Sashe 46
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Furzar da numfashin ɓacin rai yayi ya rufe box ɗin, ya tsani sai a lokacin da yake da buƙatar abu ya samu babu, shi yaya zai yi da yaran nan ne su daina saka mishi abubuwan shi a gaba? kuma sun sani bayi shan coffee saboda babu caffeine a jikin shi ma ƴar tsama ne tsakanin shi da barci, dalili kenan da ya saka ya dawo da shan tea ɗin shi sama duk da nashi ɗakin a ƙasa yake amma hakan ma bai tsira ba. Domin da farko a main kitchen ɗin yake bari sai su shanye ba kuma zasu faɗa mishi ba sai dai yazo ya gani da idanun shi, duk faɗan da zai yi kuma ba zasu fito da waye ne last ɗin sha ba sun gwammace ya haɗa su duka yayi faɗan.
Ɗaukan mug ɗin yayi a haka ya nufi ƙasan, kai tsaye ya wuce kitchen ɗin da ya fara jiyo hayaniya daga cikinta tun daga nesa.
Me zai gani da shigan sa? Irfan ne riƙe da wuyan hijabin Reina itama ta cukumo wuyan rigan shi tana ta faman muzurai da hura hanci.
"Ba zaki sake ni ba ko?!" Irfan ya gargaɗeta yana kwaɗa baki.
"Sai ka tsuguna ka kwashe abinda ka zubar tass ko in yi maka shegen duka a wurin nan, hmm baka san wacece Reina ba ko? Sunana kawai kake ji amma ka tambayi Maama da Safina ka ji duk ƙaryan rashin kunyar ka tsaff zan gyara maka zama"
"Sake ta nace" Sabir ya make shi a bayan kai, sannan ya tura shi gefe.
"Amma yaya kana gani ita ta fara duka na" ya gwada Reina dake gyara wuyan hijabin ta idanun shi na tara ƙwalla.
"Ita sa'an ka ne toh da zaka rama? Kuma ba tana aikin ta kazo mata shishshigi ba? Ina ruwan ka da abinda take yi har zaka yi almubazzaranci da abinci?"
Aicha da aka fara rikicin a dalilinta tana tsaye ta maida su TV da cup ɗin tea wanda shine na ƙarshe da ta gani a ma'ajiyar Yaseer ta ɗauko, tana sipping tana kallon su hankali kwance.
Suhail da ya kamata ace shine ya shiga tsakani kasancewar shi babba a cikin su hidiman gaban shi kawai yake.
"Kun gama?" Suka ji muryar shi ta bayan su.
Dukkan su suka juyo suka dube shi.
Irfan wanda kuka ya kufce mishi ya buɗe baki zai fara maga Reina ta ɗaga muryar ta fiye da nashi a tsorace ta fara ƙoƙarin wanke kanta. "Yauwa yaya Yaseer ka gani cucumber da na wanke na gama slicing ya saka hannu yayi firo da shi ya zubar a ƙasa"
"Zagin darling tayi wallahi, da nayi magana kuma ta fasa min baki" ya gwada gefen bakin shi da ya fitar da jini.
"Ni kuma? Dan Allah kada ku saka ni a cikin case ɗin ku ban daɗe da shigowa ba ma" Aicha ta ɗaga hannu daga inda take. A'a
Bai tsaya sauraren ɗaya daga cikin su ba, Juyawa yayi kawai ya fita daga kitchen ɗin yana faɗin "Idan kun gama kuzo ina jiran ku"
Da sauri Reina tabi bayan nashi don Yau kam ta sani babu abinda zai hana ta komawa gidan Umman Zahra.
A main parlour ya zauna ya fara shan ruwan zafin haka ko zai samu ɓacin ran shi ya sassauta.
"Yaya Yaseer..."
"Zauna" yace idanun shi a cikin kofin hannun shi.
Niman wuri tayi a kujera zata zauna muryar shi ya dakatar da ita
"ƙasa"
Sai ta fara mayar mishi da abinda ya faru tun kafin ta gama kaiwa ƙasan, bai ce mata uffan ba sai da Irfan ya ƙaraso sauran ƴan uwan shi suka rufa masa baya tare da Aicha.
"Kun zo ayi hukuncin da ku ko?" Ya tambaya yana duban su.
Ɗaga hannu Sabir yayi "Haram shaida nazo bayarwa tunda a ido na komai ya faru"
"Ke kuma fa!" Ya dubi Aicha.
"Umm.. daman naga tea bags ɗinka ɗaya ne ya rage shine na ɗauka nace zan faɗa maka"
"Toh zaki iya tafiya"
"Amma yayan mu kayi haƙuri ba zai sake ba"
"Ba kin ce kada a saka ki a ciki ba? sai kiyi tafiyar ki"
Cikin sanyin jiki ta koma kitchen ɗin tana saka ma ranta banbanci yaseer yake son gwada mata tunda gashi ai bai sallami su Suhail ba.
"Kai kuma yi min kneel down a nan" Irfan ya zuba a kan guiwowin sa yana kuka.
Yaseer ya bada Sabir dama ya mayar da yanda aka yi tun daga farko har ƙarshe, sannan ya juya kan irfan a fusace.
"Baka da hankali ne ko tayi kama da sa'ar ka?"
Zai kare kan shi Yaseer ya daka mishi tsawan da ita kanta saida ta firgita ta ƙara maƙalewa a jikin kujera.
"C'mon bata haƙuri!!"
Sai da ta amsa ta haƙura kafin Yaseer ya ce yaje yayi kneel down sannan ya juya kan Suhail da faɗa, don bai ga amfanin kasancewar shi babba a tsakainin su ba, sannan ya sallame shi
"Hafsatu sai nace kada kiyi abu kike jin daɗin yi ko?"
"A'a wallahi. Ka yi haƙuri"
"Toh nikam na gaji, cikin sati ɗaya duk kin hana ni sukuni, idan na sake ji ko na gani tabbas zan san yanda zan yi da ke".
"Daga yau ba zaka sake ji ba yaya Yaseer wallahi nayi alƙawari"
Saida ya bari suka ci abinci suka ƙoshi sannan ya ɗauki Reina da Irfan zuwa laundry room ya saka su wanke duka kayan dake wurin.
"Har bedsheets, inga komai tatas" ya jawo musu ƙofa yayi tafiyan shi.
A kan injin wanki ma sai da suka kusan sake rikici amma sai gashi da jikin su ya fara tsami sun haɗe kai yanda zasu yi su gama wankin su huta gashi har da zanin gado da duvets masu yawa.
Ganin idan suka bi na dryer zasu wuni a nan Irfan ya je ya ɗauko musu igiya a store, Yaseer dake zaune a farfajiyar gidan sai gani kawai yayi ana ɗaura igiya a sama ya tsaya kallon ta mecece sai ga Irfan da Reina sun kamo ƙaton bahon kaya sun fito da shi.
Su biyu suke kama masu nauyin su shanya har aka zo kan ƙanana. Ta saka ma ranta Yaseer tashi zai yi idan suka ƙaraso wurin shi amma har tayi mishi magana yayi kaman bai jita ba, ala dole ta san ran shi a ɓace yake da ita.
Saida ta bari tazo dai-dai yanda yake zaune sannan ta shiga buge rigan pillow ruwan jiki ya fesu mishi tun daga saman kan shi har zuwa takardun da yake dubawa.
Ya ɗago yana kallon ta cike da al'ajabi sai ta ɗan saki murmushi "oh sorry ashe kana nan, to ɗan matsa"
Kallonta kawai ya tsaya yi itama tana tsaye tana jiran ya matsa ɗin aka buɗe gate mota ta shigo.
Reina ta juya ta dubi na cikin motar "laa daddyn Niger ne" tace tana ajiye rigan pillown ta wuce Yaseer dake daskare a wurin ta ƙarasa wurin Alaji Abdou da ɗan hanzarin ta cike da farin ciki, sai dai lokacin da motar tayi parking wanda ke ɗaya bangaren ya fito idanunta suka ware a kan shi saboda mamaki.
"Uncle Bilal?" Ta kira mamaki bayyane a muryarta, rabon ta da saka shi a idanun ta kusan shekara ɗaya da rabi.
"Na'am doll. Gani na dawo"
~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
75
~~~~~~~~~~
_Afin de te voire_
_(So that I could see you)_
_même dans un sommeil eternal_
_(even during an eternal Slumber)_
~~~~~~~~~~
*Uncle B*
"Na'am doll, gani na dawo" yace yana jinjina ma kan shi ƙoƙarin danne kewar ta da yayi don sai yanzu da ya saka ta a idanu yaji control yana niman ƙwace mishi.
"Uncle Bilal?" Ta sake kira da mamakin da yafi na da sai kuma ta kare bakin ta tana murmushi idanun ta na tara ƙwallar farin ciki.
Ji yake yi kaman ya ƙarasa ya rungume ta a jikin shi, Sai yanzu yake ganin ainihin wautar shi da bai shiga ya fita an ɗaura musu aure ba kafin ya tafi, da yanzu duk abinda za'a yi dai matar shi ce.
Takowa yayi inda take, yana shirin ɗaura hannun shi a kan kuncin ta da yaga yayi mishi wani luwai kaman mai wanka da madara sai ji yayi an make hannun.
Ya ɗube ta da mamaki amma wannan karon a maimakon ƴar shilan shi dake tsaye wani ƙato ya gani ya kare ganin shi.
Suka bi juna da kallo tun daga sama har ƙasa na sakwannin da bai wuce biyu ba, sai uncle B ya mayar da murmushin ɗazu saman fuskar shi ya miƙa ma Yaseer hannu "Yaseer ko?" Ya tambaya da muryar rashin damuwa.
Yaseer ya sauƙe ajiyan zuciya ganin ya fi uncle B tsayi ko ba komai, sannan ya kalli hannun da yake shirin taɓa Reina da shi ɗazu shine yake miƙo mishi. Ko a baya ma haka yake tattaɓa ta? Shiyasa yace ɓata mata rayuwa zai yi kuma bai yi ƙarya ba tunda gashi abun nasa har gida.
Muryar Alaji Abdou shi ya katse Yaseer da miƙa hannun shi ba don kuma yana da niyyar miƙawan ba.
"Sarauniyar Daddy idanun ki ya makance da ganin uncle ni ba'a gan ni ba ko?"
Ɗan durƙusawa tayi a kunyace hala ma har uncle B ya faɗa musu soyayya suke yi, tace "a'a Daddy ina kwana"
"Lafiya lau yaya jikin daddyn ki da sabon wuri"
Da haka suka fara wucewa ciki uncle B yabi bayan su Yaseer ma bai ga ta tsayuwa ba.
Da gudu Aicha take sauƙowa daga matakalar benen ta ƙaraso ta rungume mahaifin ta. "Daddy sannu da zuwa" tace tana kallon fuskar shi.
"Shika ni" yace ba tare da ya mayar mata da rungumar ba. "Muna ƙasa ɗaya gari ɗaya amma da ban zo ba barin saka ki a idanu na ba ko?" Ya zungure mata goshi.
"Ayyah Daddy mun yi busy ne a office gabaki ɗaya babu lokaci"
"Ko shi uban gidan naki ya je ya gaida mu har sau biyu. Ni dai na sallamar da ke ma Umma tunda baki so na ai ina da wasu yaran"
Ta riƙo hannun shi tana yaƙe don bata da ta cewa ta zaunar da shi. "Bari in kawo maka ruwa"