Sashe 62
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Taɓdi, paragraph!" Ta faɗa a fili bayan ta gama karanta saƙon, "ashe yaya Yaseer ma baban love ne haka" tayi dariya ganin yanda ya zubo bayani ko a baki bata yi tsammanin zai iya magana har haka ba.
'ya kamata mu ƙara wannan darasin a cikin karatun da ake mun' tace
Ya dawo mata da 'daman ina da niyya don na lura ba iyawa kika yi ba.'
'yaya Yaseer kaine kuwa?😃' ta turo da emoji ɗin nishaɗi.
Sai yace mata 'ki kwanta kiyi barci, gobe monday'
'okay Nyt, love you'
Har ta tura sai ta tuna ba Uncle B bane tayi saurin gogewa amma har ya gani.
Barcin da bata yi niyyan yi a lokacin ba kunya ya saka ta yi don tayi niyyar ko ɗan kallon ta taɓa kafin gobe kai ya cigaba da ɗaukan zafi.
Amma sai ta samu ta tashi tayi sallan dare saboda kwanciyar da tayi da wuri. Sannan tayi shirin ta a tsanake babu wani gaggawa ta fito suka ci karo da yaya Yaseer ya fito daga kitchen ɗin sama da mug ɗin tea guda biyu a hannun shi.
Sauƙe ido tayi ta gaida shi don har yanzu kunya bai sake ta ba daman shi illar yawan surutu kenan a garin zuba ka je ka faɗi abinda zai barka da jimami.
"Morning" yace yana miƙa mata mug ɗin hannun shi na dama.
Yaƙe tayi tana faɗin "A'a nagode I'm not a tea person"
"Zaki zama idan kika sha wannan" ya ƙara tura mata cup din don haka ta saka hannu ta karɓa tana godiya.
"Muje" yace ganin ta ja ta tsaya don haka ta fara sauƙa daga matakalar yana biye da ita har kitchen. Ya sakata zama a dining ɗin kitchen ta sha tea ɗin yana tuna mata hadisin manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam da yayi hani da shan abu a tsaye.
Sai gashi wani ƙamshi da daɗi na tea ɗin ya saka ta kafa kanta ta shanye tass. Tana ayyanawa a ranta Ashe dole kullum yaya Yaseer yake yawo da mug safe da dare babu fashi.
Suna gamawa kuma suka jona masu haɗin breakfast.
Suka fita ya bata kuɗi driver ya ajiye ta a school shi kuma ya wuce wurin aiki.
.....
Yau ne gobe ne goggo zata kira Yaseer Saudat ta ji shiru, gashi ita ta kasa zaunar da shi ta tambaye shi saboda tsoron abinda amsar shi zai kasance don ita ba makauniya bane ta hango abinda ke cikin idanun yaseer ɗin da dabi'un shi amma bata son ta gaskata ne saboda ace duk matan dake duniyar nan Yaseer ya rasa wa zai so sai Hafsatu Reina?.
Don haka da ya dawo daga aiki da wuri ranan juma'a ta saka shi ya je Jama'aren ya samu goggo kuma ta kira maman Abidah ta faɗa mata yana zuwa suyi shirin tarban shi.
Da sassarfa Reina ta fito ganin har ya juya kan mota zai fita, ganinta ya saka ya tsaya ya sauƙe glass ɗin windown shi yana sauraren ta "Ina zaka je yaya Yaseer?"
Taci ado tayi masa kyau cikin wata peach ɗin ɗin leshi mai dark green ɗin zare sai ta yafa mayafi dark green ga kuma jakan da ya gani ta saƙala ya saka shi tambayar "ke ina zaki je?"
"Gidan su Safina" ta bashi amsa, "amma idan ba ta wurin zaka yi ba zan fita in hau napep, yau malam Nuhu yana hutu"
"Jama'are zan je, zaki raka ni ne?"
Ta ɗan girgiza kai saboda wani wuri zasu wuce da Safinan har ta shirya tana jiran ta amma da zata so zuwa Jama'are.
~~~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
86
~~~~~~~~~~
_Quand je t'ai mis la bague au doight_
_(When I put a ring on your finger)_
_je me suis passé les bracelets_
_(I put handcuffs on myself)_
~~~~~~~~~~
"Shiga in sauƙe ki toh sai in wuce"
Zagawa tayi ta shiga suka ɗau hanya.
"Ya kamata kema ki koyi mota ki huta" yace lokacin da suka hau titi.
Sai ta murmusa "zaka na bani aron motar kenan idan na koya?"
"No siya miki zan yi, ina son in ga mace tana jan mota abun na birge ni. Sannan yana da amfani domin baka san lokacin da wani emergency zai tashi baka kusa ba"
Yanzu ma saida ya tuna mata ra'ayin Uncle B da ya saɓa nashi a kan irin haka, amma shima ya kawo mata dalilan da ta gamsu da su, sai dai tana sha'awar itama taga tana murza sitiyari wata rana.
"Toh yaushe zaka koya min?" Ko a sirrance ne zata koya ɗin in yaso bayan sun yi aure da uncle B sai ta lallaɓa shi lokacin da take amarci ta san zai yarda.
"Zan saka ki a driving school dai amma sai kin yi min wani alƙawari."
"Ko menene nayi maka yaya Yaseer"
"Ki dai bari ki ji menene ɗin tukunna Hajiya. Kada ki ɗau alƙawarin da ba zaki iya cikawa ba"
"Toh faɗamun menene Please"
"Idan na dawo zan faɗa miki" yace idanun shi a kan hanya daga nan kuma ya canza taɗin don kada ta dame shi da tambaya har suka isa unguwan su Safina.
Suna shiga layin su sai ga kiran Safinan, picking tayi tana faɗin "mutum ba haƙuri toh gani a gate ki fito"
"Taɓɓ yau wata rana? Wallahi sanin saiɓin ki ya saka nayi jinkirin kira daman zan ce miki mu ɗaga fitan zuwa wani sati don ɗazun nan aka kira mummy aunty Mami ta haifi twins, yanzu haka muna hanyar kano"
"Amma in kina da mutunci ki canza mun suna" Reina ta faɗa haɗe da jan tsaki.
"Da kin sammin naki ai tunda kina so in samu. Ba don halin ki ba sorry, zan turo miki hotunan babies bye"
Cire wayan Reina tayi daga kunnenta, Yaseer har yayi parking a ƙofar gidan su Safinan yana sauraron su.
Sai ta raɓa jakar ta tana ƙoƙarin buɗe kofa ta fita.
"Shikkenan kayi tafiyar ka zan nemi abin hawa in koma gida, akwai kuɗi a wurina"
"Rufo ƙofar in mayar da ke inda na ɗauko ki" yace yana sake kunna motar.
"A'a yaya Yaseer da ka barshi wlh" tace tana rufo ƙofan kuma.
Sai ya murmusa cikin ran shi ya ayyana ana so ana kaiwa kaisuwa a fili kuma cewa yayi "I insist"
Ta gyara zama suka ɗau hanyar komawa, sai da suka kusan isa ganin idan ta koma gidan ma zama kawai zata yi tace.
"Idan kaje Jama'aren yaushe zaka dawo?"
"Yau in sha Allah, goggo ne take nima na"
"Toh muje in raka ka"
Da wasa yayi mata tayin rakiyan amma sai yace "muje ki tambayi Ummah, idan kuma Maama tana nan sai tazo mu tafi tare tunda kinga tafiya ne mai nisa"
"Ɗazu itama ta tafi gidan Ummi, Irfan ne kaɗai a gidan shiyasa nima bani son zama duk shiru"
A waje ya tsaya da motan ya kira Irfan a waya yace ya faɗa ma Umma zasu je Jama'aren da shi da Reina don haka da suka ga ya fito sai suka yi tunanin ya riga da ya faɗa mata ne, Reina ta koma baya irfan ya shiga gaba suka ɗau hanyar Jama'are.
Tun suna tafe suna mishi hira har Reina ta fara yin barci sannan Irfan ma, suka barshi shi yana tuƙi cikin shiru.
.
.
Hannu ta ji a kan cinyar ta yana bubbuga ta tayi saurin miƙewa zaune tana ware ido ganin wata bakuwar fuska a gaban ta.
"Ki fito mu shiga ciki sai ki kwanta" cewar budurwan da wadataccen murmushi a kan fuskar ta.
Wayan ta dake kan seat ɗin motar ta ɗaga ta duba ƙarfe 5 da ɗoriya, lallai ta sha barci gashi ko sallan la'asar batai ba.
Budurwar ta matsa daga jikin ƙofar don bawa Reina dama ta fito tana kalle-kallen yalwan da wurin yake da shi ga wani iska mai daɗi dake kaɗawa.
"Sleepy head" tayi arba da fuskar Yaseer dake ɗauke da murmushin gefen baki sai taga yayi mata wani fresh ko dan yanzu ta tashi daga barci ne?.
Ya ƙaraso ya karɓi jakar ta da wayanta ya rike sannan suka jera zuwa ciki.
Babban gida ne mai shashi-shashi kuma tun daga shigan su mutane keta tuttuɗowa ana yima Yaseer barka da zuwa, Irfan na shan tsokana Reina kuma na shan kallo domin babu wanda ya santa a cikin su.
suka nufi ɓangaren da yafi girma da kyau suka tsaya a bakin ƙofa Yaseer ya fara Sallama Sannan ƙanin Kamal da ya shigo gaida goggon yayi musu iso don ko goggo da aka ce tana niman shi bata san da zuwan ba a yau.
"A'a mai gidan ashe kana tafe" tace tana miƙewa zaune daga kishingiɗen da take. "Ah-ah kishiyar tawa kenan?" ta faɗa lokacin da idanun ta suka sauka a kan Reina da ta shigo a ɗarare suna gaisawa da kawun su Yaseer, Yaseer yace ta shigo ciki da takalmin ta sannan ta cire ya saka hannu ya ɗaga mata su daga bakin hanya ya ajiye a gefe.
Ko shakka babu wannan itace Hafsatu ƴar Ɗahiru da ake magana a kanta, sannan ba sai an je da nisa ba idanun ta sun riga sun bata amsar tambayar ta.
"Wato ni yau baki ganni ba ko? Ko dayake ba laifin ki bane idon da na siyo miki ne ba mai kyau ba" cewar Irfan yana niman wurin zama a bakin shimfiɗin ta.
"Kan ka ake ji" ta gutsuri goro ta tauna tana kallon shi a yatsine kana ta taɓe baki ta mayar da hankalin ta wurin Reina da ta durƙushe a can bakin ƙofa kaman mai jiran hukunci.
"Kishin ne ya motsa da ba zaki zauna kusa da ni ba?"
Murmushi Yaseer yayi yace "mu ƙarasa kada ta ɗauka tsoron ta kike"
Ta miƙe har tana tuntube da bakin carpet ɗin dake baje a tsakiyar parlon, "kiyi a hankali dan Allah Reina bata cizo" cewar yaseer yana kiyaye mata takun ta ita nata idanun suna gaba, goggo Halime tana kallon su duka biyu gashi ya wani riƙo jaka kaman daman riƙewan shine aikin shi har suka isa gaban goggo sannan Reina ta sake zuba a kan guiwowin ta.