← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 117

Sashe 70

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na'am mai sunan"

"Da ace Aunty tana raye idan na auri Uncle Bilal zata yi farin ciki?"

Ummi halin Bilal na kirki kawai ta sani da ƙokarin da ya dinga yi a kan Reina da lafiyar ta. Bilal din da ta sani wanda Yaseer bai shiga masa hanci da ƙudundune bane ya fara fito da ainihin colorn shi launi daban-daban.

"Allah yayi miki zaɓin alkhairi. Ko ita Auntyn ma ai Allah ne ya zaɓa mata mahaifin ki har aka same ki, don haka kasancewar ta a nan ko rashinta ba zai canza komai daga ƙaddarar ki ba"

Kaman zata faɗa mata Yaseer yace yana sonta ta ga yanda zata hau kan zancenta ta zauna. Amma ta fasa don yanda ta ɗauke shi kullum yana kan harshen ta da samun addu'o'i kala-kala ya fi Bilal matsayi a wurinta tuntuni, ta sani zata yi uwa tayi maɗaukiya ne a lamarin sai inda ƙarfin ta ya ƙare don haka tayi shiru, zata je ta ƙara addu'a ne Allah yayi mata zaɓi da kansa kaman yanda Ummi tace.

Ta so kwana ne gobe ta koma amma da daddare sai ga Umma da Abbah sun zo gidan bayan ta kira kuma ta sanar da su zancen kwanan tan tun yammaci. suka buƙaci ganawa da Ummi, kuma sun daɗe suna zantawa ƙirjin Reina sai bugu yake yi don tana da tabbacin ko me ake tattaunawa a ciki a kanta ne, toh ko yaya Yaseer ya sanar ma iyayen shi yana sonta ne? Ita kam ta shiga uku.

Ganin bayan fitowar su Ummi bata gwada wani alama ba sannan da tayi mata sallama bata ce da ita komai ba ta ɗan kwantar da hankalin ta, kuma ta kashe wayan ta tun kafin su isa saboda kada Uncle B ko Yaseer ma su dame ta don so take yi ta raba dare tana salloli da roƙon zaɓin Allah.

.....

"Ina kwana yaya Yaseer"

Bai amsa ba ya maido mata tambayar "mai yake damun ki?"

Haka yake mata a duk lokacin da ta rufe wayan ta ya kasa samu Ko ya kira bata ɗauka ba. Ba zai yi fushi yana tambayar meyasa bata ɗauki wayan ba ko ma mai ya hana ta ɗauka. Sai dai ya tambaye ta 'kina lafiya?', 'mai ya same ki?' ko 'Allah yasa dai lafiya' ko kuma wani tambaya dake nuna kulawa ba tuhuma ba.

"Babu komai fah! Na kwanta da wuri ne" Ta amsa ba tare da ta ɗago ba.

Sai ya ajiye kofin shayin da ya shigo da shi ya tako gaban kitchen Island ɗin da take tsaye a bayan shi tana yanka ganyen albasa a kan chopping board.

"Kin tabbata? Idan akwai ki faɗa min ko akwai abinda zan iya yi a kai."

Sai ta ji guiwar ta yayi sanyi ko ɗaga ido ta kalle shi ta kasa. Ta so bashi haƙuri ne yau ɗin shiyasa ko saƙon shi na barka da Safiya ma bata amsa ba, kuma da ta kunna data taga yayi mata sallama a WhatsApp shima bata amsa ba. Amma yanzu da yake gaban ta sai take jin ba zata iya ba.

Kwarjinin shi ya cika ko'ina sai ta daɗa jinta ta kasa. Tsayar da komai a tsakanin su tun bai daɗa nisa ba shi kawai zai hana ta kukan da Safina ta roƙe ta kada ta sake komawa gareta da shi.

~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

91

"Aunty Reina wai ki zo in ji Daddy" cewar Irfan da ya leƙo kitchen ɗin

Tayi hanzarin amsawa da toh tana tashi daga gaban Yaseer daman ta kai ƙololuwa na takura, ta juya ta wanke hannun ta a sink sannan ta yi saurin bari masa kitchen ɗin yabi bayan ta da kallo ganin yanda take ta hanzari da bai san na meye ba.

A tunaninta mahaifin ta ne yake kira don har ta ɗauki hanyar ɗakin shi Alaji Abdou dake zaune a parlo ya kira sunan ta.

Fara'a ya kawo a kan fuskar ta da mamakin sammakon Alaji Abdou ɗin don ko karyawa basu yi ba. Karfe takwas ma bai cika ba.
"Ina kwana Daddy. Yaushe ka zo?" Ta fara miƙa gaisuwa kafin tambayar, Sannan ta isa gaban shi ta durƙusa kasancewar a kujeran zaman mutum ɗaya yake balle ta ɗan maƙale ta gefe.

"Ke kika ɗago ni ai mai babban suna. Wannan zuwan naki ne sai ki mun tarba mai kyau"

Ta ɗan dara sannan tace "toh ka faɗa min duk kalan abinda kake so ka karya da shi in yi maka Daddy"

Ya murmusa yana daɗa jin matsayin ta da na Aicha a cikin ran shi babu bambanci, don haka shi mai ɗaukan abu a wurin ɗaya ne ya bawa ƴar uwarta idan ta fita buƙata koda ace ɗayan ta ƙwallafa rai a kan abin. saboda duk yaƴan shi ne yana da iko da su.

"Toh shikkenan sai ki kasa kunne ki ji abinda nake so"

Ta jinjina kai "ko ganda ne Daddy na zan dafa maka"

"Bai ma kai shi wahala ba in sha Allah, kuma ba ni kaɗai ba duka iyayen ki zaki farantawa idan kika yi." Ya kalli cikin idanun ta da wani yanayi cikin muryar shi da tafi kama da umarni wanda bai taɓa mata magana da shi ba.
ya cigaba da cewa
"ɗan uwanki Yaseer muke so ki aura, shi kuma bilal zamu dakatar da shi"

Bata san kallon ƙurilla tayi ma Alaji Abdou na dogon lokaci cikin daskarewa ba sai da taji yace "zaki iya min ina mai sunan manya?"

Zaɓin Allah da tayi ta roƙa kenan da dukkan fatan ta? tana mai amincewa da duk yanda yayi da ita cikin izzar sa. mai kuma yayi saura?.

Kanta ta sauƙe Saboda ƙwallan dake shirin zubowa ta saka ƙasan mini Indonesian hijab ɗin dake wuyan ta ta goge shi sannan ta dube shi da murmushi wasu ƙwallan suna sake taruwa a cinkin idanunta tace "In sha Allah Daddy. Zan yi maka"

"Masha Allah alhamdulillah. Maraba da ƴa ta gari irin ki Hafsah. Allah yayi miki albarka ya albarkaci rayuwar ki" ya yi mata addu'a hannun shi a saman kanta ta amsa da "ameen Daddy, na gode"

Cikin jin daɗi yace "jeki ki ƙarasa aikin gaban ki, ranan da kika gama jarabawa kuma ki zo Mariama tana son ganin ki"

Ta amsa da 'toh' cikin shaƙewan murya don kukan da bata san na menene ba yake niman ƙwace mata. A maimakon ta koma kitchen sai ta shiga extra toilet ɗin dake ƙasa, ta ƙarasa bakin famfon shower ta kunna ruwa sannan ta tuɓe hijab ɗin wuyanta ta saka kanta a ƙasan famfon ta sake masa ruwan sanyi tana sauƙe numfashi. Ta ɗauki lokaci a haka har saida taji zafin da kan ya ɗauka ya ragu sannan ta mayar da hijab ɗin ta fito tana jan ƙafa.
A yanzu babu kowa na parlo, daga bakin kitchen ɗin ta tsaya tana jiyo hayaniyar su suna ayyukan su kamar kullum.

"Reina kin tsaya a hanya"

Ta matsa gefe ba tare da ta juya ba, Maama tayi mata kallo ɗaya tayi wucewar ta duk da yanayin yayar tata bai yi kama da wanda take cikin cikakkiyar nutsuwar ta ba Amma haka take ko kwana Reina zata yi tana kuka suna ɗaki ɗaya miskilanci ba zai barta ta tambayi abinda ya same ta ba.

Aicha da tazo wucewa ɗauke da Abinda ya fara zama ready zata kai dining itama tayi mata kallo ɗaya ta taɓe baki ta wuce.

"Reina wasa da ruwa kika yi?" Umma ta tambaya daga bayan ta. Sai a lokacin sauran wa'inda ke kitchen ɗin suka lura da ita. Umma ta juyo da ita tana ƙare mata kallo. Tana tsaye hijab ɗin kanta na digan ruwa har shatin kitson ta kana gani idanun ta sun kasa, ga gaban riganta ma a jiƙe.

Jan hanci tayi sannan cikin murya mai karyewa tace "kaina ne yake ciwo"

"Kuma sai ki saka masa ruwa a maimakon ki nemi magani?"

"Idan nayi hakan yana barin ciwon ne shiyasa"

Ta riƙo hannunta daya tana kai bayan ɗaya hannunta goshinta, kuma jikinta har ya ɗauki zafi. "Wani shirme ne wannan? Ai sai dai ki kara ma kan ki ciwo"

Yaseer ya ƙaraso yana faɗin "bari muje asibiti kawai Umma"

Saudat ta gyaɗa kai cikin gamsawu tana sakin hannun Reina amma ita sai ta riƙe ta gamm tana maƙalewa.
"Idan na sha ko paracetamol ma zai bari Allah."

Ganin tana shirin saka musu kuka Umma ta jawo ta cikin kitchen ɗin da hannun su dake cikin na juna. Tace Sabir ya miƙo first aid box a cabinet ɗin sama sannan ta ɓalla mata magani ta bata, Irfan ya miƙo ruwa aka bata ta sha. Yaseer dai nazarin ta yake yi daga gefe ganin yanzu ya riske ta lafiya lau amma yanzu har ta birkice, ko dai kiran da aka mata sanar da ita hukuncin da iyayen nasu suka yanke aka yi? Ya gyara tsayuwa ya zuba hannu cikin aljihun wandon cyan suit dake jikin shi, ya shiga zullumin yanda aka ƙare kuma.

Karɓan glass ɗin ruwan Umma tayi bayan ta gama sha ta ajiye Sannan ta sake riƙo hannun Reina zata maida ita ɗaki amma sai ta taho gaba ɗaya ta zube a jikinta ta rufe ido tana maida numfashi ba kuma kuka take yi ba.

Umma ta san kwanan zancen tunda da ita aka je aka sanar ma Ummi jiya sai ta riƙe ta da kyau a haka tana ɗan shafa bayanta. Ba karamin ƙokari Aicha tayi ba wajen ganin tsakin da take ja a cikin zuciyar ta bai fito ba.
Sun ɗau lokaci a haka har saida mai haƙuri yace "to a kaita ɗaki ta kwanta Umma, zata gaji da tsayuwan"

"Zaki iya tafiya?" Umma ta tambaye ta.

Gyaɗa kai tayi tana tsayawa da kyau don daman ɗumin mahaifiya take nima kuma da ta samu taji dama-dama sosai.

Ummah na rike da hannunta tana takawa a sannu suka bar kitchen ɗin.
ganin hawa stairs zai bata wahala sai ta shigar da ita ɗakin Aicha dake ƙasan tunda ita fita aiki zata yi.
Chapter 70 · 0% Book details