← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 117

Sashe 100

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani babban office da aka rubuta "Finance Director" suka isa, ma'aikaciyar ta ƙwanƙwasa sau biyu, tana hango shi ya amsa ba tare da ya ɗago ba sannan ta tura ƙofar dake na glass ta shiga tana yiwa Aicha iso.

"Sir ga baƙuwar ka tazo" tace da Rafeeq. Still bai ɗago ba ya amsa da "thank you Rachel" daga haka ta juya ta barsu su biyu a office ɗin.
Kuma tana fita ya ajiye pountain pen ɗin hannun shi ya ɗaga takardan da yake rubutu a kai ya saka a a cikin wani folder sannan ya ɗago ya dube ta.

"Makara a farkon ranan aiki ko Aichatou?" yace saboda yana tuna kiran ta da Darling da yayi jiya ya saka ya kusan wargaza shirin sa. Saida yayi mata lauya ta hanyar da ya san zata aminta amma kuma zai ƙara ɓata kan shi ne a idanunta.

Tambayar da tayi mishi a jiyan shine "A ina ya san sunan ta darling?"

Sai ya amsa mata da "tun yaushe aka ɗauki darling ɗin aka baki? Na ɗauka laƙanin duk wata mace mai kyau ne ko kuma wanda ka saka a zuciyan ka shiyasa na dangana ki da shi" a lokacin bata sake ce masa komai ba.

Amma ta fahimci wannan tasbihin da yake yi a koda yaushe istigfari ne yake yi ma Ubangiji saboda shi karan kan shi ya san zunuban shi sun yi yawa.

"Umm..hmm?" Ta sake jiyo muryan shi.

"Sorry sir, ba za'a maimaita ba" gwamma ta sauƙe kai su rabu lafiya shi yafi.

Sai taga ya miƙe yana mayar da hula kayi domin shadda ne a jikin shi ruwan toka amma ko ita da take adawa da halinsa ta san yayi kyau.

"Wani team zan yi joining kenan?" Ta tambaya bayan taga ya fito daga bayan teburin yana tunkaro ta.

Saida ya karaso daff da ita kafin yace "da nace miki zaki min aiki cemiki nayi a office? Biyo ni muje" ya miƙa mata foldern hannun shi yana fita daga ofishin babu yanda ta iya dole tabi bayan shi.

Sai taga Rachel a zaune a bayan teburin dake wajen office din, wato sakatariyar shi ce?. Haka suka jera suna tafe duk ofishin da suka wuce sai idanun ma'aikatan ciki sun yi musu rakiya, domin idan tace bin shi a baya zata yi da wannan tafiyan shin ita da ta saba da hanzari saboda yanayin aikin ta, to fa zata yi ta tuntuɓe ne da ƙafar shi ta ƙara masa dalilin da ba zai sake hawa doki ba.

Elevator ɗin executives suka shiga a hanyar su ta sauƙa a maimakon na normal ma'aikata, bata yi mamaki ba tunda ta ga estate ɗin da yake rayuwa tana da tabbacin kamfanin nasu ne.

Bai sake mata magana ba itama haka har suka fita gaban ginin lokacin da drivern shi ya ƙaraso da mota, bodyguard ɗin shi ya buɗe mishi ƙofar baya ya shiga sannan shi ya shiga mazaunin mai zaman banza, aka barta a tsaye tana kallon cikin motan da ake jira ta shiga.

Maza uku ita kaɗai mace, taɓɓ! Ai ko hauka take yi ta san ta kuskura ta shiga motan nan to ba zata fita lami lafiya ba.

Rafeeq bai san ƴar rigima ya auro ma kan shi ba saida ya samu kan shi a gaban motan Aicha tana tuƙa shi tunda shi yana da raunin da zai hana shi tuƙi.
"Sai ina?" Ta tambaya bayan ta yanki last titin da yayi mata kwatance.

Kiyi dama zaki ga wurin sai ki samu wuri kiyi parking.

Kaman yanda yace tayi, suka tsaya a gaban wani hotel.
"Sai ka fito" tace tana miƙa mishi briefcase ɗin shi da ta ajiye a seat ɗin baya.

Kallonta yayi yana ɗage gira ɗaya sannan ya miƙa mata wani takarda da ya ciro a folder ɗin daga jakan.
"Karɓa"

Karɓan tayi ta duba ko wani yarjejeniyan ne, kuma bata kuskure ba shina Amma ba na tsakanin su ba.

"Na menene wannan?" Ta tambaya tana ɗagowa ta kalle shi.

"Aikin da zaki yi min kenan. Akwai investment da muke so muyi a project da kika ga sunan shi a sama, amma abinda zamu samu a ciki bai isa ba, shine nake so kiyi amfani da surutun kin nan ki mana ciniki har su amince da percentage ɗin da muke so"

"Shine a hotel?"

"Ba'a meeting a hotel ne?" Ya hangi fargaban dake a idanunta, da alamu kuma tana da experience marasa daɗi a kan irin haka domin har yanzu harassment na ma'aikata mata yana wanzuwa a cikin industries dukda suna iya ƙoƙarin su wajen ganin sun yi yaƙi da hakan. Amma idan yana tare da ita ko ƙwaro bai isa ya cutar da ita ba balle ɗan mutum. Sai ya sassauta murya ba tare da ya ɗaga idanun shi a kanta ba yace "Ina tare da ke, kada kiji komai"

Sai ta ɗago daga steering da ta ƙurawa idanu ta dube shi sannan ta sauƙe numfashi tana cire seatbelt ɗinta ta buɗe kofa ta fita. Ya murmusa, yana son mace mai ƙarfin zuciya da jajircewa a kan abinda ta saka a gaba kuma lucky him, ya samu.

Kamar wasa sai gashi cinikayyar ta faɗa, domin Aicha bata sarara musu ba har saida suka amince, shi kuwa gogan naku yana gumm da baki idanun shi a kan duk wanda zai yi yunƙurin mata kallon da ya wuce na ƙoƙarin fahimta, har aka samu kowane ɓangare suka saka hannu a kan takarda ya basu hannu suka gaisa bisa ƙa'ida sannan ko second biyu bai ƙara ba balle a samu ɗan kasadan da zai miƙo mata hannun shi, sai ji tayi ya riƙo hannunta sun bar ɗakin taron.

Ta ɗauka shikkenan sun gama amma daga wurin wani yarjejeniyan suka ƙara wucewa suka ƙulla, tare suka ci abinci suka samu suka yi Sallah Sannan aka cigaba daga inda aka tsaya, kafin la'asar duk tayi laushi. ashe jin daɗin ta Yaseer yake barin ta tayi a YK & Co, domin a can ita take tursasa kanta tayi mishi aiki da yawa har ta gaji.

"Shiga ya mayar da ke" yace yana buɗe mata bayan motar shi da ya iso ya same su a wurin ganawa na ƙarshe.

"Kai fa?" Ta samu kanta da tambaya tunda ta san ko bari masa motar ta tayi ba lallai ya iya driving ba.

"Kada ki damu, na kira drivern office" sai yanzu ta lura ba motan da zasu fita a cikin ta da safiya bane, kuma drivern ma ba shi bane.

Ta taka ta shiga tana gyara zaman riga da mayafinta, ya jira ta gama sannan ya rufe mata ƙofan yana tsaye har saida ya daina ganin su.

Tana isa ɗakin hotel ɗinta bata zauna ba saida ta ɗauro alwala tayi sallah sannan ta rage kayan jikin ta ta faɗa gado.

7:05pm.

*Rafeeq*

"Hello" muryarta na barci ya sake shiga kunnen shi, sai ya jingina bayan shi da jikin kujeran da yake zaune, ya lumshe idanu ya buɗe su kafin ya amsa da.

"Gado kika koma?" Shi sai yanzu ma zai tashi a office ɗin.

"Kaine dama? Na shiga uku" tace yana jin yanda muryarta take wartsakewa.

Sai ya samu kan shi da murmusawa "daman kiran wa kike tsammani? Sannan amsa kira kike yi baki duba mai ita?"

Yana jin motsi alamun ta tashi zaune ko kuma ta sauƙa daga gadon. "Idan da ina dubawa da wannan ma ba zan amsa ba" ya ji karan buɗe ƙofa tare da rufewa, sannan ya fara jin karan zuban ruwa daga famfo.

"Tunda kin yi kuskuren amsawa sai ki shirya ki fito, I'll pick you by 8. Look pretty."

Ai kuwa babu inda zata fita, idan ya isa ya shigo ya fitar da ita.

105

4:07 agogon Turkey.
2:07 agogon Nigeria.

JW Marriott hotel.

Jingine take da saman gadon sanye da baƙar rigan da yayi nasaran barin jikin Yaseer ya dawo nata, saidai ita bata da confidence ɗin da zata bar nata kirjin a waje kaman shi don haka ta haɗe boturan wuyan tass. daga kunkumin ta zuwa ƙafanta kuma yana rufe cikin farin duvet da ya wadaci saman gadon, da waya ƙare a kunnen ta tana magana a cikinsa kaman bata so.

"....kuma wlh kafin ku kamo hanya ki sanar da ni don ina da saƙon abubuwan da nake son ki kawo mun"

Idan saƙon ne ba gwara ta bayar tun yanzu ba, yanda idan suna zagawa ta gani sai a siya mata. Amma sai amsawa tayi da "Toh" kawai domin bakin yayi mata nauyi.

Aunty Aina ta ɗan yi shiru kafin tace "Reina ko ba Lafiya ne?"

Satan kallon Yaseer dake juya mushroom soup ɗin da ya saka a kawo mata tayi, yana sanye ne da tank top duk damatsun nan a waje, suna haɗa ido ta kawar da kanta domin saka ta a gaba yayi ya tsare ta da idanuwa.
Ta ɗan buɗe baki da kyau tace "Lafiya ƙalau, mai kika gani?"

"Mai na ji dai. Muryar ki ta koma kaman na Maama, kaman ba wacce aka keta hazo da ita ba"

Ɗan dariyar ƙarfin hali tayi tace "jet lag ne kawai"

"Jet lag ko? Ki zauna kiyi ta raki dai. Kika dawo mana ƙasar nan babu ciki a jikin ki ni da ke!"

Shima "toh" ta amsa mata, dariya ya kama Aunty Aina sosai har Reina ta katse kiran.

Spoon mai zurfi da Yaseer ya kawo bakinta ya saka ta ɗaga ido ta dube shi. Murmushi mai annuri ne a kan fuskar shi, itama sai ta samu kanta da murmusawa tana sauƙe idanunta a kunyace ta buɗe bakin ta karɓa a hankali, ya mayar da spoon ɗin cikin bowl ɗin dake dauke da sauran soup ɗin sannan ya saka yatsa ya goge mata yanda ya ɗan ɓata mata laɓɓe ya kai bakin shi ya tsotse.
ya sake ɗibo wani ya kawo bakin ta yana tambayan ta "sauran wane?"

Kiran wa'inda bata samu taje tayi musu sallama ba take yi bayan sun kira Ummah, Daddy da ummi sun sanar da su sun iso lafiya.
"Aunty Sajida, amma ba yanzu ba, itama saka ni a gaba zata yi."
Chapter 100 · 0% Book details