← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 117

Sashe 94

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Same here my love" ya amsa tare da ciza bakin shi yana kare ma shigar ta kallo. Riga ce bodycon baƙi da iyakar shi cinyar ta, ya riƙe ko wani lungu da saƙo na jikin ta sannan ta sama ma hannun vest gare shi, sai siririn silver necklace da ta saka da ɗan kunnen su da bracelet a hannunta da ya ji lalle, ta fente leɓɓen da jan jambaki mai bushewa, kanta babu ɗankwali tana faman zuba ƙamshi. Tayi mishi kyau kaman ya sace ta ya gudu.

Yawu ya haɗiya, ajiyan cikin wuyan shi yana motsawa. Ya mayar da duban shi ya ajiye a iya fuskarta kawai saboda kallon jikinta zai iya saka duk dauriyar da yake yi ya tashi a banza, haƙurin jira sai ta samu cikakkiyar lafiyan ƙwaƙwalwa ta samu nutsuwa da kanta da kuma shi kafin su cigaba da shimfiɗa kyakkyawar rayuwa zai iya ƙarewa daga yanzu.

"Akwai wani abu ne a fuska na?" Ta tambaya tana taɓa fuskan ganin yanda ya kafe ta da idanu, ga yanayin shi da ya sauya lokaci ɗaya. Toh ko akwai wani matsala ne? Ƙirjin ta ya fara dokawa da sauri Saboda kalan tunanin da shaiɗan yake bijiro mata a cikin kanta, ko dai gajiya da ita Yaseer yayi tun ba'a je ko ina ba? Ta shiga uku!.

Murmushin nashi fuskar ya mayar ganin ta damu sannan ya sauƙe mata hannun da ta kai kan fuskarta "kada ki ɓata min kwalliya na" sai ta ɗan saki murmushin yaƙe amma zuciyar ta bai daina bugu ba, idanunta na yawo a kan fuskar shi kaman a nan ne zata karanci labarin dake zuciyar shi.

Lakatan hancin ta yayi "hey, why so serious?" Ya jawo ta da hannun shi dake ƙugunta ya manne bakin su na tsawon second 3 kacal da ta iya ƙirgawa da bugun zuciyan ta sannan ya janye. "Kawai kin yi min kyau ne, fiye da tunanin ki. Har na fara tunanin yanda za'a yi na iya rayuwa ba tare da na same ki ba, Reina na auna arziƙi"

Sosai murmushi ya kwace mata har saida ta saka hannunta biyu ta kare bakinta kada ya ga yanda take wangale shi sannan nutsa kanta cikin ƙirjin shi shima ya riƙe ta da kyau.

Ita ta fara janyewa wannan karon tace "muje in baka abinci" ya gyaɗa kai idanunta suka sauƙa a kan manyan laidojin da ya sake a wurin tun shigowar shi ta ƙarasa ta ɗaga tana dubawa. Fruits ne mai yawa a cikin na farkon sai gasassun masara a cikin na biyun.
Ta shiga kirgawa idanunta suna ƙara girma a lokacin da ta gama. "Guda Goma babe!" Ita tace masa tana so yazo mata da shi amma koda tare zasu ci ina zasu kai har guda goma?

Yace "Eh, kinga sai ki ajiye a fridge idan zaki ci kawai kiyi microwaving ɗin shi"

"Toh ai zai bushe" tace tana dariya "amma nice idea zan gwada"

Ya ja hannunta suka wuce cikin nishaɗi don murmushinta kawai yana sanya shi farin ciki.

Zama yayi tana serving ɗin shi yake tambayan ta me Suhail yazo yi gidan domin yana da tabbacin ba haka kawai zai ce zai kawo mata abinci ba bayan gashi yaje can kuma duk daren daɗewa nan zai dawo.

Murmushin dake kan fuskarta ta ƙara faɗin shi kana tace "Safina ne tazo shine na kira shi yazo ya ritsa ta"

"Amma baki kyauta mata ba gaskiya. Kada ki saka tayi fushi ta guje mu"

Ajiye masa plate ɗin tayi bayan ta gama zuba abinda zai iya ci sannan ta koma ta zauna tana faɗin "Feenah ce fa, tana hucewa zata neme ni. Kuma ma idan ban yi haka ba yaya Suhail ba sake min wuya zai yi ba, kaga daga nan duk yanda ta ƙare musu sai dai mu bi su da fatan alkhairi"

Ya jinjina kai
"Ina spoon din ki?" Ya tambaya ganin cokali ɗaya ta saka.

"Masaran kawai zan ci"

"Masara abinci ne?" Ya tambaya yana haɗe fuska ya koma yaya Yaseer ɗin shi.

"Bani jin yunwa ne"

"Da kika ci mene?" Ya tambaya Tunda da ta buɗe kwanon abincin bai ga alamun an ɗiba ba.

Duk abinda zata ƙirgo ta ci ba aminta zai yi ba don haka ta miƙe kawai zata ɗauko cokalin, ya mayar da ita ta zauna ya fara bata a baki.

"Mu gama sai ki sha magani ko?" Yace yana mayar da murmushi kan fuskar sa.
.
.
Saida ya dawo daga sallan isha ya ɗauka mata masaran guda biyu a kan plate suka wuce sama bayan sun kulle gida sun kashe komai, ya rage sauran uku domin da zai fita ta ɗauki rabi ta bashi ya kaiwa security.

Washegari da safe suka yi shirin asibiti zuwa therapy session ɗinta tare da Dr Fahad.

A kujeran da suka fara zama tare da Yaseer ta zauna suna fuskantar juna da Dr Fahad a maimakon na kwanciya.

Ya harɗe yatsun sa a gaban guiwan ƙafar shi na dama yana sauraron ta.
"..so yaya kike ji bayan ganawar mu na biyu?" Ya tambaya yana karfafa kalaman shi da motsin hannun shi ta hanyar watsa yatsun shi a iska.

"Much better, yanzu ko faɗo min yayi a rai ko nayi ƙoƙarin tunawa bani jin fargaba kaman da"

Ya jinjina kai "yayi kyau. So Yanzu kina ganin zaki iya sake bani labarin? Tun daga farkon lokacin da zaki iya tunawa har zuwa wannan ranan da kuma bayan shi. Kada ki zurfafa tunani ki saka ma ranki kaman muna hira ne kawai, idan kuma kika ji numfashin ki ya fara hauhawa sai ki tsaya ki shaƙi dogon numfashi ta hanci a hankali na seconds 4, ki riƙe shi na seconds 7, kafin ki fitar da shi a hankali ta baki na tsawon seconds 8. zan taya ki ƙirgawa muyi har sai kin ji kin daidaita" ya ƙarasa yana gyaɗa mata kai.

Numfashin ta fara sauƙewa tana ƙurawa glass ɗin ruwa da ya ajiye mata a saman table ɗin da yake tsakanin su idanu.

"I think ya fara ne lokacin ina da shekaru 7 zuwa 8. Lokacin babu wanda ya sani ko Umman Zahra ma, Aunty da Daddy ma basu sani ba saboda yana tsorata ni yana ce mun idan na faɗa kowa zai bar sona, so ganin daman Aunty tafi son Maama sai yarda da shi bai yi mun wahala ba..."

"Shi wane? Me kika ce sunan shi ma?"

Ɗago idanunta tayi daga jikin kofin ta ɗaura su a kan Dr Fahad. Babu wani yanayi a kan fuskar shi bayan nutsuwar shi da ya bata ɗari bisa dari.

Ta haɗiyi wani abu mai ɗaci ta furzar da numfashi sannan murya ƙasa-ƙasa tace "Jamal..."
.
.
.
Miƙewa Yaseer yayi ganin ƙofar ya buɗe suna fitowa, ya saki murmushi ganin akasin zuwa na farko da na biyu yau bata yi kukan ba ga dai hawaye na ƙyalli a cikin idanun ta. Ya jawo ta ya rungume yana sumbatar ta a saman kan hijabinta.

Dr Fahad yace "tunda akwai improvement sosai ba sai an sake arrangement an nima mata wani therapist a inda zaku je ba zamu iya yi sessions ɗin online. So Allah ya kiyaye sai kun dawo, ka kaita ta ga wurare masu kyau ta manta da damuwowin ta shima zai taimaka"

"Of course doctor, mun gode"

"Safe flight" ya ɗaga mishi hannu ya wuce ya bar Reina tana yiwa Yaseer kallon rashin fahimta.

Murmushin gefen baki yayi yace "What? Tafiya zamu yi"

"Ina?"

"Abuja, daga nan kuma duk inda hali ya kaimu"

Bai bata daman sake wani tambayan ba ya ja hannunta suka bar asibitin.

Gidan Ummi ya wuce da ita tayi musu sallama tunda ta riga da ta san da zancen tafiyan, don yaso sai passport ɗinta ya fito ne yayi mata surprise.

Ta samu gidan a cike kuwa jikoki sun zo yi mata weekend ga su Maama ma suna nan, kan kace mene ya nime ta ya rasa.

Bayan sun gaisa da Ummi da Baba ya tafi ya barta a gidan har saida aka yi la'asar kafin ya dawo ɗaukan ta.

Ummi ta bata shawarwari ta haɗa mata da kayan sarauniyar mata mai sirrin tsirrai da Aunty Sajida ta turo a kai mata, ta bisu da addu'a da fatan Allah ya kiyaye aka musu rakiya suka tafi bayan aljihun kowa a gidan ya shaida zuwan Yaseer.
Daga nan kuma suka wuce gidan Umma suma yake jaddada musu zancen tafiyan.

Sosai Umma ta gwada jin daɗin ganin Reina, sai gashi ta ɓige da yaryala mata ƙananun kitso a kanta, a cewarta tafiya da kuncaccen kai zai dame ta, ai kuwa bata san tana jin kunyar Umma ba sai yau amma babu yanda ta iya haka ta zauna, suna yi tana bata kalolin shawarwarin da uwa take bawa ƴar cikin ta.

Bayan Isha aka taru a parlo har da Abbah da daddynta ana shan hira, a nan Abbah yake faɗawa Yaseer ya kamata gobe ya je Jama'are yayi musu godiya kafin su tafi.
Reina ta dai sha mamakin yanda Aicha take wani kula ta tana ta faman mata murmushi wanda da ba haka abin yake a tsakanin su ba.

Sai ƙarfe 10 suka bar gidan don haka da suka isa duk sun gaji sai barci. Washegari kuma Lahadi a office Yaseer ya kusan wuni sai bayan azahar ya dawo yaci abincin da aka kawo musu don Umma tace sai ta cika musu sati guda kafin nan Reina ta fara girki.

Ya huta zuwa la'asar sannan yayi shirin tafiya Jama'aren kuma ya shaida mata da sun je zasu juyo.

Tana idar da nata sallan sai gani kawai tayi ya fita bai jira rakiyan ta ba, ga saƙon da ya ajiye mata a waya na cewa yana sauri su Abbah suna jiran shi.
Ta san idan tace bayan shi zata bi ba zata riske shi ba har ya fice don haka ta fita ta terrace ɗin dake saman ta kuwa ci Sa'a yana nufan wata baƙar Jeep da yau ta fara ganin shi a gidan. Bata damu ba kuma bata kawo cewa a gidan ne su Abban suke jiran shi ba, ga motan tinted ne balle ta hango su zaune a ciki ta ƙwala mishi kira ya juyo.
Chapter 94 · 0% Book details