Sashe 64
Reina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yaseer bai daɗe da ajiye wayan Reina bayan ya gama shan masifan Umma ba Abbah ma ya kira shi ta nashi wayan ya ƙara mishi harda bashi lokaci yayi ya dawo kuma ya kawo musu Hafsatu lafiya idan ba haka ba ran shi ya ɓaci.
Zai iya cewa ikon Allah ne kawai ya kawo su cikin gidan kuma yana tsayar da motar ya ɓalle marfin ta ya fice ba tare da ya tsaya rufewa ba. Reina tayi saurin mara masa baya har tana haɗawa da gudu a kan takalmin ta mai tsini.
Suna shiga main parlo Umma ta hayayyaƙo masa kaman zata ɗauke shi da mari ganin Reinan lafiya ƙalau dai ya saka ta yayyafa ma zuciyan ta ruwan sanyi. Daɗin abun ma ɗaya Alhaji Tahir ya tafi ganin likita kuma zai iya kwana a can don sai result ɗin tests masu muhimmanci sun fito kafin su sake shi ya dawo gida, Amma da basu san da wani ido zasu kalle shi ba.
Umma ta zauna tana mayar da ajiyan zuciya tare da hararan Yaseer, ita ta hana a kira shi a sanar da shi saboda kada a ɗaga mishi hankali ashe shine ya tada musu da nasu.
Abbah ya zaunar da su bayan ya sake yiwa Irfan faɗa an kora shi ciki. Itama Reina ta ɗauka faɗan za'ayi musu tare amma sai aka yiwa Yaseer kawai kanshi a kasa yana bada hakuri ita kuwa tana ta faman ƙifi-ƙifi da idanu.
"In sha Allah ba za'a kuma ba Abbah, ku yi haƙuri"
"Ai babu ma maganan kumawa gwara ayi wa tufkan hanci tun yanzu" ya amsa shi Sannan ya dubi Reina.
"Hajiya Hafsah zan iya sanin a cikin maneman naki biyu Bilal da Yaseer wanne kika tsayar?"
Yaseer kuma?!! Tayi saurin dagowa a firgice ta dubi Yaseer dake zaune opposite da ita a can ƙarshen carpet din. Shima ita yake kallo ga wani saƙo a cikin idanun shi mai wuyar fassarawa.
Sai ta kalli Abbah da Ummah kafin ta sake sunne kai ƙirjin ta na lugude. Yaushe aka ga suna soyayya da yaya Yaseer da har za'a saka shi a sahun maneman ta?.
"Hafsatu babu takurawa babu tursasawa, idan kika yi haka ma kin cutar da mu ne matsayin iyayen ki masu son farin cikin ki. Ki faɗa mana ra'ayin ki kuma in sha Allah idan mun duba babu wata matsala zamu baki abinda kike so."
Sai ta sake duban yaya Yaseer da bakin shi yake motsin furta wani abu amma ta gagara gane menene sai da ta ɗan ƙura masa ido tukunna.
'Please!' shine abinda yake ambata ba sauti.
"Uncle Bilal...."
~~~~~~
Wannan littafin na kuɗi ne, mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan number 08021689184.
*Seemahwrites ✨*
87
~~~~~~~~~~
_pendant ce temp, le temps passe_
_(During this time, time went on)_
_Et je subis tes balivernes_
_(and I endured your Nonesense)_
~~~~~~~~~~
*Reina*
Idan ka samu kanka a can saman wani tsauni ka ƙure karshen ta babu sauran daman gudu sannan bayan ka mayunwacin damisa ne yake tunkaro ka wani kalan mutuwa zaka zaɓa? Wanda zaka faɗo daga saman tsaunin nan kayi raga-raga ko wanda zaka tsaya damisan nan ya cimmaka yayi yaga-yaga da naman jikin ka? Domin babu sauran fata na rayuwa kuma.
Toh idan za'a tambaye ta a irin yanayin da ta samu kanta a yanzu bayanin da kawai zata yi a fahimce ta kenan.
Saboda kafin ma aje ga ra'ayin ta... wai yaya Yaseer son ta yake? Tun yaushe? Yaya Yaseer ɗin da suka yi wa tabo a rayuwa amma ƙaddara ta sake haɗa su wuri guda?!
Yaya Yaseer ɗin da Hafsatu da kanta ta sani a yanzu yafi ƙarfin ta!.
Toh ko auren haɗi ake son ayi musu? Ko tausayin ta da yake ji ya saka zai aure ta don ya rufa mata asiri?
Ta sake duban shi da ƙoƙarin ta fassara abinda ta gani a idanun shi. Yana da alaƙa da abinda take gani kwanan nan a duk lokacin da ya dubeta? Ta shiga taryo hirar su na kwanakin nan, ya sha bamban sosai da wanda suka saba da kuma wanda yake yi da kowa harda darling da tazo ta same su a tare kuwa. Hirar su yana saka ta jin wani daɗi har kan harshen ta, tana jin kaman ta bar cikin duniyar mutane ta koma nasu duniyar su biyu don haka take sakewa da shi sosai.
A hankali bakin shi yake motsin furta wani abu amma ta gagara gane menene sai da ta ɗan ƙura masa ido tukunna.

Please ta zaɓe shi? Ko please tace ba shi ba?.
Toh Uncle B fah? Idan ta rabu da shi me zai ce? Da wani ido zai kalli abun idan ta zaɓi Yaseer a kan shi, bayan alƙawuran da ta riga ta ɗauka mishi ta saka ya sakankance kan cewa ita tashi ce?. Ba zata iya da tuhumar shi ba Allah ya gani, auren shi kawai shine zaman lafiyan ta.
"Uncle Bilal...." Bakin ta ya fara furtawa Yaseer ya rintse idanun shi domin ya san za'a yi haka dama, ko bayyana mata nufin sa a kanta bai samu yayi ba ta ina zata zaɓe shi?.
"Bilal kika ce?" Abbah ya tambaya domin ya tabbatar shi ɗin ta zaɓa har ƙasan ranta.
Idan ta zaɓi Uncle Bilal kenan ta bari ma su Darling da su Abidah yaya Yaseer bayan shi ita ya zaɓa?.
Ta buɗe baki zata yi magana Saudat tayi saurin cewa "kaman bata ce komai ba ko?" Ta kalli Reina tana girgiza mata kai a kaikaice. Idan har ta tabbatar da ɗaya a cikin su toh fa magana ta zauna kenan, kuma ina aibun ɗanta Yaseer da har za'a ce bata zaɓe shi ba?!.
Abbah ya share zancen Umma ya sake tambayar "Bilal kika ce ko?"
Sai ta girgiza kai. Ba zai ambaci sunan Yaseer ba don ya san amsawa zata yi koda ba a son ranta ba sai yace "shikkenan je ki huta Allah ya tashe mu Lafiya"
Ƙafafuwan ta da taji sun dawo mata kaman lilo tayi ƙoƙarin tsayarwa a kan ƙasa amma koƙarin zubewa take yi saida Umma tayi saurin miƙewa ta riƙe ta, sannan suka taka a tare har sama kana Abba ya juyo ya dubi Yaseer.
"Sati biyu na baka, ko ita ko wata kayi ka bar gidan nan, don ba zaku zauna kuci gaba da mun shashanci a gida ina zuba muku ido ba, ba zan lamunta ba" da haka Abbah ya sallame shi, shima Yaseer ɗin ya miƙe bayan ya sake bada haƙuri ya nufi nashi ɗakin. Samm ba a haka yaso Reina ta san da sirrin zuciyar shi ba, ya so kalaman su fito daga bakin shi suyi tsalle su shige kunnen ta a lokacin da ya tabbatar da ya buɗe musu hanyar da zasu samu matsuguni a nata zuciyar.
.
.
.
"Ki shiga kiyi wanka sai ki kwanta zaki fi jin daɗi" Saudat tace tana ƙarasawa jikin wardrobe ta tura ƙofar zuwa ɓangare daya tana nimo mata kayan barci.
Ɗaga kai Reina tayi jiki ba ƙwari ta fara jan ƙafa sai umma ta bar abinda take yi ta kirata ta juyo.
"Na taɓa cewa Fauziyya ina da burin Allah ya azurta ne da ƴa mace amma ban samu ba tukunna.Tace mun Umman Yaseer ga Reina nan na baki itama ƴar ki ce, idan ta samu uwa irin ki hankali na zai kwanta saboda na san zaki mata komai. Toh In sha Allah ba zan rufe ido rayuwar ki ya shiga garari ba, na yarda da ƙaddara na haƙura daga wannan lokacin kuma na manta, ni ba Umman Yaseer bane zallah, ni Umman Yaseer da hafsat ne idan kina da damuwa ko wani iri ne ƙofa na a buɗe yake kin ji?" Sai a lokacin ta samu hawaye ya ɓalle mata, ta tsuguna a kofar ɓanɗakin tana niman haɗa kai da cinya Saudat ta ƙaraso ta ɗaga ta ta kaita bakin gado suka zauna sannan ta shiga share mata hawaye sai jin Reina tayi ta shiga jikinta ta rungume ta tana sakin kukan da yafi na da karfi.
Cikin rasa abin yi Saudat ta shiga buga bayan ta a hankali, bata sake cewa komai ba har kukan Reina ya ragu sannan ta dago ta tana sake share mata hawaye. "Auntyn ki bata yi ƙarya ba da tace kina da kukan banza"
Sai tayi dariya mai sauti tana share fuskarta da daidaita kanta.
Ƙoƙarin basar da yanayin itama Umma tayi ta hanyar tambayar "Kina jin yunwa?"
Gyaɗa kai tayi don tashin hankali ya ƙwaƙwule abinda taci.
"Okay kiyi wankan kafin nan na kawo miki abinci"
"Toh Umma, Nagode." Tace tana wucewa bathroom ɗin da ƙwarin guiwan fuskantar abinda ke gabanta a yanzu tunda ta samu bangon dafawa.
Bayan ta fito ta sauya kaya Umma ta tsaya a kanta taci Abinda ta kawo sannan ta ajiye mata jakar ta da aka dauko daga motan Yaseer ta fita.
ita kuma ta koma ta wanko bakinta ta dawo sannan ta ciro wayan da har yanzu yana Do not disturb.
Ga ƙarin missed calls din uncle B guda uku a kan biyar ɗin farko amma saƙon da ya haɗo tare da su ya saka taji ba zata bi kiran ba don bata cikin yanayin da zata iya sauraron mitan shi. Ta ja tsaki a fili "haba mutum bai san yin uzuri ba ko kaɗan? Yanzu da wani abun ne ya same ni fah?"
Ita kaɗanta take fama, ta danna numbern Safina wanda ita kira ɗaya kawai ta ƙara mata bayan ta samu labarin an gano inda Reinan take daga wurin mahaifinta.
"... Allah sarki ina babu Abinda ya same ki?" Safinan ta tambaya bayan da ta haɗa su da mummynta da kanwar ta aunty Mamy mai jego suka gaisa don kowa ya damu banda ma Safina da tayi ta kuka a tunanin ta ko a hanyar komawa daga gidan su ne aka sace ta tunda bata san tare da Yaseer suke ba.
"Babu komai fah. Jama'are muka je da yaya Yaseer"
"Yaya Yaseer dai? Shine babu wanda ya sani?"
"Ba wannan ba Feenah kina cikin nutane ne? If yes ki koma gefe don Allah muyi magana"