Sashe 37
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amma bayan koran wulaƙanci har akwai wanda suka yi yunƙurin sake tara masa gajiya.
....
Zaune yake a study room ɗin shi ya ƙura ma takardan da mutanen ɗazu suka bashi idanu, ga kuɗin da yake buƙata nan a rubuce a jiki kuma sa hannun shi kawai zai mallaka mishi su yayi masa maganin damuwar da yake ciki.
Tun ba'a kwana ba har Alhaji Tahir ya fara tunanin ko dai ya karɓi kuɗin nan ne ya biya bashin kamfani idan ya so a hankali sai yayi ƙoƙarin biyan wa'innan mutanen kafin kuɗin ruwan ya taru da yawa daga baya sai ya roƙi Allah yafiya har Umrah ma sai yaje yayi ta istigfari tunda Allahu gafurur raheem ne.
Waya ya ɗaga ya kira Alhaji Salisu. Sai da yayi kusan tsinkewa kafin ya ɗaga saɓanin da da kaman jiran kiran nashi yake yi.
Bayan yayi mishi sallama yace "Amma yaya Salisu a maimakon wannan me zai hana ku da su yaya kalabu da su Hajiya Addah ko dukkanku ku haɗu ku bani aron kuɗin nan sai in siyar da wasu kadarori na in cika? Kun san dai kafin wani lokaci zan haɗa na baku har da ihisani a kai ma"
"Idan ka tunkare su da zancen sun amince ma fi mushkila amma ni na faɗa maka abinda zan iya bayarwa shima nayi maka ƙoƙari saboda nima an ci nawa kuɗin abun da yake hannuna babu yawa a yanzu"
"Amma ba kai ka haɗa ni da mutanen nan ba Yaya Salisu?"
A ɗan hasale yace "Da na haɗa ka dasu nace ka shiga dole ko nazo na kama hannun ka?"
"Abinda zaka ce mun kenan? Amma waye ne ya zo ya dinga kawo mun shaidun ƙarya na tabbatar da sahihancin abun iye?"
"Jariri ne kai da baka da wayon da zaka yi bincike da kanka ko me?"
Haka suka dinga musanyar yawu kowa na ƙoƙarin ganin ya ɗaga rawanin laifi daga kan shi ya naɗa ma ɗan uwan shi.
Faɗowa dakin Reina tayi hawaye na bin Idanun ta "Daddy.... Daddy Wallahi ba yaya Yaseer bane, ƙarya nayi Daddy... Yaya Jamal ne wallahi, shi yake kira na ɗakin shi ya rufe ƙofa yayi ta taɓa ni, don Allah kace su sake yaya Yaseer ba shi bane."
Sauƙe wayar Alhaji Tahir yayi daga kunnen shi ba tare da ya katse ba. lokacin kira na ƙirga mintuna Arba'in da ɗaya da sakwannin dake kan gudu.
Shiruuu yayi, haka ma Alhaji Salisu dake da tabbacin duk tashin hankalin da Alhaji Tahir ya shiga a lokacin shi ya shiga dubun sa. Sai Reina dake karanto mishi duk abinda ya faru tsakaninta da Jamal ɗaya bayan ɗaya, bata manta ko ɗaya daga ciki ba domin memories ɗin sunyi ma karamin ƙwaƙwalwar ta girman da zata iya goge su.
Alhaji Tahir ya gagara motsawa ko nan da can, kaman wanda aka saka super glue aka manna da kujeran, sai hawayen dake bin fuskar sa.
"Tahir, Tahir, zan san yanda zan yi in dawo maka da kuɗin nan nayi alƙawari, idan suka shiga hannun ka sai kayi min duk yadda kaso Amma yanzu wani abu na faruwa ba zasu dawo mana dashi ba, zaka rasa TK Kingdom, zaka rasa Hafsatu da Zainab. Zaka ɓata goma ne ɗaya bai gyaru ba Tahir, koda ka rufe Jamal Amma kaima ba zaka tsira ba"
Kururuwa ya saka ya miƙe yayi firo da wayan sai da ta haɗu da bangon ƙarshen ɗakin sannan ta rabu biyu ta zuba a wurin.
Ya duɓi Reina da ta koma jikin garu a tsorace domin ta sani ita ce next ɗin duka, yau a karo na farko daddynta zai ɗaura Hannu a jikin ta Amma a shirye take idan zata tseratar da yaya Yaseer.
Domin Bata fahimci cewa tayi kuskure ba har sai da ɗazu suka je dubo Maama ita da uban a gidan Ummi tana zazzaɓi.
Duk rashin jituwar su Reina sai da ta tausaya mata ganin yanda take a wahalce, a nan ne bayan Alhaji Tahir ya tafi ya barta a gidan take tambayar Ummi ko itama Maama mutuwa zata yi, ko an faɗa mata abinda ba'a faɗa ne yasa take ciwo zata mutu?.
Ummi ta ɗau tausayi ne na ƴan uwantaka da kuma basu daɗe da rashin mahaifiya ba yasa tayi mata bayanin mutuwa da kyau yanda mai shekarun ta zai fahimta.
Baka mutuwa don an faɗa maka wani abu kuma baka mutuwa sai lokacin da Allah yaga dama.
Hakan na nufin Umman Jamal ƙarya take yi? Hakan na nufin abinda ta faɗa ma yaya Yaseer umman Jamal tace ya faɗa ma Auntyn ta ba shi yasa Auntyn ta mutu ba? Hakan na nufin ƙaryar da tayi ba shi ya ceci yaya Yaseer ba?.
"Ummi dan Allah kira min Daddy na a waya yanzu" ta buƙata hawaye na cika idanun ta da sauƙowa a lokaci guda, ga yanda ta fara rawan matsuwa kaman mai jin fitsari.
Tambayar ta abinda yake faruwa Ummi tayi amma sai girgiza mata kai take yi tana kukan a kira mata daddyn ta.
Suna haka Aina'u tayi Sallama ta shigo gidan. Alhaji Tahir ne ya turo ta da driver su dauko ta domin a yanzu ko driver ɗin da yayi shekara da shekaru yana masa aiki bai yarda da shi ba a kan Reina, bai yarda da kowa ba ma a kanta bayan kan shi.
Tun a hanya take kuka har suka Isa gida, ko parking ba'a gama ba ta ɓalle marfin motan ta fita da gudu har tana niman kifawa.
Bata tsaya ko ina ba, sai study room ɗin Alhaji Tahir. Shine aka yi wannan arangamar.
Haka Alhaji Tahir ya koma ya zauna ya riƙe kan shi yana kuka kaman ƙaramin yaro, kuka yake yi tun yana zaune a kujera har sai da ya zuba a ƙasa.
Ta ƙaraso da gudu ta rungume shi suna kukan a tare babu mai rarrashin wani, har sai da yaji tana shiɗewa ya ɗibeta ruwa-ruwa suka yi asibiti.
basu sake ɗago da maganan ba har sai da ta warke garau, yayi amfani da lokacin wurin tunani a kan matakin da ya kamata ya ɗauka, daga ƙarshe dai ya yanke zai rufawa Alhaji Salisu da Jamal asiri na wani lokaci kaman yanda ya buƙata, shikuma Yaseer koda ya shiga prison a yanzu daga baya sai a wanke shi a fito dashi ya tallafi rayuwar yaron. Da kuɗi babu abinda ba zai yiwu ba amma idan babu kuɗi shima ba zai tsira ba kaman yanda Alhaji Salisu ya faɗa.
Yanda aka yi kenan Mahaifin Reina ya rufe bakin ta na tsawon shekara ɗaya.. biyu... Uku.. Alhali a maimakon lokaci ya warkar da ciwon dake ƙwaƙwalwar ta sai Trauma ya samu wurin zama yana ƙara girma.
A lokacin da take da shekaru 12, Rayuwa ta ƙara musu baibai, Saboda kula da Reina Alhaji Tahir yayi aure fiye da biyu a tsawon lokacin amma saboda itan ba'a ɗaukan tsawon lokaci yake sakin su, domin babu wanda yake iyawa da halinta, kuma duk wanda yayi ƙoƙarin mata gyara nan zai buga miki red card, a dalilin haka har gidan Ummi ya daina kaita, su ƙarata da Maaman da suke so.
A ɓangaren dukiya kuma fafutuka bata ƙare ba, Alhaji Tahir ya samu ya tseratar da shares ɗin shi na TK Kingdom da kuɗin ruwan nan da yaƙi daga farko amma gashi har kuɗi tana niman ruɓa kanta saboda lokacin da ya ɗauka zai biya su ya daɗe da wucewa har ana niman shekara biyu, riba(Interest) kuma sai ƙaruwa take yi da kowani wucewan rana.
Yanzu damuwan da yake a gaban shi kenan har ya manta da zancen wani wai Yaseer, bala'in da yake ciki ya ruɓa na Yaseer sau ba adadi a ganin shi.
...
Shigowa tayi gidan tayi kaca-kaca, farin rigan uniform ɗin an jiƙa shi da orange juice da ketchup ga neck tie ɗin wuyan ta kaɗan ya rage ya gama warwarewa, gefen bakin ta a fashe gashin kanta kamon sabon shiga hauka Barrett ɗin ma bata san ina ta baro shi ba.
"Sarauniyata" Alhaji Tahir ya taro ta, bai ma lura da Maama da ta biyo bayan ta riƙe da jakunkunan su ba.
"Waye ya taɓa ki?" Ya tambaya cikin fushi yana dudduba jikin ta.
Da Maama kaman ba zata ce komai ba kafin murya a sanyaye tace "faɗa suka yi"
"Faɗa! Da ƴar gidan uban wa?!"
"Ta daki wata yarinya ne a class ɗin su wai sunanta Safina, shine ƴan class ɗin suka haɗu suka yi mata duka"
A maimakon ya hau sababi kaman yanda ya saba sai ya riƙo hannunta cike da damuwa "Allah yasa ba Safina Abdulhakim kika taɓa ba"
Mahaifin Safina tsohon ma'aikacin Tk Kingdom ne, kusan da shi ma aka kafa kamfanin, ga aiki tuƙuru da riƙon amana, hakan ya sama masa position cikin board members na kamfanin saboda shima ya mallaki wasu shares duk da ba mai yawa bane amma Alhaji Tahir support yake nima ta ko ina domin wasu nima suke yi a tumɓuke shi daga matsayin shi kafin ya janyo musu asarar tasu dukiyar suma.
Matsayin Alhaji Tahir ɗin a da ya saka duk yanda Reina zata tafki ƴar shi da su ƙwace mata abinci da take yi bayi taɓa cewa komai Amma yanzu reshe ya juye da mujiya.
Maama ta amsa da "Ita ce"
Reina ta ɗago ta watsa mata harara tayi saurin kawar da kanta cike da tsoro.
"Ba na hana ki taɓa ta ba sarauniya? Kina so kiga ƙarshe na ne?"
Maganar da yayi na ƙarshen cikin hausa yayita Amma sai ta zamo a bakin Mala'iku, Domin fitan da yayi bayan nan ne sai gawar shi aka dawo da ita gidan cikin jini yayi hatsarin mota.
Kafin lulluɓewar dare labarin mutuwar shi ya zaga ciki da wajen Nigeria, Kamal da ya shigo gari duba Yaseer a ranar, goggo Halime ta kira shi ta wajabta mishi zuwa ya sallaci gawar Alhaji Tahir.