← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 117

Sashe 29

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsayawa yayi a harabar ground floor na Research Centre ɗin ƙarshen maganar ta yana saka kan shi juyawa. Jamal ya auri Reina? Toh ko dai Alzheimer's ne ya kama general da ya manta karatun da ya karanto mishi a kan abinda ya faru, da kuma yanda ya ɗauki fushi a lokacin? Har yana cewa zai cire Hauwa daga cikin ƴaƴan shi kafin ta ɓata masa suna?!.

Sauƙe wayar kawai yayi ya datse kiran bai daina jin wuri na juya masa ba yayi ƙoƙarin laluɓo numbern Ummi, da ƙyar ya samu kiran ya shiga kuma har ta tsinke ba'a ɗauka ba. Sake kira yayi da niyar maimaitawa sau ɗari har sai an ɗauka.

"Assalamu alaikum" Muryar Maama ya shiga kunnen shi. "Ta shiga toilet ne Ummin, idan ta fito zata kira.."

"Kice mata su yi sauri su je su ɗauko Reina daga gidan da take. Yanzu ba sai anjima ba!" Abinda yace kawai kenan ya katse kiran da niyyar idan sun ɗauko ta ɗin zai yi musu bayani kafin nan shima ya kamo hanya. Da sassarfa ya fita daga wurin yana danna kiran general a waya, security suka bi shi da kallo ganin yanzu ya shigo kuma har zai fita, abinda wata rana sai dare ta raba suke barin wurin.

Sai a yau ya taɓa danasanin rashin kasancewar shi soja, da shi da kan shi zai diran ma Jamal, Hauwa sai tayi dana sanin haihuwar shi da tayi, amma yanzun ma bai ɓaci ba.

......

Ajiye wayar a inda ta ɗauke shi Maama tayi bayan ya kashe kiran, ta juya zata fita sai ga Ummin ta fito daga ban ɗaki.

"Waye mai kira? Tun ɗazu nake jin ruri"

"Wannan Uncle ɗin ne na gidan su Reina, na faɗa mishi kina toilet"

"Ina laifin na shiga wanka Zainab?"

Sai ta murmusa kawai, ta juya ta bar ɗakin ba tare da ta faɗi aikan Uncle B ba.
Ita kuma Ummi bata kawo komi a ranta ba ganin dama yana yawan kira su gaisa, kuma numbern ƙasar waje ne katin dake wayan ba zai yi musu ko sakwan talatin ba, ta sani ma zai sake kira.

Sallan walha Ummi ta tada, da ta idar kuma ta ɗauki Alkur'ani tana karantawa har a sannan Maama bata gama wankin uniform ɗin da take ba.

Ba wai ta manta saƙon Uncle B bane, ita kawai bata son abinda zai haɗa ta da Reina ne ko a kalmar baki. Sai dai duk yanda taso shirirantar da zancen yanayin yanda taji muryar Uncle B ya tsaya mata a rai. Toh ko wani mummunan abu ne ya samu Reina ɗin?

Wannan tunanin ya saka ta miƙewa a firgice ta ruga ɗakin Ummi a guje da farin socks ɗin da take wankewa a hannu tana fidda numfashi tace "Ummi yace aje a ɗauko Reina daga gidan Uncle Salisu, yanzu ba sai anjima ba"

Gaban Ummi ya faɗi ganin fiye da minti talatin kenan ya faɗa mata.

"Wayyo Allah Zainab!.." sai ta rasa abinda zata ce mata ta miƙe tare da ajiye qur'anin a gaban mirror ta ɗauki wayan ta danna kiran babban yayan Fauziyya.

"Idan kana kusa kazo ka ɗauke ni, idan kuma kayi nesa kaje ka ɗauko Hafsatu daga gidan Salisu. Kada ka kuskura ka bar gidan sai sun baka ita duk rintsi don Allah" ta ƙarasa muryar ta na rawa sai hankalin Maama ya ƙara tashi, dana sani ya lulluɓeta.

.....

Har sha daya Reina bata karya ba, tana kwance a bakin ƙofar da ta garƙame da key ta saka lock kuma ta kwanta a jikin sa tsakanin rai da mutuwa. sun yi bugun ta fito har sun gaji, musamman ma da Hajiya Hauwa suka yi magana da Uncle B, taso ta saka Jamal yayi ma Reinan barazana yanda zasu kira shi tace ita take son auren ya rabu da ita, amma haka Jamal ɗin ya ƙaraci bugun shi tana ji harda cewa wai zai karya ƙofar. Yana da damar idan ya karya ɗin suyi yanda suka ga dama da ita amma ita da kanta dai ba zata buɗe mishi su cutar da ita ba.

Can bayan wani lokacin da ta kasance cikin shiru, ta fara jiyo hayaniya ya cika parlorn sai kuma kaman daga sama aka cigaba da knocking ƙofar, "Hajiyar mu!" Buɗe idon ta tayi jin muryar da ya kira ta. "Reina kina ji na.."

Bai rufe baki ba ƙofar ta buɗe sai ji yayi ta zuba a jikin shi kaman kayan wanki tana ɓoye fuskar ta. "Uncle dan Allah ka tafi da ni, zan mutu a nan, ka tafi dani dan Allah"

"Shikkenan mu tafi" gyara mata riƙo yayi a jikin shi, ya janyo saman hijabin jikinta ya rufe mata fuska kafin suka fara takawa a hankali, gangun matasan da ya ɗibo wanda suka fi Jamal ƙwaya suka kasa suka tsare a parlon, suka bashi damar fita da ita lafiya lau ya saka ta a mota suka rufa mishi baya har suka bar gidan kafin suka hau adaidaitan da suka zo dashi suma wasu a mashina suka bar unguwan ko tsaya since masu gadin gidan da suka ɗaɗɗaure basu yi ba.

Ganin yanayin jikin Reina kawai ya wuce da ita asibiti emergency, bai ɗauki kiran Ummi ba har sai da suka karɓe ta ya faɗa mata suna TH. Itama duk da tashin hankalin da ta shiga sai da ta sanar ma Uncle B saboda yanda ya addabe ta da kira.

Kwanan Reina 2 a emergency saboda numfashin ta kafin aka tura su ward, shima sai da ta kwana biyu tana shan ruwa da allurori.
Tun shekaran jiya Ummi suka yi magana da Uncle B yana hanya amma har Yanzu shiru, basu gan shi ba kuma bai kira ba. Haka ma daga gidan Alhaji Salisu babu wanda yazo, duk da ba wai idan suka zo ɗin zasu basu damar ganin ta bane ko Ummi zata barsu su bar asibitin haka nan ba. Yanzu ma jira suke yi Reina ta wartsake wallahi sai sun maka su a kotu tunda yarinya ta magantu, gaskiyar magana ta fito, sun ɗaura niyyar yin Shari'a dasu har supreme court, sai sun karɓa ma yarinya ƴancin ta, zasu san sun taɓa ƴar Fauziyyar Ummi.

Ranan da aka sallame ta suka koma gida daff maghriba. Bayan Isha sai ga drivern gidan Hajiya Hauwa ya shigo da huhun goro biyu da kwalin minti biyu shima wai na tambayar Reina ne, ya miƙa musu bundle ɗin dubu ɗari guda biyu sadakin ta, da kuma katin gayyata da aka riga aka buga, wai Aure nan da asabar mai zuwa in ji Alhaji salisu.

Yayyen Fauziyya tun suna daga zaune suka fara naɗe hannun riga kafin su miƙe drivern ya miƙe zai arci na kare, yama manta ko kuɗin bai ajiye musu ba. Suka samu suka damƙe shi a bakin ƙofa suka fara jibga kaman Allah ne ya aiko su.

Tsoron rasa aikin da yayi shekara da shekaru yana ɗaukan ɗawainiyar iyalan shi da shi ya saka shi wannan kasadan dama, Amma da ko nawa suka bashi ba zai yarda ba.

Ya haɗe hannun shi da sigan roƙo su yana ƙoƙarin arcewa amma sun sun rufu mishi ba ji ba gani. Har sun fara tara ƴan unguwa abinka da cikin gari.

Cikin mutanen dake lekowa ta gate kasancewar an bar ƙofar ta a buɗe Alaji Abdou ya buƙaci hanya suka bashi ya shigo.
Da ƙyar ya iya shiga tsakanin su sannan ya ɗauki kuɗin da drivern ya yar a ƙasa yace mishi "jeka kace an karɓa, Allah ya kaimu" ya faɗa yana riƙe Babban yayan Fauziyya ganin haka ɗayan ma ya haƙura suka bar shi ya gudu saboda mutuncin Alaji Abdou da suke gani.

Barin su yayi sai faman huci suke yi, ya nemi izinin shiga parlon, Ummi dai sai kuka take, an ma ci Sa'a Reina ta samu barci a ɗaki ba lallai ta san wainar da ake toyawa ba. Maama dake rarrashin Ummin ta taso tayi masa izinin shigowa itama tana hawaye.

Alaji Abdou ya ƙarasa ciki ya nemi wuri a ƙasa yana fuskantar Ummi.

"Allah sarki mutuwa, mutuwa mai tonon asiri, daga rashin mahaifi ko mahaifiya na rasa wanne yafi tozarta yarinyar nan, kaga yanzu niman kai suke yi da Ita Abdullahi. Naji tsoron hakkin Fauziyya a hannun Tahir ashe hakkin ƴar ta a hannun ƴan uwanshi shi zai saka ni zubar da hawaye."

Gyaran murya yayi ya ɗan matsa kusa da Ummi yace "Mama ki kwantar da hankalinki ki bar mu da su, in sha Allah jikar ki ɗaya bayan ɗaya sai mun bi mata hakkin ta. Amma yanzu ki bari su ɗaura auren nan kaman yanda suka yi niyya, don Allah kada ku sake yunƙurin dakatar da su"

Sai Ummi ta bar kukan tana kallon Alaji Abdou sheƙeƙe kaman wani kai ne ya sake tsirowa a gefen wuyar shi. Ƙaramin murmushi yayi ya juya ga Maama da ta tsare su da idanuwa yace "jeki ki kira min yayar ki"

"Tana bacci fa"

"Ki taso ta"

Da toh ta amsa ta miƙe zuwa uwar ɗakin Ummi.
Hayaniyar farko ya tada Reina daga barcin ta cure wuri guda a kurƴan gado cike da tsoro don gani take yi kaman yanda kawun ta yaje ɗauko ta a gidan haka suma su Jamal suka zo su ɗauke ta su koma.

Hawa gadon Maama tayi ta ɗaura hannun ta saman na Reina wanda ta rungume bargo a ƙirjin ta kaman shi zai zame mata kariya idan an kawo mata farmaki.

"Reina daddyn Niger ne yazo. Yana kiran ki"

Ta riga Maama fita daga ɗakin da gudu don yau idan ya kama a Niger zata kwana.

Kuka ne ya ƙwace mata da suka yi ido huɗu, daman aikin shi take yi sai idan ta gaji ta ɗora da ta huta.
Sai ya mayar mata da murmushi yana yafato ta da hannu, ta ƙaraso gaban shi ta durƙusa idanun su Ummi da kawunan ta a kanta.

Shafa kanta yayi cike da tausayawa bai tsaya lallashin ta ba don ya san hakan bayi da amfani a yanzu ya miƙa mata bundle ɗin kuɗin guda biyu "Ga sadakin ki nan"
Chapter 29 · 0% Book details