← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 117

Sashe 115

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuwa hidimarta take don ta san gaskiya dole zata yi halinta daga ƙarshe kuma wa'inda suka gwada musu yatsa saboda yaya Yaseer tunda shi yafi ƙarfin su tunkare shi zasu ji kunya.

Ana gobe za'a sake zaman kotu da jamal Sannan bayan kwana uka ayi da mahaifin shi Alhaji Tahir ya kira su emergency meeting.

Suna zaune a ƙasa iyayen su a sama har da Alaji Abdou suna fuskantar shi domin su ji dalilin tara su da yayi. Bayan yayi Sallama da ɗan takaitaccen jawabi yace "Hafsatu ina kin zo da littafin da nace miki?"

"Eh daddy" Reina ta amsa tana miƙewa tsaye da diary ɗin Aunty a hannunta ta tsallako ta miƙa masa hankalin ta dai bai kwanta ba ga zuciyar ta dake faman tsinkewa.

Karɓan diary ɗin yayi da godiya yace ta koma ta zauna. Dake ƙwaɗon jiki na buɗe sai ya buɗe farkon littafin ya kalla with a sad smile. Sai kuma ya kifa ta ya kai shafin karshe ba tare da ya sa carton opener da yasa aka kawo mishi ba saboda yanda littafin ya tsufa bakin wurin da ya nane har ya fara tashi don haka ya kama wurin ya ja ya ɗaye shi duka sannan ya ɗago takardan dake linke a wurin ya buɗe ya tabbatar ita ce sannan yayi hamadala.

Kallon fuskokin su na niman karin bayani yayi ya juyo musu da takardan. "Wannan shine original copy na contract ɗin mu da wa'inda na karɓi bashin kuɗin su." Ya daga wani photo copy a gefe ya haɗa su yana faɗin "wannan kuma shine wanda ɗan uwa na Salisu ya canza. Gashi nan ya karɓi ninkin kuɗin da na karɓa da suna na harda sa hannu na wanda ba ni nayi ba, amma wannan ba abun mamaki bane tunda akwai masu kamanta kofa. Ƴan kwanaki kafin nayi hatsari ina fara gano akwai lauje cikin naɗi cikin shirin nan na samu kaina da linke original copy ɗina na contract ɗin na lika a bangon littafin nan tare da haɗawa da shafin karshe na saka glue na nane shi a tsakani yanda idan ba wanda ya san da shi ba lura da shi zai yi masa wahala. Bayan abinda ya faru kuma sai nayi tsammanin na rasa littafin ashe Allah yayi da rabo na." Reina ta haɗiyi miyau tunawa da lokacin da Zaheera ta nace ta bata diaryn da kuma lokacin da ta tafi ta bar shi a gidan Hajiya Hauwa suka biyo ta dashi, ashe Allah ne ya so su da rahama har ta kula da littafin na tsawon shekaru haka.

Ta cigaba da sauraron Alhaji Tahir da yake cewa "Dake suma masu son zuciya ne sai suka amince da nashi a matsayin na gaskiya har suke niman ƙarin maƙudan kuɗaɗe daga wuri na bayan dukiyar da suka raba ni da shi tun a baya har yafi yawan dukiyar su da na karɓa da kuɗin ruwan da suka saka a kai. Amma ba zan tada magana ko ince zan bi hakki na ba tunda ni na ɗauko wuta da hannuna na zuba ta a cikin dukiya ta don haka dole ta cinye ta kurmus!. Amma ina daɗa kara godiya ma Allah da ya taƙaita mun wahalar a iya duniya ba in biya a lahira yanda bani da komai kuma nake niman ceto ba. Yanzu da wannan takardan zamu iya ƙare wancan Shari'ar, Salisu kuma yaje ya san yanda zai yi ya biya su kuɗin su da ya karba ni babu ruwa na."

Finale

*Reina's POV*

*Shari'a*

Bahaushe mai hikima yace Ranar wanka ba'a ɓoye cibiya, sannan ita kalma ta Shari'a ko a hausance nauyi take da shi ba sai an dangana da ɗakin kotu ko lokacin da zamu tsaya a gaban Ubangiji Ya cika ba, domin a duk sanda aka yi amfani da ita wani ne ya ɗauki hakkin wani, sannan za'a bawa ɗaya gaskiya ɗaya a bashi laifi koda kuwa shine mai niman adalci.

Haka zaman ta kasance shekaru goma baya kuma haka take a yau. idanuwan da suka shaida rashin adalci yau sun dawo da ƙari a kai domin wanda aka zalunta yayi ƙarfin da zai iya karɓan hakkin shi.
Gabatar da Shari'ar aka yi a gaban alƙali sannan aka shiga gabatar da hujjoji da shaidu, Jamal da ƙyar yake iya tsayuwa a kan ƙafatun shi kuma kaman ba a ɗakin kotun yake ba don hankalin shi ya tafi inda yafi masa nan tashin hankali.

Jin hannun shi nayi a ciki nawa mai rawa, nayi saurin ɗaga idanu na dube shi ya sake jinjina kai tare da matsa hannuna domin ya bani ƙwarin guiwa. "It's going to be fine Umry, we'll be fine" yayi reassuring dina.

murmushin ƙarfin hali nayi mishi, rabin zuciyana yana samun nutsuwar sanin ba ganin Jamal a gaba na bane ya ɗaga min hankali, Yaseer ya riga ni fahimtar hakan kuma da yayi mun nuni sai nima na fahimci hakan ne, rabin tashin hankalin da zuciyata zai kasance a ciki na yadda makomar shari'ar zata kasance ne, za'a bawa yaya Yaseer gaskiyan shi ko kuma dai za'a sake kalan na shekaru goma da ɗori baya. Da wani hujja zai karɓi gaskiyan shi? Bayan shaidun mu uku ne; Shi da abu ya ritsa da shi, Jamal da ya aikata, sai kuma ni da aka aikwata wa. Kuma duk cikin mu ni kaɗai ne za'a iya karɓan shaida na a matsayin mai ƙarfi kuma ya hana ni bayarwa. Bai yarda ya zo dani kotun nan ba saida nayi mishi alƙawarin ba zan yi yunƙurin aikata wani abu ba tare da izinin shi ba domin kaman yanda Mahaifina na ya rufa ma ƴar shi asiri a baya a yau ma mijina ya zaɓi ya rufa wa matar shi asiri.

A lokacin da komai ya tafi, Shari'a tayi zafi, kuma hujjojin da aka gabatar ya isa ayi nazari a kai, lawyern Yaseer ya buƙaci gabatar da shaidan shi na ƙarshe kafin a ƙarkare Shari'a. Aka bashi damar gabatar da shaidan a gaban kotu sannan ya juyo yayi mata alamu da ta fito.
Ta yi jinkiri kafin ta miƙe, ta san duk wanda ya san dalilinta zai fahimta domin zata iya bada tabbacin a ranar yau baki ɗayanta babu uwar da zata ga bakin rana kamar ta, tunda babu wata uwar da zata sadaukar da ɗan cikinta da kanta domin ta tseratar da kanta.

Ta ƙarasa bayan witness stand a hankali tayi rantsuwa ta gabatar da kanta sannan ta fara zayyana ma duniya ainihin abinda ya faru ta hanyar amsa tambayoyin lawyern Yaseer. Komai ta bayyana, bata bar komai ba a ciki tunda babu amfanin da hakan zai yi mata, ko babu wannan case ɗin gagarumin wanda Jamal ya sake saka kan shi a ciki ya gama da shi, ya riga ya gama yawo, yanzu wanda suke da sauran rayuwa a gaba ne ya zamo hakki a kanta ta tseratar da su domin idan wani abu ya same ta ko mijinta sauran yaran ta suma sun gama yawo.

Mijina nake kallo a lokacin da zuciyata yake bugawa a ƙirji na shi kuma idanun shi na gaba hannu na a cikin nashi ya riƙe da dukkan yardan shi. Na mayar da duba na kan Umman Jamal umman Zahra dake kuka tana amsa laifukan ɗanta, ta san su duka tunda ita take taya shi bisinewa amma ni kukan ya kasa zuwa mun, hawaye na a kafe na zuba mata na mujiya cike da rashin yarda har cecekucen wanda kaduwar su bata wuce mamaki da takaici ba ya cika kotun sai da alƙali tayi bugun gudumar ta suka sarara sannan ta bada hutun minti ashirin kafin a yanke hukunci sannan aka miƙe ta fita, wasu suka fita don kiran wasu, wasu kuma don bawa ƴan uwan su ma'aikatan jarida masu manyar na'urori rahoton da zasu yaɗa ma duniya.

Ina zaune a gefen Yaseer. Bani da karsashin motsawa ko nan da can kaman wanda aka dasa a matsugunin ta. Har lokacin da aka ɗauka ya cika aka dawo babu wanda yayi magana a cikin mu, ya barni in gama digesting ɗin abinda ya faru tukunna.

Alƙalin ta ɗan juya takardunta kafin ta fara magana cikin zartar da hukunci "wannan kotu ta saurari shaidun da aka gabatar, ta kuma binciki dukkan hujjojin da suka fito, an tabbatar da cewa wanda ake tuhuma Jamal Salisu Kamal ya aikata laifin da ake tuhumar shi shekaru goma da suka wuce, Na yunkurin aikata fyaɗe ga yarinya ƴar shekara tara a lokacin" ta faɗa tana kallon fuskar Jamal ɗin da ya samu dawowa cikin hayyacin shi bayan mahaifiyar shi wanda ta haife shi ta zo ta sadaukar dashi a gaban ɗumbin jama'a.
"Bugu da ƙari bayan aikata wannan laifi kun yi ƙarya a gaban kotu, kun daura laifin da ka aikata a kan wani mara laifi wato Yaseer Kamal, kun jawo aka ɗaure shi na tsawon shekaru uku, yayin da kai da iyayen ka kuka ɓoye gaskiya. Wannan laifi ne na perjury da obstruction of justice wanda yaci karo da sassan dokar ƙasar nan."

Na lumshe idanu na. Na daɗe ina burin ace rayuwata gabaki ɗayanta mafarki ne amma a wannan gaɓar fatar kasancewar shi zahiri nake yi. Daga ƙarshe dai kuskuren da muka aikata zai gyaru, nauyin dake ƙirji na zai ragu.

"Saboda haka, wannan kotu mai adalci ta yanke maka hukunci kamar haka. Shekaru 14 a gidan yari Saboda yunƙurin fyaɗe, shekaru 7 saboda ƙarya a ƙarƙashin rantsuwa da ƙazafi. Shekaru 4 saboda cin zarafin tunani da ruhi ta fuskar ita yarinyar da aka aikatawa laifi da ya kaita ga jinyar lafiyar ƙwaƙwalwa."

Ban san ko bayan ni akwai wanda suke maimaita kalmar alhamdulillah babu iyaka ko kuma nawa ne ya fito daga zuciyata yake shiga kunne na ba.

"Ga mahaifin ka Salisu Kamal" Alƙali ta juya ta dubi Alhaji Salisu "Kotu ta tabbatar cewa ka taimaka wajen ɓoye gaskiya, ka hana Shari'a ta tafi yanda ya dace saboda haka zaka shafe shekara biyar a kurkuku ko ka biya taran Naira miliyan 20."
Chapter 115 · 0% Book details