Sashe 71
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saida ummah ta saka ta cire hijab da rigan dake a jike Sannan ta dauko wani shirt ɗin Aicha ta bata ta saka, ta kwanta ta rufe ido ba'a ɗau lokaci ba barci ya ɗauke ta.
.
.
Buɗe ido tayi tana jinta sakayau kaman ba ita ce ta kwanta da matsanancin ciwon kai ba. Ta tashi zaune tana kallon agogon dake manne a bangon ɗakin ƙarfe 10:23 na safiya.
Wayanta ta gani a gefen ta ga tray ɗin abinci a kan ɗan coffee table dake tsakiyar ɗakin.
Kallo tabi ɗakin da shi dan yau ne karo na farko da ta fara tako kafan ta ciki. Ba ƙaramin kyau kuma ɗakin yayi mata hatta agogon kallon lokaci dake da wani irin shape kaman bubble guda biyu a manne abun kallo ne balle furnitures da sauran kayan ƙawa. Aicha ƴar gayu ce, irin gayun nan da a jini yake komai na mutum sai ya kasance mai class, har ɗan simple riganta da ta ara ta saka a jikinta. amma gata nan ita Yaseer ya zaɓa kuma ita aka bawa Yaseer, Ya Allah.
Bata gama tunani ba Saudat ta turo ƙofar ta shigo ɗauke da ƙaramin flask da mug a kan wani tray din.
"Yauwa kin tashi? Daman ina da shirin ɗaga ki tunda babu komai a cikin ki in yaso idan kika karya sai ki koma ki kwanta."
Ta ajiye tray ɗin sannan ta shiga zuba mata abincin ta saka cokali ta zauna a bakin gadon tukunna ta miƙo mata.
Karba Reina tayi da godiya ta fara ci a hankali idanunta a ƙasa tunda yanzu Umma ta tabbata surkuwar ta.
"Dan Allah kada ki saka damuwa ma ranki, ki sani iyaye ba zasu zaɓa ma yaran su abinda zai cutar da su ba, idan ma Allah ya kiyaye hakan ta faru toh sai inda ƙarfin mu ya ƙare."
Ta gyaɗa kai ta ƙara kaimi Wurin cin abincin don Umma ta fahimci ta ɗauki maganan ta. Rabi taci tace ta ƙoshi umma ta tsiyaya mata kunun gyaɗan da ta shigo da shi shima ta ɗan sha sosai kafin ta ajiye.
A tunaninta umman fita zatayi sai taga ta koma kan kujera ta ɗauko remote ta kunna TV ta saka wani Indian series ta cigaba da kallo, kafin shuɗewan awa guda Reina ta san duk abinda ya faru tun daga farkon series din umma ta bata labari, don haka ta maida hankali suka ƙarasa kallo tare don ya dauki hankalin ta sannan Umma ta mayar wani Hausa series shima suka kalla tare. Kafin ayi la'asar sai ga Reina ta wartsake kuma kaso mafi girma na abinda take ji ya tafi.
"Sauran muku jarabawa nawa ku gama?" Umma ta tambaya lokacin da ta miƙe zata bar ɗakin.
"Uku" Reina ta amsa. "Nan da sati daya in sha Allah mun kammala"
Ta jinjina kai "Toh daga yau sai ki koma karatun ki a ɗaki abin ki, idan ma baki iyawa ke kaɗai sai ki ƙokarta na yau, sauran biyun kuma safina tazo miki ɗaya ki je gidan su a ɗaya kema"
Da toh ta amsa tana ayyanawa a ranta daman ita ina wani karatu zai yiwu da yaya Yaseer yanzu? Hala sai tafi jin nauyin shi fiye da umman ma.
Sai da umma ta fita daga ɗakin sannan tabi ta kan wayar ta. Ga missed calls ɗin uncle B da suka shigo a lokacin da suka saba waya tunda ya san yau bata da exams.
Sai ta tsaya kallon sunan, daga yau kalma mai kama da na soyayya ba zai sake shiga tsakanin su ba hala sai dai mutunci. Zata yi kewar shi da Mufid sosai kuma ba wai don bata amince da hukuncin da iyayen ta suka yanke bane amma zata so ta san dalilin da ya saka zasu hana shi ita.
Hannunta ta kai kan numbern tayi sliding ya ɓace daga fuskar wayan a maimakon mayar da kira da take yi a duk lokacin da ya bayyana haka.
Samun space a kan wayar ya bawa saƙon da Yaseer ya turo awa ɗaya da ya wuce daman leƙowa.
Ta ɗan yi jinkiri na sakwanni biyar sannan ta danna shi ya buɗe.
Ga kuma abinda yake cewa.
"I don't know how or where to even start this. A karo na farko na samu kaina da rikicewa a kan Abinda ya shafe ki, I'm really sorry idan ya zo miki a bazata nima haka yazo min dukda ba hakan na shirya mana ba amma nayi imani wannan shine daidai Saboda shirin Ubangiji ne da kansa kuma ina matuƙar farin ciki da masa godiya. Ki yarda Reina ban shigo cikin rayuwan ki don in ɗaiɗaita shi ba sai don mu zamo mahaɗi na rayuwar juna.
I want to be your partner for life.
Ki amince ki zama abokiyar rayuwa ta.
I want to protect you and I want you to represent me.
Ina son duk inda aka ga Reina a san Yaseer yana tafe.
I want to spread your wings and help you fly.
In zama mataimakin ki a duk abinda kika saka a gaba.
I want to hold your hand and walk you every step of the way.
Duk wuya duk daɗi Hafsat, duk wuya duk daɗi Reina. Duk wuya duk daɗi Yaseer ba zai wulakanta ki ba nayi alƙawari"
Jan hanci tayi sosai sannan ta samu kuka yazo mata Finally. Ranan ya faɗa mata abinda yake so ta zamo mishi yau kuma ya sanar da ita abinda zai zamo mata. Yaya Yaseer is clear with his intentions babu ɓoye-ɓoye a cikin lamarin shi, Allah yasa ya same ta yanda yayi tsammani shima, Allah yasa kada ta bawa wa'inda suka karar da ƙokarin su a kanta kunya.
.
.
.
Ta idar da sallan la'asar kenan tana addu'a aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin.
Ta mike taje ta buɗe sai ga Alhaji Tahir a kan keken shi.
"Sarauniya ta"
"Daddy da kanka?" Ta amsa tana matsa masa a hanya ya shigo.
"Na zo duba jikin ki ne. Mun saka miki damuwa ko?"
Mayar da ƙofar tayi ta rufe bayan ya gama shigowa ta dawo cikin ɗakin ta zauna a kan darduman da ta idar da Sallah kana ta shiga gaida shi tunda basu haɗu ba tun safiya.
Saida ya amsa gaisuwar ya dube ta da kyau ya daura da "Bani da burin da ya wuce in ga ke da ƴar uwar ki kuna cikin kyakkyawar rayuwa Hafsatu. Ƙokarin da kawai zan yi kenan in sauke amanar da Allah ya daura min in haɗu da ubangiji na da kuma Fauziyya lafiya.
Nayi soyayya, na san daɗinta na san zafin rabuwa da masoyi ba zato ba tsammani amma ki saka ma ranki Allah bai yi Bilal mijinki bane.
Bani da burin da ya wuce in kaiki gidan da zan kwanta in yi barci cikin kwanciyar hankali ba tare da taraddadin kina cikin wani hali ba. In kai ki inda idan naji shiru na san lafiya ne yayi yawa, in sha Allah kuma irin zaɓin da nayi miki kenan"
Murya can ƙasa tace "Nagode Daddy Allah ya kara lafiya da nisan kwana, Allah ya jikan Aunty da rahama."
"Ameen ɗiyan albarka. Allah ya faranta miki yanda kika faranta min, kema Allah ya azurta ki da ƴaƴa na gari masu biyayya wa'inda zasu ji ƙan ki su zame miki sanyin idaniya kaman yanda kika zama min"
Hawayen farin ciki na bin fuskarta ta amsa da "Ameen Daddy."
A wannan lokacin ta fahimci cewa Yaseer shine maslaha da Allah ya saka a rayuwar ta, kuma a shirye take da ta rungumi ƙaddarar ta hannu bibbiyu.
~~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
92
Mantawa da rigan Aicha ne a jikinta ya saka tana gama tattare mata ɗakin kaman yanda ta same shi ta fito da nufin wucewa nasu tunda taji daɗin jikinta.
Tsayawa turus Reina tayi suna kallon kallo da Aicha da suka yi karo ta nufo ɗakin, ta bita da kallon tuhuma lokacin da idanunta suka sauƙa a kan rigan wanda couple set ne Yaseer ya siya lokacin da suka je wani aiki Germany ta matsa mishi sai da ya bata na matan.
Reina ma tabi rigan da kallo sannan ta mayar da duban ta kan Aicha tace "Umma ne ta bani da riga na ya jiƙe idan na wanke zan dawo miki da shi"
sai ta rasa da me zata amsa mata ma har ta raɓa ta gefen ta ta wuce.
Gani take kaman wasu abubuwan da gayya Reina take yi don ta ƙuntata mata, tunda ta samu Yaseer yana kula ta, amma in dai shine gata ga shi itama haka zata yi ta bari.
"Yaya jikin ki?.. Kin sake shan magani?... Me kike so ki ci?..." Muryar shi dake shiga kunnen ta kalma bayan kalma ya saka ta juya ta koma parlon ta tsaya tana kallon su. Duk tambayoyin da yake ma Reina da kai take amsawa idanun ta a ƙasa saboda makirci da munafurci.
Ko ita ce dalilin da ya saka ya ɗago su daga office basu gama ayyukan gaban su ba? Saboda ya zo ya ganta? Yaseer yana mantawa tana da tsayayye ne wai?.
Bai tashi lura da Aicha ba saida Reina ta bar parlon. Ta ɗauka zai gwada alamun jin nauyi ko makamancin sa amma sai ya miƙe yana duban agogon hannun shi. "Ki je ki huta Aisha nima bari na wuce" da faɗan haka ya ɗauki briefcase ɗin shi da ya taro aiki zai ƙarasa a gida ya juya ya barta a wurin.
Aisha! Ita kam zata fi ganewa ya zage ta da ya kira sunan ta.
.....
"Uncle Bilal ka fahimce ni mana dan Allah! ko umarnin iyaye na kake so in saɓa?"
Baya yayi ya jingina da kujerar da yake zaune yana kallon macen dake zaune a gaban ƙaramin teburin da ya raba tsakanin su cikin zumbulelen Hijabi, niqab, safar hannu da na ƙafa duk don kada a samu wanda zai gane itace a tare da shi.
Haka yaso killace ta, haka ya so ɓoye ta daga idanun duniya baki ɗaya, ta zamo tashi shi kaɗai idanun shi ne kawai keda damar ganinta, amma ba wai ta ɓuya ma nashi idanun ba.