Sashe 51
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Dan Allah kai ne gatan matasa?!" Zahra ta riƙe baki idanun ta kaman zasu faɗo, tun fitowan shi kallo ɗaya tayi mishi ta gane shi, kai yanda take bibiyar shi a yanzu ko bayan ƙeyar shi ta gani zata iya gane shi, shock ne ya hanata magana sai yanzu.
Kallon tara saura kwata ya watsa mata kana ya ɗauke kai ya juya ya fuskanci Reina yace "muje ina da magana da ke" da sauri ta gyaɗa kai ta ɗauki hanyar ciki.
"Kayan ta ne fa muka kawo" faɗin Zaheera ganin da gaske tafiya zasu yi su bar su a wurin.
Yaseer ya juyo ya kalli akwatin da babu ƙafa guda ɗaya a cikin huɗun da ya kamata ace yana da shi bayan koɗewa da tsufar da yayi.
"Ku riƙe, an bar muku. Sannan zaku iya tafiya" ya koma ya tsaya yana jiran ya ga sun wuce, Zahra kam bata farfaɗo daga suman tsayen da tayi ba tukun.
Zaheera ta dubi Reina tace "diary ɗin ki fa da wayan ki?"
Ta tsayar da akwatin zata ciro abu a jakar ta amma rashin cikan tayoyi ya saka akwatin collapsing a wurin ya faɗi.
Ta dai share shi ta zaro diary ɗin da wani wayan daban ba wanda ta bari a gidan ba.
"Ba cewa nayi an bar muku ba?" Yaseer ya tambaya.
"Har da wayan?" Zaheera ta ware ido da mamaki, Sabo Alhaji Salisu ya siyo wannan ɗin yace a kawo.
Kallon da ya bita da shi ya saka ta kawar da ganin ta har da bakin da ta buɗe ta rufe shi.
Reina ta ɗan matso kusa da Yaseer sannan cikin ƙasa da murya tace "Please diary ɗin Aunty ne ka bari in karɓa"
A maimakon ya bata daman karɓan sai ya juya ya fara sauƙa daga matakalar har ya isa gaban su Zaheera ya miƙa mata hannu ta bashi. Wayyoo Zahra ina zata saka kanta gata kusa da YK gatan matasa.
Hannu na rawa Zaheera ta mika mishi wayan da diary ɗin sai ya matsar da hannun shi.
"Just the book."
Ta haɗiyi miyau ta cire wayan sannan ta miƙa mishi diary ɗin ya karɓa.
Dai-dai lokacin da ƙofar ya sake buɗewa Irfan ya fito da rike da sabon wayan Reina wanda har yanzu bata samu ta saka mishi jacket ba, ko screen guard ma babu a jiki.
"Aunty Reina your phone is ringing" ya miƙa mata wayan yana ƙarawa da "wani wai Uncle Bilal ne mai kira"
Yaseer ya juya ya watsa mishi harara "toh wa ya tambaye ka?"
Ganin Irfan Zahra ta ƙara kiɗima ta shiga bubbuga kanta domin ta tuna da sunan shi.
"Irfan Kamal J! Autan ƴan gata right?"
Sai a lokacin ya lura da su "yeah that's me" ya raɓa towel din goge gogen shi a kafaɗa yana bin su da kallo. "Yaya kuke? Amma yaya da shigan ƴan iska ladies?"
Kallon fitted gown ɗin dake jikin kowannen su suka yi wanda ba don darajar wanda ya ƙirƙiri dogon zip ba basu san ta inda zasu saka shi ko su cire ba, gashi babu mayafi haka suke yawo kaman dankalin sayawa.
Suka sake duban borno style ɗin dake jikin Reina (riga mai faɗi iya guiwa da straight skirt) sai suka ga tayi wani daraja a idanun su, they feel small a gaban ta dukda yawan kwallaiyar dake kan fuskar su babu a tata fuskar.
"Shikkenan mun tafi, ki gaida mutanen gidan sai mun sake zuwa ko kin zo, don yau sauri muke" cewar Zaheera tana riƙo hannun Zahra.
Yaseer bai ƙara second 5 a wurin ba ya wuce ciki Reina ma tabi bayan shi. Study Room taga ya nufa ta mara mishi baya, bata san yaya su Zaheera suka ƙare ba kuma.
"Zauna" yace da ita yana ƙarasawa jikin printer ya ɗauko papern da ya fitar ɗazu kafin ya fita niman ta. Ya zauna a kujerar shi ya ajiye takardan a kan table sannan ya ɗaura pen a kai ya tura mata.
"Gashi ki karanta sai kiyi signing"
Ɗaga takardan tayi tana dubawa, da ta karanta title ɗin sai da tayi murmushi mai sauti ganin wai 'Contract for snacks making' su doughnut da meat pie ne sai an yi musu takarda?. Amma lokacin da taga yawan shi saida ta ƙwalalo ido.
"Pieces 600?"
"Yes. cake, doughnut, meat pie, samosa, Spring rolls, pepper chicken da drinks. Kowanne pieces 600 zaki mana packaging na wani event ne za'a yi for two days kullum za'a karɓi dari uku-uku kenan and in two weeks muke so, idan kin amince sai ki saka hannu in tura miki deposit idan kin gama a tura miki sauran kuɗin ki."
"Yaya Yaseer ai ko wata biyu ka bani ba zan iya wannan aikin ba balle sati biyu, ni na san yanda ake siyar da kaji ne ma? Na ɗauka ba zai wuce pieces 30-30 zuwa hamsin ba?"
Da sanin shi yayi mata hakan yanzu idan ta zamo occupied ga karatu ga aiki zai ga ta inda zata ke samun lokacin da zata dinga rashewa a jikin waya. Kuma da ta gama yaga bata saduda ba zai sake ɗauko wani ya bata tunda basu rabuwa da taro.
"Ga dai takarda a hannun ki, zaki iya tunani daga yanzu zuwa gobe ina jiran answer"
miƙewa tayi idanun ta a kan takardar, har ta nufi hanyar fita ya kira sunanta ta juyo.
"Babu abinda kika manta?"
Ya ɗauka hankalin ta zai bata wannan dama ce da zata yi amfani dashi ta bashi haƙurin abinda ya faru kuma tayi alƙawarin dainawa don a tunanin shi a shirun shi zata fahimci girman laifin da ta aikata.
"Ohh..." Da sauri ta dawo ta ɗauki biron da ya ajiye mata tayi gaba abinta.
Yaseer yayi mata rakiyar idanu kawai.
.
.
Sai da suke waya da Ummi can Yamma take faɗa mata.
"Yanzu kin ce masa ba zakiyi ba?" Ummin ta tambaya tana jinjina wauta irin na Reina.
"A'a yace in yi tunani tukunna"
"Ki amsa idan ya tura miki kuɗin ki zo nan, ai maman ku da ta koya ma Fauzee tana da masu taya ta, kuma ma marra ya saka ba sosai ake samun aikin ba yanzu. Za'a yi lissafin yanda za'a yi a siyo kajin ayi aikin shi da komai, za'a yi mishi aiki mai kyau sai ya sake dawowa in sha Allah. Kema sai kiyi ƴar sticker ɗinnan kinga sana'a ta samu miki"
"Allah ma yasa kada ya dawo" tace cikin ƙasa da murya yanda Ummin ba zata ji ba.
......
Yau ɗin ma Yaseer bai tura a kira ta ba, amma tayi tunanin tunda babu inda yaje zata same shi don haka ta ɗibo kayan karatunta ta same shi a yanda suka saba haduwa, ga Aicha zaune a gaban sa.
Tunda suka amsa mata Sallama suka ɗebi shirgin ta suka watsar kuma yau Da faransancin da Aicha kan yi magana wani lokaci idan bata son Reina ta fahimci abinda suke tattaunawa a kai Yaseer kuma yana ganin zata tsargu idan suna sauya harshe a gaban ta yana mayar mata da Hausa ko turanci, toh yau da faransancin yake mayar mata.
Ta san ba zai wuce zancen da ya shafi aiki bane amma sai taji a ranta tana son ta ji abinda suke faɗa. Musamman ma idan suka yi wani maganan Aicha ta ɗago ta kalle ta, sai duk tabi ta tsargu kuwa.
Su kuwa maganan program ɗinnan suke yi Aicha tana complain ɗin ɗaukan alhakin souveniers masu yawa ya bawa Reina da Yaseer yayi bayan suna da masu musu ƙwararru, idan ta ɓata fa?.
Nata French ɗin kuwa ɗan na primary ne da ba maida hankali take yi ba a lokacin, sai yanzu take nadaman rashin iya wani abu bayan su Bonjour.
Babu daɗewa ta miƙe domin karatun bayi shiga, ta kawo mishi yayi mata tambayoyi a kan wanda ta ƙara bayi nan sannan ya sallame ta.
.....
Washegari
4:06pm
Da shirinta ta fito tana raɓa jaka a kafaɗa ta janyo ƙofar su. Sauƙowa ta fara yi ta hango shi yana tsaye yana jiranta a parlo yana ta kallon agogo kaman wanda yake saurin zuwa wani wurin.
Yayi kyau cikin dakakkiyar getzner kalan sararin samaniya da hula wanda ya ɗauki fuskar shi ya dace da kayan tun daga inda take kuwa ƙamshin sa mai kamo hankali ya kwantar da shi luff yake ziyartan hancin ta.
"Yauwa hurry up please, ana jira na" yace lokacin da ya hango ta.
Ƙara sauri tayi amma tana kiyayewa Saboda tsinin takalmin ƙafarta, ta miƙa mishi takardar da biron da isar ta.
Karɓa yayi yana kallon fuskarta da ta sha sauƙaƙƙiyar kwalliya laɓɓen da ta shafawa jan baki ta ɗaura lip oil a kai sai sheƙi yake yi.
mayar da idanun shi yayi kan takardar yana tambayar ta "Ina zaki je?"
"Gidan Ummi" Ta mayar mishi da amsa.
"Ta wurin zan yi, muje in ajiye ki"
Yace yana ajiye takardan a wurin ganin ta saka hannu alamun ta amince kenan, ya san idan wani ya zo ya gani zai ɗaga mishi.
"Okay barin yi Sallama ma Daddy da Umma"
"Ki same ni a mota" yace yana karɓan jakar ta, sai ta sake mishi amma tana tsoron uncle B ya sake kira ya ɗauka, don haka da sauri-sauri ta gama ta fito ta samu ya kunna motar tana diri ita yake jira.
Gidan gaba ta shiga ta jawo ƙofa ta rufe.
Ya miƙo mata wani card yana faɗin "gashi, na saka 1.2m a ciki kada in tura ma ɗan ƙaramin account ɗin ki su rufe. Zan tura miki pin, Idan ana buƙatar wani abu sai ki mun magana, kuma saura ki saka mana ramammun kaji ko ki bamu meat pie mai zallan flour sai kin biya ni kuɗi na"
Saida ta haɗiyi miyau ta iya karɓan card ɗin, ya bata jakarta ta saka a ciki kada ta yar, tukunna suka ɗauki hanya.
Ta ja bakin ta tayi shiru ganin wulaƙancin da yayi mata jiya shi da darling ɗin shi amma sai jiyo shi tayi yana tambayar ta.
"Reina nayi kyau?"
Ta tsaya kallon shi sai ya fara gyara zaman wuyan riga da Hula. "Wurin babe ɗina zani tana ta complain bata saka ni a idanunta ba kwana biyu"