← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 117

Sashe 7

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya saka hannu ya karɓa ya shiga dubawa. Tayi copy tun daga farko har ƙarshe, daman shi ba rubutu yake yi a aji ba sai yaga dama, anyi marking ɗin note bayi da ko shafi ɗaya shine malamin ya bashi sati ɗaya idan bai kawo complete note ba ze kai complain ma mahaifin shi, gashi cikin ƙanƙanin lokaci wannan yarinyar har ta gama kwafa. yayi mata nuni da hanyar da ta fito da kayi. "Yayi, zaki iya tafiya"

Sai ta gyara zaman barret ɗin kanta domin ta samu kwarin guiwa tace "babu wani ne?"

Kwana 3 ta ɗauka tana kwafa masa note, daga sun dawo makaranta zata duƙufa ba dare ba rana har islamiyya taƙi zuwa don kawai ta samu ya kula ta yayi mata magana, amma gashi haka kawai ya zauna sai hira suke yi da Reina bayan a da kowa ya san basu jituwa.

"Idan akwai zan kira ki, bar min nan" ya saka ƙafa zai hankaɗa ta Reina ta shammace shi ta hanyar mikewa ta turo shi daga kan desk ɗinta baki ɗaya ya faɗo ƙasa timm, ƙarar faɗuwar da ihun da ya saki ya jawo hankalin kowa kan shi tunda ba'a kai ga fita break ma ƴan secondary ba sai su Zaheera ƴan primary sun koma kafinnan, don haka ajin a cike yake.

Miƙewa yayi ya karkaɗe jikin shi yana bin Reina da kallon tambaya tunda yau ba da tashin hankali yazo mata ba.

"Baka san ƙanwata bace?"

"Ba Zainab bane kawai ƙanwar ki?" Da gaske ya ajiye duk husumar dake tsakanin su.
Ta miƙe ta harare shi kana taja hannun Zaheera suka bar ajin wanda ita ba haka taso ba.

.....
Har sai da suka ci abincin rana suka gama kafin ma Hajiya Hauwa ta Lura Reina bata dawo ba.
"Ke ina Hafsatu?" Ta tambayi Zaheera.

"Ta bi Uncle ɗinta da yazo ɗaukan Maama, wai zata koma gidan grandma ɗinta"

A firgice Hajiya Hauwa ta miƙe. "Dan ubanki kuma shine sai yanzu kike faɗa min.!" Ai gwamma ko ina ma da gidan su uwarta, dangin munafukai.
A saba'in tayi ɗaki ta ɗauko key ɗin ƙaramar motarta, ta fito sanye da dogon hijabi a kan dogon rigan shan iskar dake jikin ta.

Toh yanzu idan taje ɗauko ta sai tace musu mene? Yarinyar da aka kawota shekaran jiya har ta gudu? Wa ya san me taje ta faɗa musu ma tunda bakinta ba sakata gareshi ba?.

Bata jira anyi mata iso ba ta faɗa musu parlour bayan tayi gajeriyar sallama, Zaheera na biye da ita a baya, hannun ta ɗauke da kwalin pizza da ta biya ta siya ta rinjaye ta dashi. Reina na kwance a kan cinyar Ummi tana biya mata karatu, ga Tv a kunne amma an zuge muryar shi.

Ɗaga Reina Ummi tayi ta tarbi Hajiya Hauwa da sakin fuska ta tura a kawo musu ruwa. Sauƙe ajiyar zuciya Hajiya Hauwa tayi domin irin watsewar da suka yi a kan riƙon yaran da ace Reina ta faɗa mata wani abun koda a kan irin zaman da sukayi a kwana biyun tabbas ba zata samu tarba mai kyau ba.

Don haka itama ta saki fuska aka gaisa cikin girma da arziƙi, Reina dai na maƙale da Ummi, babu abinda zai maidata wannan gidan mugayen.

"Ai ta matsa tana son ganin ƴar uwarta ne fah, shine nace tazo nan ɗin idan na tashi daga aiki da kaina zan zo in ɗauke ta."

"Allah sarki, ai na ɗauka tazo mana kwana biyu ne, har kuwa zan tura a karɓo uniform ɗin islamiyyarta taje gobe, Ita ƴar uwartan ma ta tafi."

Murmushin yaƙe Hajiya Hauwa tayi "haba yanzu yayi wuri, idan an kwana biyu dai za'a kawota" ta shiga yafato Reina da hannu Amma taƙi zuwa, tayi mata nuni da kwalin pizza nan ta shiga kokwanto. A gidan Ummi ba'a dukanta ba'a barinta da yunwa amma kuma basu da irin wannan abun, ko ta bisu ne Idan suka cigaba da abinda suke mata ta sake gudowa?.

Hannun Zaheera ne ya sauƙa a saman nata tana sake mata murmushi.
Ta miƙe ta ƙaraso gaban Hajiya Hauwa tare da yin ƙwafa tana nuna ta da yatsa "Wallahi tallahi idan na biki kika sake...."

"Ba nayi miki faɗa a kan rashin kunya ba?" Ummi ta katse ta.

Taci gaba da cewa "toh ai itace take bani abinda bani so kuma ta sani"

Da rawar jiki ta miƙa mata kwalin hannun ta "Shikkenan zan baki abinda kike so kinji?"

"Kice wallahi"

Lallai yarinyar nan zata gaya musu idan ta shiga hannun ta.

"Hajiya ai ba'a biyewa na yara. Ki ɗauke ta kawai ku tafi, Allah ya kara haƙurin riƙo"
Zuciyar Ummi a wanke yake sanin cewa suma jininta ne ba zasu cutar da ita ba, sannan riƙon Reina daman sai an kai zuciya nesa tunda uwar da ta haifeta ma saida ta koka.

Cikin jin daɗin komai lafiya tace "Toh ki bawa Maama wannan sai ki ɗauki na mota"

Babu musu ta mika ma Ummi kwalin, zuwa yanzu ta fara jin ƴar uwarta a zuciyar ta koda ita bata kulata kuwa, tun abinda ya faru da daddyn su.

Babu wani pizza a mota daman guda ɗaya ta siyo kuma ta ɗau alwashin Reina ba zata ci ba. Basu bar unguwar ba sai da ta saka Hajiya Hauwa kafa mata ranƙwashi masu zafi ita kuma ta shiga mata ruwan ashariya.

Suna shiga gidan ta tura ta ɗakin da ta watsar da kayan ta ko ina ta kuma sanar da ita idan bata gyara shi ta kintsa komai a wurin zaman shi ba yau babu ita babu abincin dare.

Tayi tunanin zata tsallake, ko me Hajiya Hauwa zatayi sai dai tayi, amma ta samu kanta ƙarfe 12 na dare tana kalmashe kayayyakin iya iyawar ta tana jerawa a tsohon wardrobe ɗin Zahra tana zubar da hawaye, Zaheera tana nata gadon tana shaƙar barci taƙi taya ta don yau haushinta take ji a kan Abinda ya faru a school.

Saida ta gama tass taje ta samu Hajiya Hauwa ta bata wani sanƙararren jollof ɗin taliya, haka ta tura a cikinta tana godiya ma Allah da ba shinkafa bane domin a gidan Ummi ma shi ɗin taci, anje siyo mata awara ta ɗaura a kai kenan Hajiya hauwa tazo ta ruɗeta da pizza ɗin ƙarya.

Washegari tayi shirin makaranta a birkice kaman jiya uniform ɗin ba a goge ba, stockings ɗin ta cusa ta gaba ta baya ta barshi da halin shi, ga bow tie ɗinta ma ya warware kuma bata iya ɗaurawa ba. Haka ta zurma barrett ɗinnan kaman malum-malum don hijab sai sun shiga senior class tukunna.
Ta fito kana ganinta kaga mara gata, suka isa jikin mota suka ɗaura rikici da Zahra a kan wurin zama domin yau Zaheera ma taƙi zaman gaban, Fitowar Hajiya Hauwa kuwa sai ta jawota tace suyi tafiyar su.

Tunda ta koyi guduwa makaranta zata canza mata, amma sai tayi discipline ɗinta tukunna.

..
..
..

Koda ace abubuwan dake iya sauyawa cikin wata guda suna da yawa Reina bata yi tsammanin zata kasance ɗaya daga cikin su ba, bata da rama har yanzu amma idan ka ganta ba zaka ce tayi mummunan ƙiba kwanaki ba, domin abu biyu Hajiya Hauwa take horata dashi, yunwa da duka.

Bata zuwa school har yanzu, Ummi tazo bin ba'asi lokacin tana zazzaɓi sai tayi tunanin dalilin rashin zuwan kenan, kuma Hajiya Hauwa tayi musu tsaye a kai tana zazzare mata idanu a bayan idon Ummi Sai Reina taji tsoron magana har ta tafi.

Tun daga lokacin kuma ba'a sake barinta ta taka ko bakin gate ba. An ƙwace tab da laptop ɗinta, sannan yanzu bata da wani kataɓus a cikin gidan.

Durƙushe take a ƙasan wurin, hannunta bibbiyu take cuɗar tiles ɗin da iya ƙarfinta.
"Allah idan bai fita ba yau ni da ke a gidan nan" Hajiya Hauwa ta juya ta bar ɗakin domin aikin dake gaban su da yawa, muhimmin baƙo ne yau zai sauƙa a gidan, shine tsabar tsiya an ajiye abincin shi Reina ta buɗe ta ɗiba.

A matsayin punishment ta saka ta wanke toilet ɗin ɗakin da take fatan ya yarda ya zauna bayan an tuttuɗa bleach da toilet cleaner da take jin ƙarfin su har cikin huhunta kuma shine akace sai ta wanke da hannu ba da brush ba, kuma idan bai yi ƙyallin da zata ga fuskar ta a garu da ƙasan bayan gidan ba sai ta jibge ta. Gashi ta koyi dukan ta a wuraren da ba zai gwada ma wani raunukanta ba saidai ita taji azabar su a cikin jikin ta, Kaman kanta, bayan ta, cinyoyinta da ƙafafuwanta yanda yake rufe da kaya.

Miƙewa tayi jin tana niman sumewa ta ɗauraye hannunta tayi kwanciyar ta a gadon ɗakin da aka saka masa sabon bedsheet ƙarr aka gyara shi tass sannan aka feshe shi da turare. Zata ɗan kwanta ne kaɗan idan kanta ya rage sarawa sai ta ƙarasa wanke toilet ɗin ta gyara gadon ma tunda yanzu dole yasa ta iya, babu ɓata lokaci gajiyan dake jikinta ya gayyato barci suka zo su biyun suka danneta, domin daren jiya har ƙarfe ɗaya ita da masu aikin gidan suna kan ƙafar su, yau ma tun tashinta sallar asuba bata koma ba.

Kan Hajiya hauwa da ya ɗauki zafi ya saka ta manta da Reina da kuma aikin da ta bata gashi jirgin su ya sauƙa, Alhaji Salisu ya kira ya sanar da ita sun baro airport.

Saida ta tabbatar da kimtsuwar komai Saboda ta san Bilal da tsantsenin sa. Da yaya ma ta samu ya yarda zai sauƙa a gidan ta? Yayar ta Maryam itace mutuniyar shi dama, shiyasa ya baro aikin shi yazo bikin ƴarta, ya haɗu kuma da kasancewar angon Abokin shi don za'a iya cewa ma shi ya haɗa auren.

Yana amsa waya suka yi parking a ƙofar shiga don haka yayi zaman shi a bayan mota har sai da ya gama kusan minti 10 suna tsaye suna jiran shi kafin ya fito.

"Oyoyo Uncle B" Zaheera ta karasa ta rungume shi cikin nutsuwa dukda tana ɗauki amma sun sani bayi son rashin fasali.

Daga nesa Zahra ta iya gaida shi, bata manta da marukan da ya ɗibeta dasu wancan zuwan shin ba.
Chapter 7 · 0% Book details