← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 117

Sashe 56

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai lokacin da ya gama nisa a wannan hanyar ne makaranta sun daɗe da koran shi saboda tarin carry over kafin su Hajiya Hauwa suka zo duba shi. Da gaske hankalin su ya tashi matuka a lokacin, amma tsoron tada zaune tsaye ya saka basu koma da shi Nigeria ba sai gargaɗin daina bashi kuɗi da suka yi, ko a jikin shi tunda abinda suke bashin a gaban abinda yake samu ba komai bane, ya ma yanke hanyar da zasu ke samun shi ya bi babban dealern su na Ghana zuwa Italy Saboda ubannin gidan su suna son ganin shi.

Sun yi mishi gwaji sosai irin wannan a kama shi ayi mishi dukan mutuwa ko zai faɗi sunan su Amma ya ƙi, don haka suka saka shi cikin amintattu suka jiƙa shi da kuɗi ya ƙara dawowa wani gagarumin ɗan Iska.

Amma bai san cewa Yaseer na biye da sawun shi ba, kuma ɗan zuwa gida da iyayen shi zasu saka yayi da alƙawarin za'a aura mishi Reina itama ya samu ya fasa da ita duniya bayan ya gama kashe ƙishir ruwan shi a kanta ya caski kuɗi da ita. Ashe ƙarshen shi ne yazo.
.....

Murmushi Alaji Abdou yayi bayan ya gama duba takardan sammacin ya naɗe ta ya ajiye ya dubi Alhaji Tahir da Kamal. "Lokaci yayi da zamu sake ɗana tarkon mu na biyu, ni banma yi tunanin zasu kai wannan lokacin basu waiwayi kuɗin nan ba sanin cewa kana raye baka mutu ba"

Alhaji Tahir ya jinjina kai "Fargaba na ɗaya kada wani abu ya taɓa rayuwa ko lafiyan yara na, suna da ƙananun shekaru gasu mata, bani son a sake yin abinda zai taɓa ƙimar wani ko nasu Shiyasa nace ma yaron nan Bilal ya dakata idan an gama komai ya ga yana kan bakan shi shikkenan. Amma suka yi aure a halin yanzu duk abinda ya shafi Hafsatu shima ya shafe shi"

"Haka ne kam." Abbah ya amshe "Amma shekaru bakwai muna shiri in sha Allah komai zai tafi daidai. Shi karan kan shi Alhaji Salisu ai bai san mun san abinda yayi ba, lokaci ne yazo da Allah zai bi mana kadin Abinda suka yi mana da yaran mu. "
.....
*Reina*

Sai can jimawa ta ɗago daga kwanciyar da tayi a kan desk ta ajiye wayar da ta shiga game ɗin dole domin bayanin Yaseer yana shiga kanta sosai.

Ta gyara zama ta bashi hankalin ta tana sauraron Abinda yake fada su Safina suna jotting main points sai ta bari kawai ta saurara idan sun fita ta karɓa ta kwafa.

Sai a lokacin idanunta suka shiga cikin na Aicha dake zaune a high table kujerar ta a gefen na Yaseer.
Aicha ta daɗe idanun ta a kan Reina amma sai yanzu ta samu suka yi ido huɗu don haka ta sake mata kasalallen murmushin daɗin kiranta da 'Ƙanwata' da Yaseer yayi, ga Uncle B ya turo iyayen shi ita kam alhamdulillah Reina ta kusa fita daga idanunta, so ma take yi su fara mutunci yanzu, don haka ta ɗaga mata hannu Saboda idan ƙanwar Yaseer ne Ya kamata mutane su san sun san juna suna mutunci saboda kallon da suke mata a matsayin masoyiyar shi.

"Mayya" Reina tayi mumbling tana jan guntun tsaki.

Safina ta juyo ta dube ta, "ke kuma da waye yanzu?"

"Wallahi na tsani mutum mai fuska biyu, da har ta fara burge ni amma haushi take bani yanzu"

Taɓe baki Safina tayi don ta gane zancen wa ake. "Ko dai kishi kike yi da ita ba? amma me ya kawo zancen maita?. Kuma ga mai fuska biyu nan uncle ɗin su Zaheera! Daga yanayin yanda yake hidimomin shi ya kamata ki gane. Ki buɗe idanunki ki farga kafin ayi miki mulkin mallaka"

Shiru Reina tayi bata tanka ba ganin surutun su ya saka mutane sun fara waiwayen su alamun suna cika musu kunne. Amma ta shiga nazarin kalaman Safina. "Waye zai mata mulkin mallaka? Aicha ko Uncle B? Tunda su ta ambata a cikin zancen ta Amma idan suka fita zasu ƙarasa.

Ƙarfe 1 aka tashi, ba'a bar su sun tafi ba aka shigo da abinci mai rai da lafiya aka basu sannan aka yi rabon souveniers ɗin da Reina tayi kowa ya fita daga wurin da nauyin shi.

Masallaci suka wuce suka yi zaman cin abincin "Wannan ai ko kuɗin da muka bayar bai isa ya ciyar da mu haka ba, ga kayan laidan kun ma yayi kyau, Allah dai ya ƙara ma yaya Yaseer ɗin mu arziki mai albarka" safina ta saka cokali ma fried rice ɗin da shima ya ji kaji ga coleslaw.

Reina ta kalli abincin itama, Kaman ummi ta sani suka yi stick meat da samosa a maimakon pepper chicken da meatpie da za'a sauya su da shi gobe.

"Hmm ni dai daga nan mu wuce gidan ku cos ba zan iya komawa class ɗinnan ba ƴan jarida su tsare ni da tambayoyi kuma ba zan iya komawa gida ba don kunyan Daddy nake ji sosai wallahi."

"Duk ke kaɗai" Safina ta taɓe baki ta fara cin abincin ta. Takeway ɗaya suka ci tare ya ishe su suka yi kyautan ɗayan sannan suka wuce gidan su Safina, sai a lokacin ta samu faragar kiran Uncle B.

"Uncle Bilal ina wuni"

"Lafiya Hajiya Hafsah"

A shagwaɓance tace "yau ba doll ɗin kuma?"

"Yanzu kam kin wuce wannan matsayin dan na lura kin ƙaro capacity"

Yamutsa fuska tayi "Uncle Bilal mana!" Bata san shi da mita ba Amma Yanzu yana son ya bi mishi jiki.

"Serious question Hafsah kin daina so na yanzu ko? Tunda kina da gata baki buƙata na"

"Ina son ka mana Uncle Bilal, me zai kawo wannan tunanin cikin ran ka?"

"Hmm" yace yayi shiru.

Kaman ta kashe wayan ta bar shi ya huce don kan shi amma ta kasa tana tsoron wani balbalin da zai biyo baya.

"Ina Mufid? Yanzu ka daina kawo min shi" ta sauya akalar taɗin ko za su yi Sallama a mutunce.

"Yana KD, ban kawo shi bane kuma saboda baki buƙatar kyautar shi da nayi miki alkawari, da kina yi da jiya kin yarda kin zama halali na doll" shi ya fara sauƙowa daga yanayin muryar shi da ta ji Amma ita tsugul ya saka ta miƙewa ta zauna cikin kaɗuwa.

"What are you talking about uncle Bilal??"

"Na faɗa miki duk Abinda za'a yi ke tawa ce doll, duk abinda za'a ce duk abinda za'a yi ke tawa ce. Nayi sadaukarwa masu yawa a kan ki don haka ba zan iya haƙura da ke ba gaskiya. Idan ma kin fara sauya tunani kiyi ki dawo hayyacin ki, na soki tun baki da komai don kin samu ba zaki guje ni ba".

~~~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

82

Shiru tayi mishi bayan ya gama, ita ya kamata ace ta gwada ɓacin ranta ba shi ba, saboda wani irin abu ne haka kaman a garin gaɓa-gaɓa.

"Hafsah, banza kika yi min?"

"Amma ba haka muka yi da kai ba Uncle Bilal" tace murya na rawa ƙwalla na taruwa a idanunta, shiyasa ashe babu wanda ya tunkare ta da maganan saboda rashin hankalin ta suke gani, ita da wani ido zata kalli Daddy, ko wata biyu basu kai da sake ganawa ba Amma har zata cigaba da ɗaga mishi hankali.

"Tunda auren nan zamu yi Hafsah menene banbancin yanzu da gaba uhmm?"

"Nima abinda nake gani kenan idan mun bi komai a hankali, Daddy na bayi da Lafiya Uncle Bilal Ina tsoron in sake saka shi a wani hali dan Allah ka fahimce ni" tace kuka na ƙwace mata lokacin da Safina ta turo ƙofar ɗakin zata shigo idanun ta a kan Reina dake faman sheshsheƙa da waya a kunnen ta, gudun ɓacin rai ta mayar da ƙofan ta rufe tana jan tsaki.

"Toh menene na kuka kuma yanzu. Shikkenan zan jira Allah ya kaimu lokacin Amma sai kin yi min alƙawarin babu komai tsakanin ki da Yaseer" ya ƙare ya fitar mata da ainihin Abinda ke cikin zuciyarsa.

Kukan ne ta ji ya tsaya mata lokaci guda "Yaya Yaseer kuma?"

"Eh shi"

Cikin tashin hankali tace "Ka san komai dake tsakani na da yaya Yaseer, ka san mummunan ƙaddarar da ta ratsa tsakanin mu"

"I hope it stays that way doll, I really do. kada ki zo ki canza magana daga baya"

Haka dai suka ƙarasa wayan cikin wani yanayi da Reina ta fara gajiya da shi, Uncle B yayi ƙoƙarin sako wani hiran ita kuma hankalin ta ya karkata kan dalilin da zai saka shi tunanin Yaseer shi zai kawo Matsala a tsakanin su.
.....
Tuesday
12:44pm.

Zaune take a row na biyu ta saka tagumi ta Zuba ma Yaseer dake bayani idanu, yana cikin coffee brown suit da ya amshi kalar fatan shi haibar shi ya daɗa fitowa fiye da na jiya.

".... So Finally ba wai na zo in cika ku da surutu bane, Na san duk kun gaji.."

Ihu suka saka suna girgiza hannu "dan Allah a ƙara mana ya kai sati biyu Sir" muryar wasu ya fito bayan hayaniyar ya lafa.

Yaseer ya ɗan waro ido yana dariya idanun Reina a kan Adam's apple ɗin shi dake motsawa. Ta haɗiyi miyau tare da gyara zama tana ƙoƙarin mayar da duban ta kan fuskar shi zalla don a wurin ya kamata ace amsar yake.

Duban ta yayi na sakwanni biyu, idanun su ya shiga cikin na juna ba tare da fara'ar ya bar kan fuskar shi ba sannan ya ɗauke kai.
Chapter 56 · 0% Book details