saurin rintse idanunta cikin sadaƙarwa tana jira amma shiru kuma har yanzu tana jin ƙamshin turaren sa mai kwantar da hankali a kusa da ita.

ɗan ƙyalla ido tayi, yana tsaye a gaban ta bai motsa ba, sai da tayi yunkurin buɗe idanunta a tunanin ta ko ya haƙura ne ya shammace ta ya sake ɗane mata goshi ta kuwa ji zafin shi sosai sai ga hawaye zirrr.. "wayyoo Allah yaya Yaseer"

Gaba yayi ya barta a wurin kafin hawayen ta su narka mishi zuciya, ya shiga ɗauko kayan da yaga sun yi mishi kyau yana ƙara mata. Suna haka har su Aicha suka ƙaraso suka same su a Wurin.

"Kuna nan ashe?" Ta dubi Yaseer da yake duba wasu beanie caps, can gefe kuma ga Reina dake sharar ƙwalla.

Sauƙe ajiyar zuciya tayi don Allah ya gani hankalin ta bai kwanta ba tunda ta bar su a tare, shiyasa bata tsaya wani tantance kayan da suka zaɓo ba, don suyi su dawo.

Turamen zannuwa, laces, materials da shadda suka ɗibo sai undies, Amma duka kayan a shopping cart ɗaya suka ciko har Maama tana ce mata yayi yawa.

"Yanzu mai ya rage?" Ya tambayi Aicha da ta ɗora ainhin murmushi a fuskarta a maimakon yaƙe.

"Uhmm.. kayan shafe-shafe, turare, takalmi da jaka, veils da hijabs, sai kuma kayan kwalliya da jewelries" Bata ga su abaya ba amma tunda ta san a wurin ta bar su sun siya, kenan kayan da Yaseer ya jida mata a gaban nasu ba komai bane, kuma ma taga shi yake zaɓan kayan da kan shi.

"Ku siya sauran, na gaji zamu fara wucewa, zan turo driver ya ɗauke ku"

"Da ita zaku tafi?" Ta gwada Reina.

"Eh, akwai matsala ne?" Ya tambaya kaman mai niman sani da gaske.

Girgiza kai tayi "A'a, Allah ya kiyaye"

Ya tsaya yana jiran Reina ta ƙaraso su jera amma sai ta koma bayan Aicha ta ɓoye.
"Ka tafi kawai zamu zo" ta sani zalin ta yake son yaci gaba da ci, goshin ta kuma har yanzu raɗadi yake mata.
Chapter 40 · 0% Book details