← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 117

Sashe 74

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Takawar ki lafiya amaryar Alhaji Yaseer yaron alkhairi ɗan mutan Jama'are. Yarinya kin zaɓo tsalele irin uban ki" Wata mata cikin goggoni tazo ta rungume ta da warin hayaƙin da take yi.

Aunty Zeenat ne ta samu ta gudo da ita bayan sun yayyame ta suna mata wasu maganganu marasa kan gado daga zuwan ta.
Saidai ko ba komai ta samu tunanin abinda ya faru ya bar kanta na ɗan wani lokaci.

A can ajin da suka rubuta jarabawa kuma Safina tana ƴan baya-bayan fitowa don haka itama wasu suka tsareta da zancen tunda basu ga Reina ba, cikin Sa'a kuwa tana dai-dai da su don saida aka raba ta da wata yarinya da ta faffalawa mari ba notice kafin ma ta kaiga ƙarshen maganganun da Safina take jin basu gamshe ta ba.

Rikici ya kaure tsakanin mutanen da suka samu aka yi accepting proposal da suka tura bayan program ɗin nan sune suke bin bayan Yaseer sai Safina, da kuma ƴan baƙin ciki da hassada wanda basu samu shiga ba sun fi kowa sautin murya.

Ƙarshe sai da lecturers da suka yi invigilating exams ɗin su ne suka zo da security aka kora su. Safinah sai ganin jakarta tayi a gaban aji bata san wa ya ajiye ba. Da ta duba wayanta ta same shi tayi ƙwafa don da yau da sun sace mata waya da bala'in da za'a yi bata san kalar shi ba.
.....

Saida suka gama karatun su na ƙarshen sati kafin a rufe da addu'a Abbah yace "in Allah ya yarda gobe zamu je kai tambaya da sadakin ƴar uwar ku Hafsatu gidan su mahaifiyar ta..."

Babu wanda ya kawo komai a cikin su saboda tunanin su ya basu wanda Uncle B ya kawo ne zasu ɗauka su kai musu a raba ma ƴan uwa.

"...Muna fatan a saka lokaci nan kusa in sha Allah za'a ɗaura auren ta da Yaseer bisa amincewar dukan su biyu"

"Wani Yaseer?!" Suhail ya riga Aicha tambayar da yayi tsalle tun daga cikin ta sai kawai ta zuba ma Abbah idanu tana jiran ta ji akasin abinda shaiɗan ya raya mata na second guda kafin tayi yaƙi da shi.

Shi kuma Abbah wani irin kallo yabi Suhail da shi yana ƙara tamke fuska yanda yaji Suhail ɗin ya ɗaga masa murya sannan ya amsa da.

"Yaseer babban ɗa na. Yayan ku. Shi zai auri Hafsatu yarinyar Alhaji Tahir kwanan nan in sha Allah"

"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un!!!" Umma ta saki salati tana yin kan Aicha da ta zube a wurin sumammiya.

.....

Komai ya tafi yanda ake so, an haɗu an gaisa cikin girma da arziƙi sannan aka gabatar da munafar da ya tara su gaba ɗaya.
Alaji Abdou shi ya karɓi sadakin Reina aka tsayar da biki nan da sati huɗu bisa kafiyar dangin amarya saboda wai su samu suyi shirye-shirye a tsanake. Ba don su Abbah da suka zo da sati biyu a bakin su sun so ba amma haka suka amince tunda sune masu nema. Aka yi zumunci aka yi raha taro ta watse lafiya kaman yanda aka fara ta sannan ko wani ɓangare sun tafi da tsaraba mai yawa.

Sai fatan Allah yasa ayi lafiya.

.....
*Yaseer*

Minti talatin ba'a yi da sanar da shi yanda aka yi ba, shi da yake can wata uwa duniya sai ga katin 'save the date' mai ɗauke da sunan shi da na amaryar shi da ranar da zata zama mallakin shi ya ɗaura a status ɗin shi.

Kaman ya rufe wayan shi bayan haka tunda ya san mutane idan suka soma kiran shi don niman tabbaci sai yaji babu daɗi amma yana so ya kasance mutumin da zai tabbatar musu zai auri Hafsah da bakin shi, don haka ya ɗauki kira na farko da ya fara shigowa wayan shi yana shafa kan shi da ƙayataccen murmushi a kan fuskar sa.

......
Aicha da suka yi kwanan Asibiti tun jiya ta tsurawa status ɗin idanu hannun ta mai sanye da drip yana karkarwa.
Su Ummah ne suka kawo ta asibitin kuma su ke zaune da ita don ko iyayen ta basu sanarwa ba, Sannan kasancewar ta cikin halin ha'u'la'i bai saka sun fasa nima ma ɗan su aure ba ko ma su jinkirta tunda halin da zata shiga ba damuwar su bane.

Wata Nurse ce ta shigo da allurar ta zata yi mata, tayi mata yaya jiki sannan ta shiga haɗa allurar tana tambayar ta ina mai jinyarta ta tafi?.

Bata amsa ta ba Saboda abinda take faɗa bayi shiga kunnen ta har sai da ta ƙaraso jikin ta da allurar zata yi mata a jikin cannula sannan ta dube ta.

"Dan Allah sister babu wani poison da zaki iya haɗa min wanda zan mutu cikin ƙanƙanin lokaci?"

Nurse ɗin ta waro ido cikin firgici tana ayyana wannan ai patient ɗin psychiatric ward ne a cikin ranta.

Tace "kada ki damu zan biya ki, zan tura miki duka abinda ke cikin account ɗina tunda bayi da amfani, ki bani account details ɗin ki in saka miki yanzu ma, kuma babu wanda zai sani tunda na riga da na mutu kinga kuma taimako na kika yi."

Ta riƙo hannun Nurse gamm wanda ta saki ihu cikin firgici tana ƙwala kiran "Doctor! Doctor! Wayyoo Jama'a azo a taimake ni don Allah!"

Aicha ma ƙara ƙarfin riƙon ta tayi tana kukan ta taimaka mata kada ta barta taci gaba da rayuwa don Allah.

.....

."ki saki jiki ki zaɓi kaya uban ki ne zai biya, idan ma tausayin aljihun shi kike ji yace na faɗa miki kada kiji komai akwai su da yawa ya tara domin ku"

Cewar Mariama tana daɗa matsawa jikin Reina ta tura mata magazine ɗin da take gwada mata hotunan furnitures da za'a yi shipping wanda ta zaɓa a kawo shiyasa take so ayi da wuri don kada a samu delay ɗin shigowa da su.

Ita kuma tunda Alaji Abdou ya kira Mariaman ya sanar da ita ranar da aka yanke sai matsanancin kunya ya kamata. Wai itace aka tsayar wa ranar Aure? Gabaki ɗaya wani iri take ji.

"Mummy ki zaɓa min kawai, duk wanda kika ɗauka yayi"

Mariama ta haɗe rai "ai Saboda ba zan zaɓa ɗin bane nace kizo. Ashe haka kike shiyasa kika kusan jajiɓo ma kan ki bala'i ko? Ke mai ma ya kai ki haɗa alaƙa da wa'innan mutanen har kika jawo muka kusa sadaukar da ke?"

Maganganun ta suka saka Reina tayi mata kallon rashin fahimta.

Takaici ya saka Mariama ta dungure mata goshi "kin san wa nake nufi sarai bani son munafurci, da yanzu ya lallaɓa ya aure ki idan ma baki zama Allah sarki ba toh kina hanyan zama."

"Uncle Bilal kike nufi wai?"

"Zaki ce mun baki sani bane?"

"Ban san mene ba mummy?"

"Abinda ya raba shi da uwar ƴaƴan shi mana"

"Yace wai cewa tayi ta daina son shi ta kai shi kotu a raba auren"

"Shikkenan abinda yace miki?"

Ta gyaɗa kai.

"Amma wannan Allah yayi baƙin munafiki"

hankalin Reina ya tashi wanda ya gwada hakan a kan fuskarta, ta dubi Mariama cikin niman ƙarin bayani don bata san ta ina zata iya ɗauko wani mugun hali ta haɗa shi da Uncle B a cikin kanta ba.

"Toh saurare ni kiji da kyau ance soyayya suka yi na bugawa a jarida da suke makaranta, da suka gama makaranta suka buƙaci yin aure iyayen ta suka ƙi saboda kin san balarabe koda na africa ne da ƙin baƙin fata, haka dai suka samu suka yi auren ya koma da ita Canada saboda ya samu aiki da su a matsayin ƙaramin likita. Ita aikin jarida ta karanta kuma ta samu offer a wurare da yawa da tayi applying tunda takardun ta sun yi kyau sosai, sai ya hana ta zuwa interview ya karɓi takardun ta wai shi da kanshi zai sama mata a manyan gidajen talabijin na ƙasa da ƙasa. Watanni suka ja bata ji daga gare shi ba sai ga ciki, nan ya samu wurin maƙalewa wai ta haƙura ta haife shi tukunna zuwa lokacin koma menene yake jira ya fito, kuma wai sun yi alƙawarin ba zasu haihu da wuri ba sai ta samu ƙwarewa a kan aikinta ta samu matsayi amma me ya faɗa mata Allah masani sai gashi ta yarda ta haifi yaron da aka ce wai har gida yake zuwa miki da shi" ta ƙarashe tare da watsa ma Reina dake kallonta baki da hanci harara.

Amma ita dai bata ji wani abun tashin hankali a labarin ba, koma abinda zai saka a hana shi aurenta, idan wannan dalilin ne bai isa dalili a wurinta ba Wallahi.

"Saida ta haife yaron nan ya fara fito mata da ainihin halin shi. Ta buƙaci taje ganin gida suma su ga jariri ya hana wai sai ya ƙara gwaɓi, Shekara ɗaya biyu matar nan ko cikin garin da suke Bilal ya hana ta bari, ya ɗauke passport ɗinta ya ɓoye kuma labarin aiki shiru.
Still suna zaman su lafiya har sai da ta samu wani cikin bayan maganin planning da take sha ashe Bilal ya canza mata da na bogi. Toh a lokacin ne ta tada rikicin sai ta zubar da shi sai ya samu damar da zai ƙara buɗe mata waye shi. Ya fara kulle ta a cikin gidan wataran ma a cikin ɗaki har ya je ya wuni a wurin aiki ya dawo, Sannan ya ƙwace wayar ta da duk wani abu da zai sada ta da waje shi yake kai yaron kindergarten ya rufe ko ina na gidan da sun dawo ya sake rufewa daga ciki, ya zaga kuma yana faɗawa duk wanda ya tambaye shi ita kuma wai sun rabu. haka ta ɗauki wata taran rainon cikin nan ko bakin ƙofa bata taɓa takawa ba sai da tazo haihuwa yaga zata rasa ranta kafin ya kaita asibiti aka mata tiyata aka cire amma yaso da shi zai karɓi kayan shi a cikin gida.
Chapter 74 · 0% Book details