Sashe 9
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Malam baƙo" bai ɗago ba don ya san ba dashi ake ba. "Kai ɗan ƙasar waje." Sai da kalmar kai ɗin ya bar bakinta taji kaman ta bishi ta jawo shi ya dawo, idan tace ɗan ƙasar waje ma kawai ai zai gane.
"Come again?" Yace yana tsareta da idanuwa.
"Dan Allah kayi haƙuri" ba ƙaramin tsami hannunta sukayi ba amma tana tsoron sauƙe su.
"Nayi" ya faɗa a babin 'kai' da tace mishi, a nata tunanin laifin kwanciya a ɗakin da aka gyara mishi ya haƙura. Sai ta sake matsar wasu ƙwallan don ya daɗa jin tausayinta tace "toh in tafi?"
"Daman ni na tsayar da ke?" Bai ga dalilin da zai ɗauki alhakin hukuncin laifin da ba ma shi aka yi ba, bayi da wannan lokacin.
Sauƙe hannunta ta fara yi don ta gani ko da ba'a yayi maganar tunda Hajiya Hauwa ta saka yanzu dole ta fara ganewa. Ganin bai ko kulata ba ta zauna da kyau, hankalin shi ma bayi kanta yanzu.
"Umm... Ɗan kasar waje"
Bai san dalilin da yasa ya ɗago ya kalleta ba duk da ya ƙware a yiwa mutane banza sai dai ko bakuwa ce a gidan ba zata rasa jin an anbaci sunan shi a gidan yau ɗin ba, tunda har ta san daga ƙasar waje yazo.
"Nace dan Allah idan kaci abincinka zaka rage mun?" Tana tsorace amma ba karamin kalolin kayan daɗi aka haɗa mishi ba. "Yunwa nake ji sosai Allah"
Har tudun cikin ta da take shafawa a yanzu ya ɗan koma Amma Uncle B yaga girman shi ainun.
"Yaya sunan ki?"
"Reina"
"Sunana Bilal ba ɗan kasar waje ba. Uncle Bilal"
Sai ta jinjina kai alamun ta fahimta. "Toh Uncle Bilal zaka rage min abincin?"
"Kije kiyi Sallah sai kizo muci"
Lallai wannan Uncle bilal ɗin ɗan aljannah ne.
A take ta miƙe jinin da ƙafafuwan ta suka tara ya saka tayo gaba kaman zata sake zuba masa a kan kafafu yayi saurin matsawa yana hararar ta, ta miƙe da kyau tana washe baki tayi saurin barin wurin.
Ko minti goma cikakke bata yi ba ta dawo har tayi Sallah.
"Toh muje Uncle Bilal" Yanda ta ranƙwafo kaman zata ɗauke shi don taga yana mata saiɓi, kada ma tayi gaban kanta ne Hajiya Hauwa ta ritsa ta amma da sai dai yazo daga baya.
Sai da ya kusa gama ƙure haƙurin ta kafin ya miƙe suka nufi dining ɗin taja masa kujera ya zauna. Ta ɗauki plate ɗin gaban shi ta zuba masa abinda ta fara cin karo dashi a cikin kulolin ta ɗauki bowl ta zuba mishi farfesun naman rago kana itama ta shaƙe nata plate ɗin ta diran masa.
Yayi kewar abincin gida kuma yana jin yunwa amma bayi jin ya kai Reina dake dagargazan cinyar kaza da hannunta biyu. Har yanko naman take yi tana dandala masa pepper sauce ɗin jiki kafin ta cusa a cikin bakin ta da ƙaton murmushi.
Da farkon fara cin abincin su Hajiya Hauwa tazo ta tsaya tana kallon su cikin kaɗuwa, Reina da ta saka a hukuntata shine ake mata hukuncin da kayan daɗi!.
Tazo cin ubanta Uncle B ya hana, tunda da izinin shi take zaune a wurin. Babu yanda ta iya haka ta ƙaro musu pepper chicken ɗin dake tururi da ƙamshin daɗi shine Reina ta diran mishi.
Ta rungumo kwanon romon ragon nan baki ɗayanta ta kawo baki tana kurɓa ɗumi da daɗi na ratsa har kwanyar ta. Ita bata san ma yaushe ta fara jin daɗin abincin da ba kayan fulawa ba har haka, ko dan su naman ma an dade ba'a haɗu bane?.
"Reina, use a spoon" cewar Uncle B.
Aikuwa bai rufe baki ba ta ƙware.
~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
47
~~~~~~~~~~
_I try to live in black and white but I'm so Blue_
_But I'm not what you need_
~~~~~~~~~~
Kofin ruwan gaban shi ya miƙa mata ta karɓa tana tari ta kafa kai, ta sha da yawa kafin ta samu numfashin ta ya daidaita. Ya zari tissue ya miƙa mata ta goge bakinta da hannunta , taji zafin yajin da ya haura mata kai don haka ta ɗauki cokali kaman yanda yace, ta cigaba da ci a nitse, ta fara ƙoshi yanzu kam ma.
"Uncle Bilal" ta kira cikin ƙasa da murya kada Hajiya Hauwa da ta dawo falo ta jita.
Bai amsa ba bai kalleta ba amma tasan yana jinta.
"Zaka tafi dani gidan ku dan Allah? Ko ƙasar wajen ma zan bika"
Ɗago ido yayi ya mata wani irin kallo. "Saboda ku baku da gida?"
Gyaɗa mishi kai tayi "eh bamu dashi yanzu, wai an siyar"
"An siyar?"
"Eh, ana bin Daddy na bashi ne shine ya siyar"
Tamke fuska ya ƙara yi "A ina kika ji wannan maganan?"
Sai tasha jinin jikinta ta koma wasa da cokalin ta a kan plate kana ta amsa da "Mutane da yawa ne suke faɗa harda su Abban Zahra ma da Umman ta".
Kallon Hajiya Hauwa yayi a kaikaice, itama su take kallo ta kasa kunne ko zata ji abinda suke tattaunawa a kai sai dai tsakanin su akwai rata sosai.
Sai yanzu ya gane wacece Reina, yarinyar Alhaji Tahir mamallakin TK Kingdom wanda ya kasance ƙanin mijin ƴar uwar tashi kuma ya samu karayar arziƙi a shekarun baya.
"Naji, muci abinci" gabaki ɗaya tausayin ta sai ya kama shi, ance mahaifiyarta ta rasu ga yanzu ma mahaifinta babu.
Amma wannan maganan ba na tsakaninsu bane, shi da Hajiya Hauwa zasu yi shi, yaji yanda za'ayi a inganta rayuwar yarinyar tunda yasan yaya maraici yake, mahaifiyar shi a haihuwar shi ta rasu, bayan ta haifeshi shi kaɗai namiji cikin ƴammata 9 a cikin gidan su, mahaifiyar su Maryam maman Meesha ita ta raine shi. Yayi nashi maraicin cikin daula da tsananin gata amma sam bashi da daɗi.
Da ya tashi tafiya haka ya ciro kuɗi masu yawa in dollars ya bata don bai samu daman yin canji ba tukunna. Su Hajiya Hauwa ma yayi musu alkhairi sosai ita da yaranta amma zama kam yaƙi zama, suka ɗunguma dukkansu suka mishi rakiya mota suna kallo driver yaja suka bar gidan.
Bata iya bari ma sun koma ciki ba Hajiya Hauwa ta saka hannu ta ƙwace kuɗin Reina duka. Kuka ta saka tana binta wallahi sai ta bata har da riƙo mata riga, bata samu zaman lafiya ba saida ta ɗauke ta da wani marin ta rabu da ita.
Idan ba ɓata yaro ba ma mai me shekarun Reina zata yi da kuɗi? Ta daɗe da mantar da kanta cewa Reina ta girmi Zaheera, ita ta tsira da nata dukda babu abinda ta nima ta rasa.
Ɗaki ta koma ta risgi kuka son ranta har ta ƙare ta bawa kanta haƙuri, amma tunda cikin ta a ƙoshe yake, ga naman da ta naɗe a foil paper ta ɓoye a aljihun bayan jeans ɗinta lokacin da Uncle B yake shirin tafiya to yau Hajiya Hauwa sai dai suci aikinsu su kaɗai.
Ta cire naman ta ajiye kana ta gyara kwanciya a kan gadonta sai dai babu barci a idanunta sai juye-juye take yi. Can ta tuna da diary ɗin Auntynta ta miƙe ta ɗauko shi a cikin wardrobe, ta ciro key ɗin a jakar makarantarta ta buɗe. Tsallake wurin da ta karanta ranan tayi saboda kada ya sake tsinka mata zuciya ta ɗaura da abinda ya biyo baya.
'Nayi burika da yawa a rayuwa, amma ina daɗa girma ina ƙara sanin menene duniya. Daga farko gani nake yi kaman duniyar baki ɗayanta domin ni aka yi, amma daga baya sai nake fahimtar akwai da yawa a cikinta wanda suka fini daraja. Na ɗauka babu wanda suka fimu jin daɗin rayuwa saboda muna zagaye da mutane masu ƙaramin ƙarfi, ashe muma masu ƙaramin ƙarfin ne a gaban wasu domin duniya ba zallan unguwar mu ta ƙunsa ba, unguwar tana zagaye da Bauchi, Bauchi tana zagaye da Nigeria, Nigeria tana zagaye da africa kuma duk yawan ƙasashe da mutanen dake cikin africa bamu yi ko kwatan duniya ba ashe.
Daga wannan matakin ne burika na suka fara zama mafarkayya, idan na tuna cewa sauran mutanen duniya ma rayuwa suke yi da fafutuka kamar ni sai inji guiwa na ya ƙara yin sanyi. Ni Fauziyya, ɗaya ce daga ɗumbin mutanen duniya, I'm not as special as I thought I am.'
"You're special Aunty, bani da kowa a duniya kamar ki, you're special to me, Maama and Daddy. You're special to Ummi too"
Ta shafa shafin kaman zata ji lokacin da take rubutun kana ta buɗe shafin gaban shi taci gaba da karantarwa.
'wani lokaci nakan yi tunanin da ace ni kaɗai su Ummi suka haifa da rayuwar mu zai zama daban? Da zan zama ƴar gata nima kaman yaran da nake gani a makaranta iyayen su suna ajiye su a mota? Ban damu sai nayi cuɗanya da mutane sosai ba, ciwon kai suke saka min amma nakan yi kwaɗayin rayuwan yaran masu kuɗi nima ina shiga motoci kaman su ina rayuwa a gida mai bene. Zan yi karatu ne in zama likita in yi kuɗi in gina mana gida mai bene sai dai a karon farko da nayi jarabawar kammala secondary maki na be kai na karatun likita ba. Ina son in haƙura in sake rubutawa wani shekara amma ina tsoron na sake faɗuwa gashi sa'o'i na sun tsere ni, kuma ma ina cikin masu Sa'a domin wasu ma basu ci jarabawar ba baki ɗaya.
Haƙura nayi na karɓi course ɗin da na samu tunda ɗan adam bai san yanda arziƙin shi yake ba. Don haka na fara koyon gashe-gashe a wurin ƙanwar Ummi ina zuwa gidanta na musamman ina taya ta idan zatayi ma mutane na biki kafin in fara zuwa makaranta, cikin ƙanƙanin lokaci na iya kuwa.'
Shafin gaba ya bambanta sosai da labarin da take bayarwa. Reina ta tashi ta zauna da kyau ta matso da littafin kusa da fuskarta ta gani da kyau kaman sunanta ne a rubuce da manyan baƙi.
Kwanan wata ta fara rubutawa kana ta saki layi ta ɗaura da.