Sashe 33
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suka ja motocin duka suka bar wurin har da wanda aka tilasta Irfan shiga tun Alhaji Salisu bai ida ƙarasowa ba, a cewar yaseer yayi yaro sosai kada ya koyi rashin kunya ma manya, dalili kenan da ya saka har yayi magana ya gama shima Suhail bai tsoma baki ba.
.......
*Reina*
Baki buɗe suke bin gidan da suka shigo don tun daga gate ɗin gidan abun kallo ne.
"Daddy, gidan ka ne wannan?" Reina ta tambayi Alaji Abdou dake zaune a kujeran mai zaman banza, ita kuma da Maama suna baya sun saka Alhaji Tahir a tsakiya.
"Nikam ba kin san gida na ba?" Ya bata amsa.
Parking suka yi a daff mashigar gidan, Alaji Abdou yace musu su fita sun iso sannan Sabir ya fito ma Alhaji tahir wheel chair ɗin shi suka taimaka suka ɗaura shi.
"Daddy mai ya same ka baka tafiya?" Maama ce ta kasa haƙuri ta tambaya.
Sabir bai tsaya jiran su ba yayi ciki kasancewar yaga motocin gidan a mazaunin su banda na Yaseer. Daman lokacin da suka yi video call har sun kamo hanyar dawowa kuma ya sanar dashi office zai wuce daga nan.
Zai je ne ya samu labarin abinda ya faru dalla dalla a bakin su Suhail.
Murmushi kawai Alhaji Tahir yayi mata, ya kunna wheelchair ɗin kasancewar ta electric, sannan akwai yanda aka yi masa a gefen matakalar shiga gidan da zai iya haurawa ba tare da taimakon kowa ba.
"Muje ku huta kun ji" yace da su.
Sai Reina ta riƙe bayan wheelchair ɗin, Maama suka jera da Alaji Abdou zuwa ciki.
.....
Lokacin da Alhaji Salisu suka koma gidan cikin maɗaukakiyar tashin hankali ya ɗan ji daɗi ganin ginin yana nan lafiya, da abun sai yayi masa yawa idan bomb ɗin gaske ne.
An mayar da Hajiya Hauwa parlour amma Tana miƙe shame-shame ana kan faman fifita Zaheera sai kuka take yi, shock ɗin ganin Alhaji Tahir ne har yanzu bai sake ta ba.
"Hauwa'u, Hauwa!" Ya faɗo parlon babu ko sallama "Sun tafi dashi, sun tafi da Jamal"
Tsugul ta miƙe, "sun tafi dashi ina? Su waye suka tafi da shi"
"Wannan bala'i mai suffar mutum ɗin mana, Yaseer. Yaseer dai ɗan Kamalun Jama'are."
"Na shiga uku! La ilaha illa anta subuhanaka inni kuntu minal zalimin, Ina ya kai min yaro?"
Wasu ƴan bikin da suka ga ba lafiya ba sun saɓule jiki sun gudu tuntuni, Musamman da Alhaji Tahir ya gargadi Hajiya Hauwa ta kikaye ranan da zai sake waiwayen su kafin ya saka yaran shi a mota suka tafi. Amma ƴan gulma kam suna nan basu tsoron ta kife idan dai zasu samu na bada rahoto.
"Daddy baban Reina yazo ya tafi da ita" cewar Zaheera.
Hajiya Hauwa dake niman ɗankwali da mayafinta ta dakata, ita jin sunan Jamal shaff tama manta, sai da ta kalli Alhaji Salisu cikin ido kana tace "yanda naga Alhaji Tahir Allah yasa naga Annabi Muhammad s.a.w haka Wallahi, kuma kowa a nan ya gan shi"
Munafukai suka shiga gyaɗa kai cikin tabbatarwa.
Amma daga rantsuwar da tayi ya daina jin komai, kunnen shi yayi mishi wani dummm sai ƙaran da yake ji kaman zai fasa mishi kai ga ganin shi da ya koma dishi-dishi.
Hannun kujera yake ƙokarin riƙewa Amma bai kai ga kamawa ba ya faɗi ƙasa warwas, ƴan parlo suka saka salati.
Bomb! lallai da gidan ne da abun cikinta ya ƙone ƙurmus da yafi mishi alkhairi.
.....
Ba yabo ba fallasa mutan gidan suka amshe su, Suhail ne kawai yaƙi zama a parlon bayan sun shigo, Aicha kuma ta bi Yaseer office.
Reina taso ta gane wasu daga cikin mutan gidan, amma gidan da suke ciki aka sanar da ita sune masu shi da kuma suturun dake jikin su ya musanta wa basirar ta, ba su ɗin bane, wannan ba iyayen yaya Yaseer ɗin ta bane.
Suna maƙale a jikin Alhaji Tahir kaman wanda za'a raba su har aka kira sallan azahar kafin Saudat ta shiga dasu yin Sallah mazan kuma suka tafi masallacin dake jikin gidan, wannan karon har da Alhaji Tahir tunda yanzu ɓuya ya ƙare.
A maimakon a haɗu wurin cin abinci kaman yanda suka saba sai suka bar dining ɗin ma Alhaji Tahir da yaran sa su samu faragar zantawa, mutan gidan kowa yayi ɗaki da abincin sa.
Sosai Reina taci abincin, domin bayan yunwa da take ji har da Appetite da ta kwana biyu bata da shine ya dawo mata a yau. Shi Alhaji Tahir ya ma kasa cin abincin sai dai ya kura ma wannan ido ya shafa kan wannan.
Muryar Reina na rawa tace
"Daddy, har yanzu ina ganin kaman mafarkine anjima zan tashi komai ya koma kamar da. Idan suka aura min Jamal zan mutu daddy, dan Allah ko a mafarkin ne ka fito ma Ummi itama da daddyn Niger kace musu baka so"
"In sha Allah ko hanyar da kika taka Jamal ba zai sake bi ba sarauniya ta, zan zame miki katangar da bai isa ya haura ba balle ya riske ki, za'a shiga tsakanin ku yanda ko kallon arziƙi na sani ba zai sake miki ba bare na banza"
Maama ta amshe da "daddy ina yanzu muma zamu dawo rayuwa tare da kai?"
"In sha Allah" ya amsa da murmushi. Bai san ta ina zai fara ba amma zai maida farinciki a rayuwan yaran shi.
.....
Bayani Muhammad yake ma Yaseer, suna zaune a wasu jerarrun sofas a tsakiyan office ɗin, wanda aka tanade su na ganawa da baƙin da ba'a buƙatar sai an dangana da meeting Room, amma kaman hankalin Yaseer ɗin bayi jin shi baki ɗaya.
Daman idan banda fitina kowani ma'aikaci na hutawa a weekends shine su ya ɗago su.
"YK" Muhammad yayi ƙoƙarin dawo da hankalin shi gare shi.
"Ina so in gan ta Muhammad" shine kalmar da ya fito daga bakin Yaseer ba tare da ya sani ba.
Numfashi Muhammad ya furzar, tuni shi daman ya gane matsalar. "Toh kaje ka ganta mana, daman ina tana gidan ku yanzu?"
Ya kalle shi, "yaya aka yi kasan wa nake nufi?"
"Yaya za'a yi ba zan san wa kake nufi ba? Kana da wata bayan itan ne? Akwai wata mai rabin matsugunin da ta samu a zuciyar ka ne?"
Gwada ƙirjin shi Yaseer yayi "wurin da ta samu tsana ne ya cika shi ba komai ba"
"Ko wurin tsanar ne Jamal da yayi maka sanadi yana da kwatankwacin shi?"
Yaseer ya yamutsa fuska "Yaya zaka haɗa ta da wannan abun?"
Muhammad ya taɓe baki daidai lokacin da aka ƙwanƙwasa kofar, kafin Aicha ta buɗe ta shigo kanta tsaye bakin ta ɗauke da sallama, tunda yau ba kaman sauran ranar aiki bane.
Tana cikin jin daɗi, kallo ɗaya zaka yi mata ka fahimci hakan sanin cewa Yaseer yana sane da za'a kawo Reina gidan su amma ko damuwa yaje ya dubata bai yi ba, alamu suna son nunawa yanzu Reina bata gaban shi.
"Yayan mu ga papers ɗin" ta faɗa tana miƙa mishi takardun da ya sakata tayi reviewing sai ta kawo ya saka hannu.
Karɓan takardan yayi ya ajiye su a kan teburin gaban shi, ya ciro fountain pen a aljihun rigan jamfan shi.
"Yaushe zaki tafi gida?" Ya tambaye ta yana signing papers ɗin.
"Zan jira ka mu tafi tare"
"Muhammad yaje ya sauƙe ki zan yi dare sosai" ya faɗa cikin muryar bada umarni babu yanda ta iya bayan amsawa da toh.
Ana sallan la'asar Alhaji Tahir da yaran shi suka tafi gidan Ummi, duk yanda Ummi taso yin haƙuri hankalin ta ya kasa kwantawa a kan lamarin Reina, kada abu bai tafi yanda aka tsara ba, duk da su aunty zeenat da suka dawo sun shaida mata sun ga alhaji Tahir ido da ido itama tana son saka shi a nata idanun, shine zuwa la'asar ta sallami kowa ya koma sai yaranta kawai kafin su Alhaji Tahir ɗin suka je.
don haka koda Aicha ta koma gidan su yaseer bata same su ba, amma itama taji tana son sake kallon Reina, ko wannan karon ba zata ji wannan faɗuwar gaban ba tunda shi a yanzu ba ta ita yake yi ba.
Alhaji Tahir ya bawa su Ummi labarin Abinda ya faru da shi sama-sama kuma an ci kuka musamman da aka tuna da Fauziyya, haka itama Reina ta shiga zayyane masa irin rayuwar da tayi a gidan Hajiya Hauwa, nan ma aka sake wani kukan na tausayin ta, har sai da aka musu faɗa ita da Maama kafin suka yi shiru, Ummi ta ɗauko mata maganin ta da yake wurinta ta sha. Sai a lokacin Uncle B ya shigo hirar tasu, Alhaji Tahir ya shaida ma Ummi ya san da zancen shi har sun yi magana a waya ma.
Basu dawo ba sai can dare, kusan rabin gidan kowa ya kwanta, duk yanda suka so bin Alhaji Tahir ɗakin shi haka Kamal ya hana Saboda ba wai ya samu cikakken lafiya bane yana buƙatar isasshen hutu.
Saudat ta basu wadataccen ɗakin da aka tsaftace shi aka gyara, komai akwai.
A karo na farko bayan tsawon shekarun da suka haura goma, Reina da Maama suka kwanta a ɗaki ɗaya, a gado ɗaya, rungume da junan su, cikin daɗin rai.
.
.
.
Bata yi tsammanin zata iya barci har a tashe ta tayi Sallah ta sake wani barcin har gari ya gama wayewa ba tare da ta saka mahaifin ta a idanu ba, ko don ma ta tabbatar ba mafarki take yi ba. sai dai shi barci bashi ne idan kaci biya dole, kuma ta kwana biyu tana karɓan wannan bashin, duk da dai ganin ta tashi a wannan gidan ya samar mata da nutsuwa.
Brush kawai tayi ta tako ta fito daga ɗakin tana hamman gajiyan da yake tambayar ta a yanzu, idan taje taga Alhaji Tahir sai ta dawo ta ɗan ƙara barcin ko kaɗan.
Janyo ƙofar tayi tana takawa da baya kafin ta juyo shi kuma ya zo wucewa da kofin tea a hannun shi.
"Hankali!" Yace saboda kada ta ƙona kanta dukda yana ƙoƙarin kauce mata.
Muryar tashi a maimakon ta ankarar da ita sai tayi saurin juyowa a firgice Idanun shi ya shiga cikin nata.