← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 117

Sashe 32

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alaji abdou bai ce komai ba har ta dasa aya. "Ina Hafsatu, mahaifin ta yana son ganinta"

"Toh bismillah mu shiga ciki mana, ai tana ciki sai ku gana"

"Mahaifin ta Tahir ne yake son ganinta ba ni ba, tunda auren ya fasu yana da burin tafiya da ƴar shi."

Ba kaman Reina da ta san Alaji Abdou zai iya wasa da ita ba har lokacin da ya bata kuɗin da ya kira da sadaki take jira yace mata wasa ne, Hajiya Hauwa ta san Alaji Abdou ba sa'ar wasan ta bane, sai dai idan hala bayi da lafiyar ƙwaƙwalwa toh wannan zata fahimta.

Murmushin kan fuskar ta take ƙoƙarin mayarwa amma ta gagara, da muryar alhini tace "Allah sarki, Allah ya jiƙan rai, yaci burin ganin wannan rana amma Allah bai yi ba"

"Ni na faɗa miki naci burin wannan rana Hauwa?"

Alhaji Tahir ya ƙaraso a wheel chair ɗin shi Sabir na tura shi, lokacin da take ta zuban zance suka fito ta ɗaya ɓangaren bata lura ba.

Cikin tsananin tashin hankali ta dafe ƙirji cikin ɗaga murya tace "Innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir rahmanir raheem!"

.....

*Yaseer*

Fitowa suka yi da Jamal hannun shi dake sanye da ankwa a bayan shi.

"Ba na faɗa maka zan ɗaiɗaita rayuwar ka ba? Ka ɗauka ƙarya ne?"

Ya ɗago ya dubi Yaseer wanda ya sake mishi saurayin murmushi, bai san shi ba, bai san mai ya haɗa su ba, haɗuwar su ɗaya a Rome, Italy. lokacin yabi sawun wasu kaya da zasu turo Ghana da Nigeria sai kuma yau.

"Ko ma wani cartel kake aiki ka guji ubannin gida na su biyo bayan ku, you'll be destroyed." Cewar Jamal cikin gargaɗi yana ƙoƙarin fisgewa yayi kan Yaseer.

"Matsala ta da kai ƙaramar ƙwaƙwalwa, shiyasa ko wancen lokacin ma ba ƙaramin wahala na sha ba kafin ka fara gane math" Yaseer ya ƙarasa tare da zare shaɗes ɗin idanun shi suka yi ido huɗu da Jamal.

Lokacin da suka yi alƙawarin zasu iya basu ya cika don haka suka cigaba da angiza ƙeyar Jamal, Suhail ya samu ya ɗan kai mishi naushi yana faɗin "wuce" tun jiya suke practice ɗin abinda zasu yi amma shi irfan bai samu dama ba aka jefa Jamal cikin mota.

Alhaji Salisu ya riga ya kwaɓe babban rigan da hulan kan shi amma an yi mishi shamaki da ƙarasawa wurin Jamal, har suka rufe motan suka yi gaba dashi.

Wannan wani irin tozarci ne za'a kama ango a ranar ɗaurin aure, bayan mutane sun gama taruwa kuma! Idan so suke yi su ɗauke shi sai su je gida tunda sassafe, yanzu yana da tabbacin sune a farkon shafin jaridar gobe.

Bai sani ba Yaseer ya taimake shi ma ya saka su a na yau, shine dai bai karanta ba. don haka ƴan jarida kaman an turo su daga sama da kayan aikin su, Jamal dai ya dawo Celebrity.

.......

Aunty Sajida ba zata iya jira sai sun gama dramar su kafin su ga highlight ba don haka ta shigo ta jawo hannun Reina da aka maido ta cikin su, Maama na maƙale da ita, itama ta riƙo hannun ta.
"Ku zo daddyn ku yazo"

Haka suke binta duka tunanin su wurin Alaji Abdou zasu je, to shi da yayi mata auren dole yanzu me zai ce mata idan ta je? Ko yana so ya zamo mutum na farko da zai shaida mata ta zamo mallakin Jamal ne? Mummunan ƙaddarar ta!

Idanun ta cikin na Alhaji Tahir suka fara shiga lokacin da ta fito, komi nata tsayawa yayi cakk kawai tana kallon shi cikin ido.

Riƙo hannun Maama dake ƙoƙarin ƙarasawa wurin Alaji Abdou tana mai fashewa da kuka tayi, don bata lura da Alhaji Tahir ba tukunna.

Da ƙyar ta iya buɗe baki murya na rawa tace "Dad..daddy na ne.. wannan?" Reina ta tambaya tana gwada Alhaji Tahir da duk yanda yaso yin dauriya sai da ƙwalla suka cika idanun shi.

Ta riƙe hannun Maama gamm, cikin rasa abin yi.

~~~~~

Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.

*Seemahwrites ✨*

65

~~~~~~~~~
_Don't hate you_
_But we can't save you_
~~~~~~~~~~

"Daddy kai ne?...Daddy na nake gani Wallahi, na gane shi shine" Ta jujjuya tana duban mutanen wurin da suka tsaya cirko-cirko suna kallon abun al'ajabi, babu wanda bai san da mutuwar Alhaji Tahir ɗin ba a cikin su, ba kwanan nan ba kuma, sai gashi yau ya bayyana gaban su.

Hajiya Hauwa ta daɗe da sumewa, su Zahra da mutanen ta suka yi kanta suna fifita wasu suka ɗibo ruwa aka shiga yayyafa mata. Koda tashin hankalin ta a kan abinda ke faruwa da Reina yana da yawa bai kai na cewa Alhaji Salisu ne yayi yunƙurin kashe Alhaji Tahir ɗin ba, sannan abinda ya rage daga dukiyar shi suka hau kai suka danne, bayan wanda suka haɗa baki da mutanen da suka cuce shi idan sun kwaso ana rabon dai-dai da shi.

"Nine sarauniya ta" yace da murya mai rauni, bai ɗauka zai karaya haka ba lokacin da ya saka su a idanun shi amma kuka yake yi hannun shi a kan fuskar shi.

Bai yi tsammani ba sai jinta yayi a jikin shi ta runƙume shi kaman zai ɓace ɓatt idan tayi wasa, Maama ma ta ƙaraso a guje ya haɗa su duka biyu ya rungume sai kuka, kuka ba mai saka damuwa ba sai dai wanke ta, irin kukan da ko a mafarki mutum yayi shi zai tashi da sanyin zuciya.

Tayi tsammanin idanun ta ne suke mata gizo, ko kuma mutuwa ce ta ƙwanƙwasa mata ƙofa shiyasa har ta fara ganin wanda suke jiran ta a can, amma hakan bai saka ta ƙasa a guiwa ba. Duk wani ɗa da ya rasa iyayen shi idan ace za'a bashi zaɓin sake ganawa dasu koda na second ɗaya ne they won't hesitate.

Sai dai jin ƴar uwarta ta ƙaraso tayi yanda tayi itama sai duk wani ɓakin ciki da ta taɓa shiga a rayuwar ta ya narke kaman kumfan teku, babu komai a cikin kan ta da zuciyar ta bayan farin ciki.

Sun ɗauki lokaci a haka kafin Alhaji Tahir ya ɗago su yana ƙoƙarin daidaita kan shi ganin kukan nasu yana niman wuce misali.

"Sarauniya ta kin girma, Mama na kema haka. Miƙe na gani"

Dariya mai hade da zubar wani hawayen Reina tayi kafin suka miƙe tsaye a hankali, ta juya a gaban Alhaji Tahir, Maama dai na rike da hannun shi.

Ta cikin wayan da Sabir ya kira shi video call Yaseer yake kallon ta, ko menene na rashin daɗi a tsakanin shi da Reina dole yaji mata ɗaɗi. Sannan ya ji sauƙin sauƙe ɗaya daga cikin alƙawuran da ya ɗauka, ta haɗu da mahaifin ta cikin aminci.

"Haka kika yi tsayi?, Lallai za'a bawa daddy Labarin wani irin taliya kike ci baki sam ma mamana ba" ya ƙara damƙe hannun Maama a cikin nashi itama.

Dariya dukkan su suka saka, amma a zahiri itama Maaman ba wai gajera bace, kawai dai yafi sanin sarauniyar shi ƴar kuttuɓa ce ita kuma Maama jikin ta jiya i yau.

.....

Tsayawa Yaseer yayi bayan an tafi da Jamal saboda akwai saƙon da yake son miƙawa Alhaji Salisu kafin su tafi, zai bayyana mishi kan shi, ya san da su waye yake karawa a wasan da ba zai yi nasara ba. Zai faɗa mishi shirin shi a kan su don yaji daɗin zama yana kallon shi yana fafutukar da babu hanya mai ɓullewa, har sai ya gaji, ya galabaita duk wani ƙarfi nashi ya ƙare kafin daga ƙarshe su yi mishi one blow seven die.

Tunkaro shi Alhaji Salisu yayi, Alhaji kalabu mai niman jin kwaƙwaf yana biye dashi, ganin tare suka zo da jami'an a tsammanin shi shima ɗaya daga cikin su ne. kaman wanda ya fara zarewa tsayuwa mai kyau ya gagara a gaban Yaseer.

Hannun shi biyu ya haɗe wuri guda "Yallaɓai, yallaɓai dan Allah. dududu satin sa biyu da dawowa ƙasar baki ɗayan ta yallabai, yanzu kuma auren shi za'a ɗaura kun zo kun kama shi bai yi muku komai ba."

"Bai yi komai ba kace? Shaidun da suka tabbatar da yana safara da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi ba komai bane?"

Riƙe baki Alhaji Salisu yayi cikin kaɗuwa "innalillahi! Wani shaidu kuma yallaɓai? Wallahi Wallahi kaji na rantse maka ɗana bai taɓa shan ƙwaya ba, bai ma santa ba, kai bani tsammanin ya taɓa ganin ta ma"

Yaseer ya jinjina kai murmushi na ƙwace masa duk yanda ya so yaci serious, yace "hakane. Ashe Irin rantsuwar da kayi kenan ka tseratar dashi daga fuskantar hukunci lokacin da yayi ƙoƙarin keta haddin Hafsatu a cikin gidan ka, sai aka ɗaura laifin wa ni da bani da gata bani da galihu ko?. Toh nima abinda nake shirin aikatawa kenan, sai na tabbatar yayi zaman firsina har tsufa ta kama shi kuma ko a ɓoye babu uban da ya isa ya fito dashi saboda zan mayar da shi bayi da gata bayi da galihu. Lastly sai na karɓa ma Hafsatu ƴancin ta domin bai ci banza ba!"

Ba Alhaji Salisu ba hatta Alhaji Kalabu kalan mamakin da ya kama shi bayi faɗuwa.
"Yaseer?!" Ya ambata cikin kasa gaskata sunan da ya sabulo daga bakin shi.

"Na'am, ashe zaka tuna ni" ya miƙe daga jinginen da yake ya mayar da tabaran sa idanu. "Idan da zan baka shawara da nace kada ka wahalar da kan ka, idan da hali ka sallama shi, don bayan ka muke son gani fiye da nashi, amma na sani ba zaka ji shawara ta ba. Kuma ka hanzarta kaje gidan ka bomb ya tashi".

Da haka Suhail ya buɗe mishi gidan baya Yaseer ya shiga ya tura ƙofar ya rufe masa sannan ya juyo wurin su Alhaji Salisu dake daskare a wurin ya ɗaga musu yatsu biyu a jikin goshin sa "Bye!" Yace ɗauke da shu'umin murmushi sannan ya shiga motar dake gaban na Yaseer ɗin a maimakon su koma tare kaman yanda suka zo amma so yake yi ya gwada musu duka motocin su ne.
Chapter 32 · 0% Book details