← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 117

Sashe 103

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aicha ta miƙe a lallausan gadon bayan ta sauya kayanta zuwa na barci, ta rufu ta rufe idanu Amma barcinta yau kaman yayi ɓatan hanya ko dan tayi da yamma ne?. Can sai ta samu kanta da tunanin haɗuwar su da Rafeeq har zuwa yau, ƙwaƙwalwarta ta kasa gane wani irin mutum ne, gashi kaman mutumin banza amma wani lokaci sai yayi halin mutanen kirki, saidai taƙama kam akwai kuma ya iya yaɓawa mutum magana.

Wasa-wasa saida ta ɗaga waya ta kalli agogo ya gwada mata ƙarfe 2 da ƴan kai sannan tayi ƙoƙarin ture tunanin Rafeeq daga kanta ta samu ta rintsa, abinda bata taɓa yi a kan wani ɗa namiji ba bayan Yaseer.

......

*Reina*

Sai bayan sun samu isasshen hutu jikinta ya ɗan wartsake kafin a yammacin rana na uku suka fara fita.
_Tarihi tashan Kahvecisi_ shine first stop ɗin su yanda suka sha shayi na gargajiya sannan suka shiga miƙe ƙafa a _Hamamönü old town_ a yayin da rana tayi sanyi. wuri mai yawan shagunan kayayyaki, shagunan maƙulashe da Cafés, ga gidaje samfurin ottoman empire wato daular ƙasar na lokacin baya da ya shuɗe.

Reina tana cikin wata sky blue English gown da farin mayafi da ta yane kanta dashi tana rungume da hannun Yaseer a kirjin ta wanda ke cikin farin shirt da wando navy blue. suna takawa a sannu suna hira da bayyana ma juna ƙauna da soyayya a cikin idanun su da kusancin su ba tare da damuwan ƴan sa ido ba domin kowa harƙan gaban shi yake yi babu irin su Aunty Aina a wurin, sannan bayan su akwai masoya irin su da yawa da suka zo yin ban ruwa ma furen ƙaunar su.

Basu koma hotel Room ɗin su ba sai 10 kuma suna shigowa niman hutu suka fara tunda sun ci sun ƙoshi ga kuma kayayyakin da Reina ta jido ma kanta da Yaseer ma da kuma wanda zata yi tsaraba da su.

A ranar dai ta samu ta tsira amma washegari basu iya fita a lokacin da suka yanke ba dukda da nisa zasu tafi a ranan saidai Yaseer ya gwammace su ƙara lokacin tsawon zaman da zasu yi.

Tafiyan awa 3 suka yi zuwa _Cappadocia_ duk da sun so makara don sammakon zuwa ake yi yanda zaka mori lokacin ka a tsanake.
Suka shiga hot air balloon aka ɗaga da su a sararin samaniya, Reina bata san tana da Acrophobia ba wato fear of height saida ta kalli ƙasa bayan sun fara tashi tana jin kaman hantsilowa zata yi.

"Daina tunanin komai ki kalle ni" Yaseer yace yana rike da ita a jikin shi ya tallafo fuskar ta a cikin tafin hannun shi. Amma wai sai gashi bayan sun sauƙo tana cewa daɗi su koma, haka kuwa suka sake komawa ihun da tsoron duk ta sake saidai ba kaman na farko ba. Juyawan da kanta yake mata ya saka saida suka huta suna kallon sarari da fili fallau iya ganinka wanda korayen shukoki da furanni suka masa ƙawa ga kuma masu hawa baloon ɗin a bayan su wasu har sun fi Reina ihu da tsoro wasu kuma sun riga da sun saba.

Suka yi lunch a _Seten Anatolian Cuisine_ sannan aka kai su wuraren tarihi suka ɗauki hotuna da yamma suka koma cikin Ankara.

106

*Abuja, Nigeria*

Ita da Asal suke rayuwar su suna komai a tare, sai kuma Rafeeq da ƙafar shi bata yankewa a hanyan zuwa gidan har ya zamo tare da shi suke karyawa da cin abincin dare. Kowani safiya Asal da take aji biyu a jami'a zata tafi makaranta itama Aicha ya saka ta a gaba su wuce office.

Da ta tambaye shi ganin ya saka an yi mata cabin a cikin ofishin shi suna fuskantar juna sai yace cemata yayi a zallan wajen office zata yi masa aiki?, Kuma bata da gogewan da zata iya aiki da Teams ɗin dake ƙarƙashin shi amma shi zai iya manage. Maganar ya taɓa ta amma yaya ta iya?.

Aicha ne tsaye a gaban frying pan dake kan gas, hannunta riƙe da matsamin non-stick tayi readyn kwashe plaintain ɗin da ta zuba domin ya ɗauko soyuwa, kuma shi ne abu na kusan karshe da zasu haɗa na breakfast domin har Asal ta riga da ta fara shirya table.

Ƙarasowa jikin gas cooker ɗin Asal tayi ɗauke da tray, da bowl guda uku masu farfesun kifi a kai.

"Aunty yayi?" Ta tambayi Aicha don haka ta juyo ta kalli abinda take gwada mata.

"Ki ƙara ma yayan ki" tace tana nuni da wanda yafi yawa a ciki, tunda shine mai son kifin ya saka su yin farfesun shi da sassafe ai sai ya shanye.

Komawa Asal tayi ta ƙara mishi kaman yanda Aicha tace kwanon ya cika sannan ta fita da tray ɗin dining inda Rafeeq yake zaune da takardu a gaban shi kaman ko yaushe.

"Yaya ka fara ci kafin ya huce"

"Darling fah?" Ya tambaya ƙasa-ƙasa.

"Tana zuwa yanzu,"

Ya haɗe kan takardun da suka zamo mishi wajibi ya basu muhimmanci a gaban ta idan har yana son kasancewa tare da ita na wani lokaci. Idan so samu ne tunda yau asabar farkon weekend a gidan shi ya kamata ya wuni ya huta shiyasa ya tattaro ayyukan da za su zauna a jikin shi su kasance tare.

ƙamshin kifin yana shiga hancin shi ya san ba Asal bane tayi, don ya fara bambance girkin matar shi har a ido.
Ya kai spoon na farko baki sai gata ta fito riƙe da kwanon plaintain da sausage a hannu ɗaya sai kuma na omelette da ta soya yanzu-yanzu da ɗumin shi a ɗaya hannun ta jera a gefen sauran warmers dake wurin, sannan ta shiga zuba ma kanta abinda zata iya ci.

"Ina kwana sir" ta gaida shi don sa'ilin da ya shigo gidan tana kitchen.

"Lafiya ƙlau, kin tashi lfy"

"Alhamdulillah" ta amsa muryar ta a sake Saboda Asal kada ta fahimci wani abu amma ta haɗe gabas da yamma kuma ta ƙi kallon shi.
A lissafinta daren yau a gadon ta zata kwana a gidan Daddy ko gidan Abbah, amma jiya da daddare Rafeeq ya tuna mata bata cika satinta ba tukun tunda sai Laraba ta fara masa aiki.

Ta samu wuri ta zauna taci gaba da harƙan gaban ta.

"Uhmm, akwai wasu takardun da nake so mu duba tare" can ya ƙare yayi magana.

Sai ta mayar da cokalin da tayi nufin kaiwa baki ta ɗago ta dube shi. "Yau Saturday fa"

"Kin amince sai talata kafin ki koma kenan?"

Shiru tayi kawai tana kallon ikon Allah, Ta gagara gaskata wai har ta kwana shida a garin Abuja ita kaɗai sannan kwanan ta uku a gidan Rafeeq a ƙarƙashin kulawar shi ba tare da sanin kowa ba, domin bata san ta inda zata fara yima iyayenta bayanin hujja ko dalilinta na yin hakan ba.

"Shikkenan bari na gama sai in shirya mu tafi" gobe dai duk ƙulafucin sa haka zai haƙura ya barta ta tafi kuma ba zata bar Abuja ba tare da tayi blocking ɗin numbern shi ba.

"Ba sai munje office ba, zamu iya a nan"

"Okay" tace ta ƙarasa cin abinci suka tattare wurin zasu tsaftace abinda suka ɓata Asal tace taje kawai zata ƙarasa.

Dawowa tayi ta samu Rafeeq ta zauna a kujeran da yake kallon nashi fuska babu annuri tace "dame zamu fara?" Tana ɗaukan ɗaya a cikin takardun ta shiga dubawa don kawai kada ta kalle shi cikin ido.

"Aysh. Nayi tunanin mun riga mun wuce wannan matakin"

"Wani mataki kenan?" Tace still idanunta a kan takardan hannunta.

Sai gani tayi ya zare takardan don haka dole ta ɗago ta dube shi. "Mun fahimci juna right? We Said we're going to give this a try"

"Amma ajiye ni a nan yana da alaƙa da hakan ne?"ta tambaya tana kallon shi

"Alƙawari kika ɗauka, ni ina bawa alƙawari muhimmanci domin idan na ɗauke shi ma kowaye ne sai na cika balle ma ke. Mu fuskanci juna Please Aysh. This could work, ina son ki da tsarkakakkiyar niyya. Just say yes and we could make this official"
Zata yi ƙarya idan tace bata fara jin Rafeeq a cikin zuciyarta ba zuwa yanzu. Gani take yi kaman dabara ya mata ya samu ya dabaibaye tunaninta har take ganin shi daban da sauran maza, sabida bata taɓa haɗuwa da irin shi ba.
Yanda ya ɗauki nauyin ta yake kula da ita kuma ya ƙara masa ƙima a idanunta, juya ta yanda yaga dama da yake yi ne dai bata so.

"Ko ƴata ce ba zaki iya riƙewa ba?"

Saurin girgiza kai tayi ita shine damuwan ta ba ƴar shi ba, yanda zata cire Yaseer baki ɗaya daga zuciyarta ta bashi gurbin shine tunaninta, amma ɗa na kowa ne tunda ita ma bata fi ƙarfin ta haifa ta mutu ta barsu a hannun wata macen ba.

Yaci gaba da cewa "Zan iya barin ta taci gaba da zama a wurin Jadda, amma sauran ƴan uwanta da zasu zo daga baya ma tare zasu taso domin ina son yara na su haɗe kan su."

Ta sake girgiza kai. "Ba haka bane, idan dai zuciyata zata amince da kai me zai hana ta amince da jinin ka. Komai ne dai yazo min da sauri I'm seriously confused" ta ƙarashe tana dafe goshinta tare da kallon wani wurin.

"Shikkenan, mu bi komai a hankali ko?" Yayi ƴar ƙaramin murmushi, daga nan ya kawar da zancen ya ɗora da mata bayanin aikin da zasu yi.

komai na tafiya musu lafiya a wannan rana mai albarka kafin lokacin da notification ya shigo wayanta ta duba taga Yaseer ne ya ɗaura hoto.
Tashin hankalin da ta shiga a dalilin hakan ya saka Rafeeq yanke shawarar taƙaita musu wahala duk su huta.

.......

*Reina*

"...yayi kyau! Ana samun cigaba cikin gaggawa, I'm impressed gaskiya"
Chapter 103 · 0% Book details