Sashe 61
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yanzu kin gama zan iya magana?" Abbah ya tambaye ta, bata ce komai ba sai share hawaye da ta cigaba. Yace "Idan irin wannan yafiyar ne da kin bar abinki, domin banga amfanin kana iƙirarin yafiya kuma ka cigaba da ganin mutum da laifin sa ba. Sannan Idan kina tuna sharri shima alkhairi kada kina manta shi Saudatu don wannan rufin asirin da muke ciki Allah ne ya buɗa mana Amma Hafsatu da mahaifin ta sune sila. Sune silar da mu da yaranmu muke cikin kyakkyawar rayuwa kin manta da wannan?"
Shiru Saudat tayi don bata da ta cewa, amma shima Kamal ya sani amsar wannan lamari ba zai zo mata da sauƙi ba dama, don shima ya zo masa a bazata matuƙa, amma yaya zasu yi? Alaƙar da Ubangiji ya riga ya ƙulla babu mai iya warwarewa sai shi, Idan Allah ya riga da ya ƙudurta Hafsatu ita ce ƙaddarar Yaseer babu yanda suka iya dole su taya shi amsar ta hannu bibbiyu.
"Shikkenan damuwan ko akwai abinda yayi saura?" Goggo ta tambaya.
Shiru dukkan su suka yi. Ta gyara kishingiɗen da take a kan shimfiɗin ta a tsakar babban parlon ta da komai akwai amma a nan take tarewa saboda ciwon ƙafa dake hana ta yawan zirga-zirga balle zama a sama.
"Saudatu ke meye matsayin Abidah a wurin ki?"
"Ƴar uwata ce goggo" ta amsa cikin raunin murya.
"Kai fa Kamalu, Menene matsayin Hafsatu a wurin ka"
"Nima haka goggo"
"Sai kuma aka ci Sa'a ku biyun ƴan uwan juna ne. Toh alhamdulillahi, duk wanda ya yiwu zumunci aka ƙulla mai ƙarfi, don haka kiyi haƙuri ku koma zan kira shi Yaseer ɗin yazo ya faɗa ra'ayin shi kuma in sha Allah ba za'a mishi Abinda bayi so ba Saudatu nayi miki alƙawari."
Ta miƙe tana goge hawayen ta da jero godiya, goggo tayi musu adalci don babu yanda za'a yi ace Yaseer yana son Reina wannan shiri ne kawai.
......
*Yaseer*
Yau ma shi ya kai su Reina gidan Ummi wuni kuma almuru na gabatowa ya dawo ya ɗauke su. A hanya ma hira suke sha sosai harda Maama, haka suka dawo cikin nishaɗi yayi parking a ƙofar shiga duk suka fito sannan ya bawa driver key ya adana motar a yanda ya kamata sannan suka nufi ciki.
Sai a lokacin suka lura da Umma da Abbah dake tsaye a jikin motar da suka dawo a cikin ta yanzu, Abbah yana riƙe da hannun ta yana magana da yanayin da yafi kama da rarrashi ita kuma ta kawar da kai gefe tana sauraron shi.
"Barka da gida Abbah, Barka da gida Umma" muryar Reina ya katse su sannan ta durƙusa tayi musu gaisuwa.
Idan ba idon ta ne suka mata ƙarya ba kaman hararar ta Ummah tayi sannan ta wuce ciki abinta ba tare da ta amsa gaisuwar ba duk suka bita da ido.
Haka aka ci abincin dare babu Ita babu Yaseer don shi taraddadin fuskantar ta yake yi tunda yanayin ta ya gwada ta san komai.
Yana zaune a ɗaki a gaban reading table ɗin shi, wayar shi yayi ƙaran shigowan saƙo sannan screen ɗin tayi haske ta bayyana manhajar da aka turo saƙon da sunan mai ita.
Saurin ajiye Abinda yake yi yayi ya ɗaga wayan yana shiga saƙon da aka turo ta WhatsApp da yake cewa.
'Yaya Yaseer me yasa baka fito cin abinci ba yau?'
Murmushi yayi yana miƙewa ya koma bakin gado sannan ya mata reply da.
'Not hungry. Ba kin bani abinci a gidan Ummi ba?'
Ganin har ta duba tana typing reply yayi ƴar murmushi, yau layin markaɗen ta ya zo ta kan shi kenan Finally, don wannan ne karo na farko da ta taɓa masa magana a chat.
'Haka fah!'
'Na manta ne har na damu ko wani abu ne ya same ka'
Sau uku yana karanta reply ɗin ƙarshen yana jin daɗi yana ratsa shi har magudanan jinin shi.
'ina lafiya. thanks for the concern'
Wannan karon sai da aka samu tazarar wurin minti bakwai kafin ta turo da.
'most welcome💗' da emoji ɗin pink ɗin heart yana bugawa.
Kaman ya bawa hakan muhimmanci amma sai ya lura kusan duk saƙon da zata turo sai ta saka emoji a jiki. Don haka ya share ya tura mata.
'me kike yi yanzu?'
Shima ya ɗau wurin minti 5 kafin tayi reply.
'just lying on my bed and chatting away'
'karatu fah?'
'ba sai gobe kace ba my yaya Yaseer?🥺'
Ya kalli saƙon ya sake kallo. Ko bai yi niya ba ai dole ya barta sai goben.
'Allah ya kaimu'
'Thank youuu' ta turo da emoji mai rawa, sai ya saki murmushi mai sauti yana miƙe bayan shi a kan gadon.
'Ina kallon drama ɗinnan da kika tura min, and it's interesting' ya mayar mata don bayi son hirar tasu ta tsaya.
'wanne?😱'
'WLGYT???'
'abbreviations ɗin shi kenan?' ya tambaye ta.
'Eh'
'yaya kaga park bogum? Handsome right? Gashi so calm and composed'
'ina son IU ita jarumar amma saboda shi na kalla'
'Reina!🤨' ya sha wahala kafin ya samo emoji ɗin ɗaga gira ya tura mata saboda ba saba amfani yayi da su ba.
'Oh sorry yaya Yaseer' ta turo da emoji mai rufe baki yana blushing.
'Na manta kai ne fah'
'hmm'
'but soyayyar su akwai tsayawa a rai'
Yayi tunanin ko saƙon shi na ƙarshe yayi mata wani iri ne ta gagara amsawa ganin lokacin da ta ɗauka bata amsa ba, har ya shiga da niyyar yin delete for everyone sai ya ga tana typing don haka ya dakata.
'indeed! Ina son soyayya irin haka'
'very selfless kuma with all your heart'
'da ace ta yarda ta bi ɗan banza mai yaran nan saboda yana da kuɗi da na shiga film ɗin nan na naɗa mata na jaki kafin in dawo'
'amma kaga ko da ita da mijinta sunyi rayuwa cikin talauci amma daga ƙarshe Allah ya ɗaga yaran su'
Ya tura mata 'ban kai ƙarshe ba kada ki bani spoiler '
'oh sorry' ta sake turowa da emoji mai rufe baki yana blushing. Sannan taci gaba da cewa.
'amma ka ga da ta auri wanda ya san mutuncin ta gashi ta samu kwanciyar hankali kuma ta cika duk mafarkayyan da take da shi, sannan duk abinda zata yi koda yana ganin ba mai yiwuwa bane yana goya mata baya'.
*Reina*
Da Uncle B suke chat don yau bata jin yin wayan kuma ba zai iya haƙura ba. Ita bata sani ba ma ko tsayawa yake yi a waje har su gama kafin ya tafi gidan shi ko kuma yana gidan suke hira na tsawon lokaci haka.
Ga damuwan da ya gagara fita a kanta na rashin fitowar yaya Yaseer tunda suka dawo har aka ci abinci banda shi.
Fita daga chat ɗin Uncle B tayi ta tura ma yaya Yaseer saƙo sannan ta amsa saƙon Safina ma da ya daɗe yana jira sannan ta dawo kan Uncle B.
Ganin yaya Yaseer yayi reply ta fara amsa Uncle B tukunna don shi yafi son da yayi magana ta buɗe ta amsa bayi son jira ko na second goma. Amma kafin ya rubuto saƙon gaba ta san har zata yiwa yaya Yaseer reply ta dawo.
Haka ta cigaba da yawo a tsakanin su biyun ta ajiye Safina a gefe zasu ƙarasa nasu gobe.
Hirar su da yaya Yaseer yayi mata daɗi sosai saboda zantawa suke yi a kan abinda take da interest a kai, amma Uncle B da tayi masa tayin kallon gwale ta yayi, ita ko favourite one ɗinta ma ya kalla saboda suyi labari a kai irin haka sai gwada mata yayi kallon fina-finai irin haka shirme ne da shiririta gwamma tana kallon abinda zata ilimantu ko kuma american action films. Toh ita ba namiji ba mai ya haɗa ta da action film?. Da ta faɗa mishi magana makamancin haka sai yace mata shima ba mace ba mai ya haɗa shi da labaran soyayyar ƙarya ayi ta saka ma mata wani expectations da ba shine ba ana gwada musu wasu na mata-na mata a matsayin maza suna kallon mazan dake tare da su kaman basu kai ba.
Tana da abin cewa a lokacin amma tayi shiru don idan ta san na faɗa bata san na mayarwa ba amma bata san kallo da ake yi saboda nishaɗi kawai yana da wannan tasirin ba ma.
Gashi yaya Yaseer har sai da ta manta da shi suke hiran ta shiga zuban zance sai da ya tunasar da ita.
Dogon saƙon da ta tura mishi daga ƙarshe ya saka tayi jinkirin dawowa kan chat ɗin Uncle B, sai ga saƙonnin complain rututu. Shi bayi son wulaƙanci mene da mene sannan ma ya sauƙa daga online ɗin.
Saƙon Yaseer ta hango ya shigo ta notification bar don haka bata cewa Uncle B komai ba ta fice a chat ɗin shi ta koma na yaya Yaseer don ta lura idan ba bauɗe mishi take yi ba wani lokaci ba zasu dinga zaman lafiya ba.
'Respect shi yafi komai muhimmanci a soyayya da auratayya ma baki ɗaya, saboda idan couples suna respecting juna za'a samu mutunta juna, amana, tallafawa, tausayawa, da abubuwa masu yawa, Amma idan babu respect haka soyayya yake saurin mutuwa kaman an hure candle, zaman aure kuma zai ƙuntata kaman yanda mutumin da taƙi aura yake yiwa matar da ya aura a madadin ta'
Ganin saƙon Yaseer tayi kaman yana yi da ita ne da Uncle B har sai da ta karanta ƙarshen shi ta tuna labarin film suke yi.
Sai tace 'Haka ne, but love is difficult yaya Yaseer, yana zuwa da sadaukarwa masu yawa'
'no ban yarda ba Ma Cherié (my dear). love is the easiest thing in the world saboda baka ɗaukan sadaukarwan da kayi ma masoyin ka a matsayin wahala sai wani mataki na nasara na ƙara mallakan zuciyar abinda kake so. Daga ranar da ka fara kallon wannan sadaukarwan da wani ido daban kuma ya kamata ka dasa ma soyayyar ka alamar tambaya saboda kai ma baka san wani irin sadaukarwa partner ɗin ka yake yi ba tare da sanin ka ba ma.'
'love doesn't exist without effort Reina, always remember this'