← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 117

Sashe 3

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko babu komai bai yi asarar rayuwar shi da lokacin shi gaba ɗaya cikin shekaru uku ba.
A farkon kawo shi nan ya ɗauka duhu na har abada ne ya lulluɓe shi ba zai ƙara ganin haske a rayuwar shi ba kuma. Amma a cikin qur'ani ya fara samun haske, a cikin ƙur'ani ya fara samun sauƙin ƙunan zuciya, ya so shiga masifu da yawa a wannan wuri, an fara cin zalin shi saboda ƙarancin shekarun shi, an so saka shi a cikin hidiman kasuwancin ƙwaya Saboda yanayin shi da calmness ɗin shi ba za'a taɓa zargin shi ba idan anzo bincike, da wasu kalolin bala'in da bai san dasu ba ma a tsohuwar duniyar shi, amma Allah ya tseratar da shi, ilimin addini da ƙur'ani ya ɗaga darajar shi a idanun kowa har wasu da kansu suke niman koyo daga gare shi. Kaman wasa kuwa, bayan shekaru uku har sun fara sauƙewa a hannun shi.

.......
*Reina*

Fitowa tayi daga ɗakin bayan sun fidda tsammani da fitowar ta, Kayan tun jiya ne a jikin ta, bata samu damar sauyawa zuwa na barci a daren jiyan ba, hatta Barci ɓarawo sace ta yayi, tare da mugayen mafarkayya. Farkawar ta sau biyu tana isti'aza da tofa adduo'in da Yaseer ya koya mata amma sai da safen ta samu tayi barcin a nutse.

Wuce ƙofar ɗakin ɓaki tazo yi sai ta ja ta tsaya, kallon ƙofar take yi tana tuna abinda Ya faru a ɗakin a wancan ranar. Saboda lokaci ya ja, hoton Jamal da yunƙurin shi a kanta ya fara zama duru-duru a cikin tunaninta amma bata jin zata taɓa mantawa da Ranar da yayi dalilin rasa Yaseer a rayuwan ta.

"Ƙaraso mana Hafsatu" Hajiya Hauwa tace a dake, ba wai nutsuwa ta samu da zaman Reina a tare dasu ba Allah ya gani, babu yanda suka iya ne kawai.

Ta ƙarasa jikin dining da kowa yake fama da abinda ke kan plate ɗin shi, kujerar da babu kowa a kai ta ja ta zauna, ɗaga kan da zata yi idanun ta ya sauƙa cikin na Zahra, kafin tayi yunƙurin ɗauke nata ta watsa mata mummunan harara, sannan ta mayar da hankalin ta kan wayar da take danna shi da hannu ɗaya, ɗaya hannun na kai abinci bakinta.
Reina ta taɓe baki. Zahra tayi mugun Sa'a ƴan bala'in ta basa kusa yanzu amma da ko ramawa sai tayi.

"Da kika kama wuri kika hakimce waye zai yi serving ɗin ki hajjaju?" Sai ta ɗaga ido ta kalli Hajiya Hauwa dake faman tsare gida. Ita ta saba a gidan su abincin ma idan ta so a baki za'a bata, ita komai mata daddynta yake sakawa ayi.

Bata motsa ba, tana zaune kaman an shuka dusa, bata fasa kallon Hajiya Hauwa cikin ido ba kuma.
"Mu nan muna da tarbiyya bari kiji, so ki sauƙa kiyi serving kanki tunda babu wanda kika ajiye." Hajiya Hauwa ta ware mata idanu da nufin tsorata ta ɗaga nata daga cikin su.

Zaheera ce ta miƙe ta buɗe food flask mafi kusa da ita kana ta ɗauki plate ɗin gaban Reina zata zuba mata abinda ke ciki Alhaji Salisu yace "Bata ta saka da kanta!"

Marairaice fuska tayi, ita tausayi Reina take bata tunda ance bata da kowa yanzu "Abbah Please, wannan ba komai bane"

Jin bai sake cewa komai ba Zaheera ta warware foil papern cikin flask ɗin sannan ta shiga zuba ma Reina soyayyen doya da ƙoyi, ta zuba mata farfesun kaza da egg sauce kana ta ajiye a gabanta ta rufe kulolin ta shiga haɗa mata tea mai kauri.

Bata ce komai ba har Zaheera ta gama haɗa mata komai ta koma ta zauna tana sake mata murmushi.
Amma sai Reina ta ɗan ture plate ɗin daga gabanta tana yamutsa fuska bayan ta ƙare ma abincin kallo.

"Ni bani cin wannan"

Da ba'a Hajiya Hauwa tace "toh sai me kike ci?"

Bata san ba'a ba, a lokacin baya babu mai ƙarfin guiwar mata wani abun bayan lallashi, sai ta amsa da.
"Waffles nake so. A saka chocolate spread da whipped cream da maple syrup da kuma strawberries a kai"

Wannan karon duk tagwayen idanuwan dake zagaye da teburin sai da ya dawo gareta, mamaki ya saka su warewa a kanta.

Ba wai zata ci waffles ɗin bane saboda ta ji daɗin shi sai don yunwar da ya addabe ta, domin rabon ta da saka wani abu a cikin ta tun jiya da rana, amma a hakan idan basu yi mishi haɗin da take so ba ta san ba iya ci zatayi ba.

Tuntsirewa da dariya Hajiya Hauwa tayi, wato yarinyar nan ta ɗauka daa da yanzu ɗaya ne ko? Babu komai a hankali zata gyara mata zama.

Suna gama karyawar su kowa ya miƙe ya kama gaban shi, masu aiki suka zo suka tattare wurin aka bar Reina da zaman jiran waffles.

Yau ne, gobe ne, har 11 ta wuce babu waffles babu labarin shi, cikinta sai kuka yake yi, tana jin kaman ana tona rami a cikin sa. kaman mai azumi take jinta duk da har yanzu bata taɓa gwada cikakke ba don bata jurar yunwa saidai rabi zuwa sha biyun rana, amma a hakan wahalar shi take ji.

Yanke shawarar zuwa ta leƙa kitchen ɗin tayi taga ko sun kusa gamawa wayam babu kowa a kitchen, hatta kwanukan da aka ci abinci an wanke an mayar dasu wurin zaman su an share ko ina an goge.

Kai tsaye ɗakin Hajiya Hauwa ta wuce ta shiga buga mata ƙofa.

*Seemahwrites ✨*

43

Jin bugun yayi tsanani Hajiya Hauwa ta buɗe ƙofar ɗayan hannun ta ɗauke da ɗan kunnen da take ƙoƙarin maƙalawa a kunne.
"Hafsatu lafiya?"

Turo baki tayi tace "ina ta jiran waffles ɗinne fa Umman J..." Sai ta gagara ƙarasa kiran sunan, ta manta rabon da ta ambace shi a saman harshen ta, tun ranar da ta bayyana gaskiya ya zama karo na ƙarshe kuma bata sake taka ƙafar ta a cikin gidan ba sai jiya.
"Ina ta jira"

Takaici ya lulluɓe Hajiya Hauwa, Idan bata yi ta bar wa Reina gidan nan ba karairaya ta zata yi a kwana ɗaya kawai. Don haka ta mayar da kofarta ta rufe a kan fuskar ta, sai dai ko komawa kan abinda take yi bata samu ba wani bugun ya sake biyo baya.

A zuciye ta dawo ta buɗe ƙofar da niyyar sauke wa Reina marin da sai taga taurari sun gifta a idanun ta amma mamakin ganin tana kuka shar-shar da hawayen ta ya saka ta sauƙe hannun.

"Umman Zahra Wallahi yunwa nake ji sosai"

"Haba?? Gashi kuwa mu bamu da waffles, me zaki ci kenan?"

"To ko pan cake a mun dan Allah, sai a saka min chocolate spread ko maple syrup da butter a kai"

Sai da dariya ya kuɓuce ma Hajiya Hauwa, lallai zata ci uban yarinyar nan da cokali, ayyanawa take yi a ranta idan ta fara ɗirka mata tuwo sai ta tsani kanta.

"To ki jira kaɗan bari ayi miki kinji, ina baki sha tea ɗin ɗazun ba?"

Jan hanci tayi cikin muryar kuka tace "Eh, bani shan Milo sai Nesquik ko ovaltine"

"Gaskiya ne, to ki ɗan ƙara haƙuri kin ji? Yanzu zan saka ayi miki"

Hannun ta na kan tulelen cikin ta kaman matashiyar akuya mai juna biyu ta gyaɗa kai "to ayi sauri Please" kana ta juya ta koma babban parlour mai haɗe da kitchen ɗin tana zaman jira.

Ita kuwa Hajiya Hauwa shirinta ta ƙarasa a tsanake, ta fito sai tashin ƙamshi take yi tana kaɗa key ɗin sabuwar Jeep ɗinta.

Ɗakin Zahra ta ƙwanƙwasa tare da tura ƙofar ta kutsa kai.

Tana kwance saman gado tana video call ta riske ta, tana ta ƙyalƙyala dariya, daga ita sai wata ƴar ficikar vest ga halittun ta sun fara bayyana.
Firgigit tayi ta miƙe tana gyara zaman rigan domin bata ji knocking ɗin ba tunda kunnuwan ta a toshe suke.

"Sorry guys, I'll call you back mummy ta shigo" ta katse kiran ta cire airpods ɗin kunnen ta sannan ta kwaɓe fuska.
"Umma na ce kina knocking kafin ki shigo Please, Allah zan fara sakawa ƙofana key"

"Kin toshe kunne kina dariya kaman mahaukaciya daman ta ina zaki ji ni?. Da wa kike video call tsirara?"

Waro idanu tayi tana taɓa baƙin vest ɗin jikin ta ko Hajiya Hauwa bata gani da kyau ne. "Ƴan ajin mu ne fa, kuma ga kaya a jiki na?!"

"Mata ne zalla?"

Bata ɓata lokaci wurin gyaɗa mata kai ba dukda ba zallan matan bane, mazan ma sun fi yawa amma a ganin ta normal ne tunda duk friends ɗinta ne, ƙauyanci kawai ummanta take fama da shi da ra'ayi irin na mutanen da.

"Toh shikkenan ni zan fita, kije ki rufo min store ki ajiye key a wurin ki kuma ko wani yazo nima kice na tafi da shi, Idan yunwa yaci min ƙaniyar ta zata dawo dai-dai."

"Wannan Reina ɗin ne ko?" Zahra ta yatsine fuska, tuntuni jinin su bai zo ɗaya ba samm, kuma hakan ya samo nasaba ne a yawan kushewa da zagin da su Hajiya hauwan suke ma iyayen Reina har ya fara sauƙowa kanta a gaban yaran su.

"Eh fa! Kiji min yarinya da iya shege wai ni zata sauƙe ma jaraban da ubanta ya ɗaura mata.
A da ɗin ma ai da kuɗin shi ake yi yanzu kuma ina kuɗin?"
(Ko Hajiya Hauwa ta manta da mai shekara 15 take magana ne?
Kokuwa sabo ne da zuban zance kowani iri a gaban ƙananun yara? a saka su tashi da tsanar wanda bai yi musu komai ba, a dasa musu mugayen halayya da munanan ra'ayi da ƙananun shekaru.?)

Kwafa Zahra tayi "Ai har bread da cornflakes ma ɗagawa zanyi daga kan dining muga yanda zatayi yau"

"Toh sai na dawo, kina saka riga mai mutunci a jikin ki idan video call ɗin naku da maza kinji nafaɗa miki. Sannan Ki gwada bari na murɗa kofar nan na jita a kulle ki gani, a ranar zaki koma kwana ɗaki ɗaya da Zaheera da wancan yarinyar."

"Allah ya sawaƙe" ta furta a ƙasan maƙoshi.
Chapter 3 · 0% Book details