← Book details Reina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 117

Sashe 107

Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yeah, cousin ɗina ne. Ɗan Aunty Zuwairah dake Abuja, and bayi da mutunci ko kaɗan, as far as I could remember ma ɗan giya ne, don a sanadin an saka ni sharan ɗakin shi na fito da kwalban ban san ta mecece bane ya kama ni yayi min ɗan banzan duka har yayi ball dani na bugu a jikin handle ɗin drawer naji ciwo a nan." Ta ƙarasa tana juya baya tare da ɗaga ƙasan rigan ta dake iya guiwa ta gwada mishi wani tabo a bayan cinyar ta.

Numfashi ya furzar ya ja rigan ya sauƙe mata sannan ya riƙo hannunta ta zauna a kujeran dake gefen nashi ya juya mata screen ɗin MacBook ɗin yana matsar da résumé ɗin zuwa wanda yake na gaba kana ya tambaye ta "Wannan fah?"

"Brother ɗin shi ne" ta amsa.

Ya ƙara wucewa zuwa na gaba yana tambayan ta again. Sai ta kalle shi cike da damuwa.
"Idan baki faɗa min ba ma na bincika zan gano. Daman abun yayi mun wani iri domin ba irin mutanen da muke buƙata ba kenan, muna buƙatar real talent ne aikin mu ba na daƙiƙai bane kuma bamu ɗaukan alfarma, amma ba zan iya musawa Rafeeq ba tunda shi ya roƙa, yace shima bai san inda zai saka su bane saboda ta ƙafar Auntyn shi suka biyo, shiyasa ya nemi in maƙala su a project ɗin da zamu yi tare tunda zai ɗauki shekaru kafin a gama."

Sauƙe nannauyan ajiyan zuciya tayi sannan ta mayar da duban ta kan fuskar Haydar dake kan screen ɗin tace "ɗan Umman Jamal ne wannan, shima cousin ɗina ne"

Ya wuce zuwa na ƙarshe "wannan fa?"

"Ɗan Hajiya Addah ne amma da gaske shi babu ruwan shi."

"Iyayen shi sun jawo mishi" yace yana dawo da fuskar MacBook ɗin gare shi ya buga musu reject dukkan su sannan ya ɗaga waya ya kira Rafeeq.

......

*Abuja, Nigeria*

*Rafeeq*

Knocking ɗaya.. biyu.. yayi yana bada tazara a tsakanin su, idan yayi na uku bata buɗe ba kuma sai ya buɗe ƙofar ya shiga ciki.

Ya ɗaga hannu zai yi na ukun aka murɗa hannun ƙofan ta ciki tare da jan shi ya bude, sai ya matsa daga jiki don ya bata hanyar fitowa.

Idanunta ne suka shiga cikin nashi tun bayan daren jiya da ta gama shan kukanta har barci ya ɗauke ta, ya dauke ta ya kai ɗakin ya kwantar ya fito.

Tayi wani plain haka, fuskar ta kaman ba nata ba. Sai ya fahimci abinda ta saba ado ma fuskarta ne babu shi a yanzu. ba wai muni ne ya bayyana a fuskar ta komin kashin sa ba, amma ta kasance mace ce ma'abociyar tozali da eyeliner, ko da ba zata shafa komai a fuskar ta ba amma zata yi ado ma idanunta don ya ƙara mata kwarjini. Saidai yau idanun da farin su suke kallon cikin nashi, yanda Allah ya halitta mata su.

"Bonjour Mon amour" ya gaida ta.

"Bonjour mon mari" ta mayar mishi da gaisuwan cikin dasasshiyar murya tana ɗaga idanunta daga cikin nashi.

Murmushi yayi jin ta kira shi da mijinta. "How was your night" yace yana riƙo hannunta zuwa cikin parlon ita kuma tabi hannun da kallo tana mamakin wai halalinta ne ya riƙe ta, babu zunubi a cikin haka saidai akasin shi.

Suna cikin tafiya ya juyo ya dube ta. "Care for a cup of coffee? Baki yi kama da wanda kika samu isasshen barci ba Gaskiya" yace hannun shi na kaiwa kanta dake cikin ɗankwalin dogon rigan material da ta saka don yau babu ɗaurin Fatima balle Zahra.

Gyaɗa kai tayi ta sake ƙoƙarin motsa bakinta ta samu ya furta "Yes Please".
sai bai tsayar da ita a parlorn ba ya wuce da ita kitchen ya sama mata wurin zama kana ya ƙarasa jikin coffee machine da mugs guda biyu a hannun shi ɗaya baƙi ɗaya fari, ita dai bin duk motsin shi da ido take yi, tana ƙoƙarin shigar ma ƙwaƙwalwa da zuciyar ta cewa zahirinta kenan a yanzu.

Ya kawo farin mug ɗin ya ajiye a gabanta cikin kulawa sannan ya sama wa kan shi matsuguni suna fuskantar juna.
Ta ɗauki mug ɗin ta kai bakinta domin bata san mai zata ce mishi ba tukun.

Har saida suka ɗauki mintuna kaman goma haka sannan ya fara magana. "Darling I'm so sorry." idanunta a kan shi yaci gaba da cewa. "Ban yi tsammanin zan same ki ba shiyasa ban bayyana miki ni wanene da wuri ba, a lokacin da na same ki kuma tsoron rasa ki ya saka na cigaba da ɓoye miki kaina. Ana ɗaura mana aure na wuce Bauchi jin labarin rashin lafiyar ki, Kusan kullum ina zuwa duba ki a asibiti amma lokacin baki son ganin fuskar kowa ballantana ki amsa gaisuwan mai ita. Ban dawo ba saida na tabbatar kin warware, amma haɗuwata da ke a nan ƙaddara ce kawai, ba ni na shirya Yaseer yazo min da ke ba, saboda bani haɗa hidiman business da family, Musamman ma wanda ya ƙunshi maƙudan kuɗaɗen da bani kaɗai nake da hakkin su ba. Nayi niyyan janye investment ɗinmu daga YK & Co da gaske saboda wannan matsala da ta taso, ita duniyar kasuwanci babu ruwanta da yaseer yana da gaskiya ko bayi da shi. Amma saboda ke Aicha, Saboda ke a karo na farko na yarda da abinda bani da tabbaci a kai, saboda ba zaki iya roƙa nace miki A'a ba. Saboda kin fi ƙarfin dukiya a wuri na."

Kallon shi kawai take yi da mamaki har ya dasa aya domin kaman Rafeeq ɗin dake tare da ita jiya-jiyan nan ba shi bane wannan, Idan shine to hala ya haɗiyi aku.

"Kice wani abu Amour" ya murmusa sanin cewa mamakin shi take yi har da kai hannun shi kan nata dake riƙe da hannun mug.
Sai ta sake bin hannun da kallo sannan ta ɗago ta dube shi, sai ta buɗe baki kaman zata yi magana tabi ta rufe, ta sake buɗewa ta rufe again, ta rasa da me zata fara.

Ya ɗan matsa hannun nata "say something please, ki tambaye ni ko menene zan amsa miki da iyakar gaskiya ta."

"A.. a ina ka san ni ka san mahaifi na? Ko a Niamey? Ko wani ne ya gwada maka ni?"

Ya girgiza kai. "Ba a Niger na fara sanin ki ba, ba a Nigeria ba, kuma ba a wurin wani ko wata ba"

Ta ɗan yamutsa fuska cikin rashin fahimta tace "toh a ina?"

"The pearl convention center, Doha, Qatar. Shekaru biyar da suka wuce a 'Aurelia Global Summit' da ake yi duk shekara a watan Nuwamba, a shekaran an yi taron ne a kan innovation da Human Impact. Yaseer yana cikin guest speakers, a gefen matsugunin shi kuma na hango fuskar da ta ɗau shekaru daga wannan rana tana min yawo a ka.......

107

Dakatawa yayi yana kallon yanda ta waro ido tana mishi kallon mamaki, ba don ya mata dalla-dalla ba ita tama manta abinda ya faru ko kuma kasancewar su a wurin a ranar.

Ya ɗora gaskiyar kalaman sa a kan yanayin fuskar shi yana mai cigaba da faɗin "A lokacin mamakin kasancewar ki a wurin nake yi saboda ƙarancin shekarun ki, I think you're the youngest person there don daga gani ba zaki wuce 17-18 ba, ina da tabbacin ko kin gama secondary ba da daɗewa ba. Kuma ba don hankalin ki da nutsuwar ki gaba ɗaya yana kan abinda ake gabatarwa wanda nake mamakin amfanin da zai yi ma ƙaramar yarinya irin ki ba wataƙil da kin kama ni ina kallon ki."

Ɗan gyara zama tayi tana mayar da idanunta cikin mug ɗin gabanta tunawa da dalilin da ya saka ta kasance a wurin ta bayar da nutsuwar ta ga abinda ake gabatarwa saboda ta tsinci abinda zai jawo nutsuwar dalilinta na zuwa wurin gare ta. Dalilin da yanzu yayi mata nisa har abada.

"Shekaru biyu bayan nan sai gaki da mahaifin ki a naɗin sabon Sarkin damagaram, da na ɗaura idanu na a kan ki a lokacin sai naga kaman jiya muka rabu saboda hoton fuskar ki yana danƙare a zuciyata kuma ban san dalili ba, domin nayi imani babu wata mace a gaba na a lokacin. Shekaru uku da rabi kenan da na rasa mahaifiyar Najma, kuma masu haɗawa sun buga sun gaji domin ba uwar riƙo ko mai reno nake nimawa ƴata ba, don ko bani raye zata samu gata a cikin Estate fiye da masu iyaye a raye. Abokiyar rayuwa nake nima, macen da idan na kalleta zan ji ta isheni duniya da abinda ke cikinta"
Ya sauƙe numfashi ya zare hannunta daga jikin hannun mug ɗin ya riƙe a cikin nashi yana shafa bayan hannunta da babban yatsar shi. "Ban ji hakan a kan kowa ba saida na ɗaura Idanu na a kan ki Darling. ban yi ƙasa a guiwa ba na samu mahaifin ki a ranan, abin dariya ko sunan ki ban sani ba sai a lokacin, amma sai haƙuri ya bani, babu ƙwaƙƙwaran dalili kuma, ya barni da kokwanton ko girma nayi miki, ko dan na taɓa aure ko kuma akwai wanda kike so, dole cikin su za'a samu ɗaya tunda ya san iyaye na, sun daɗe suna kasuwanci da mahaifi na kafin Allah ya ɗauki ran shi, ni kuma bai kai ga bincike a kaina ba ya dakatar da ni balle ince aibu na ya gani, sai na haƙura. Ba dake ba da auren baki ɗaya sai na haƙura, saboda a gani na duk wacce zan aura idan ba zan iya bata kulawa da dukkan zuciya ta ba na cuce ta. kuma naga riban haƙuri domin shi ya mallaka min ke bayan tsawon lokaci, ban cire rai ba, ban daina addu'ar alkhairi ba har Allah ya tabbatar min da ke a matsayin tawa a lokacin da ban yi tsammani ba"

"Shine ka hau doki zaka karya ƙafa gaka sabon ango" tace da sautin dariya tana share hawayen da ya biyo idonta ɗaya da ɗayan hannunta.
Chapter 107 · 0% Book details