← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 269

Sashe 99

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarfe bakwai na safe Doctor Hamza yayi wa mahaifin su Sallama bayan doguwar hirar da suka yi tun bayan sallar asubah ,  duk wata nasiha da yakamata tare da tunasarwa sai da yayi masa ,

A ƙarshe da ya miƙe zai tafi ya bishi da addu'o'in tsari da fatan samun nasara suka yi sallama , ya shiga motar sa yana barin gidan ɗauke da niyyar biyawa yayi sallama da Amne kafin ya ɗau hanya !

Ƙarfe tara ta sami colonel Youssouf  tare da colonel Tafeedah a babbar headquarter na soji da ke garin ,"Giwa barrack ,"  inda bayan ƴar gutuwar mahawar tare da gabatarwa aka haɗa su da gungun sojoji kimanin su goma sha biyu akan su raka su , a je a kwaso mutanen da colonel Youssouf yace sun ɓoye masa ƙanwar sa ,"

Hilux biyu ta soji É—auke da bindigogin su suka yiwa unguwar su madam saly tsinke ,.

   Tunda suka doso unguwar matasa da ma wasu daga cikin magidantan da  suke da tsoffin laifuka suka fara guje-guje , kasancewar unguwar kusan cike take da marasa ji ƙananu da manyan masu laifuka sai kawai aka hargitse da guje-guje , saboda sun san haka tsigau gungun sojoji basu kauce hanya su gangaro musu cikin unguwa ba shakka wani ne yayi wata ta'asar aka zo yin ram da shi ,

Basu kula kowa ba suka bi hanya ƙarƙashin jagoranci Conole Youssouf da yake hakimce gaban motar farko .

Tun daga nesa madam saly da ÆŠan liti da suke zaune daga cikin rumfa kan kujeru suna jajantawa juna game da asarar maÉ—uÉ—ai da suke jajen sun same su , suka fara jiyo jiniyar motar sojoji ,"
    Gefe guda kuma ma'aikatan tane baki ɗaya kowa na aikin sa , masu goge-goge da share-share na yi , ta ciki kuma masu wanke-wanke da haɗa ruwan barasar nayi .

    Ɗan liti da ke karkaɗa ƙafa yana tsuma yace
   Hmm ai ke dai saly fara bar tuna min ,"cin kazar daren farko ," ban son ko tunawa da yadda waɗannan magudan kuɗaɗen da Bala manci yayi mana ta leƙo ta koma da su , ai ƙwaranƙwasa da mun kama su da mun tsalleke kogin talauci , naira dubu ɗari tara fa saly fara ?  Kuma ke a ganin ki da mun biya masa buƙatar sa ba zai cikace mana ya zama miliyan bane ??

   Kai dai bari liti wallahi ni sai yanzu nake jin takaicin gudun tsinannun yaran nan ƴan gudun hijira yaks da ƙanwar ta , ka ga wannan ƴar luɓu-luɓun ƙanwar tata ai ita ce irin wacce Bala ya nemi da mu kai masa , ƴar ƙwailar da take gaf da balallagewa , "

  Uhun ni na tabbatar ke ce mai baƙar ƙafa saly dan duk wata harka indai ta kuɗi ce idan na haɗo da ke ban ganin falala a cikin ta , ƙwaranƙwasa da na sani da juwai me kala-kala na kaiwa harkar nan da yanzu tuntuni kuɗaɗe na sun nuna sun yi ligif a hannu na ,"dan nasan ko ramin kura ta shiga ta nemo irin wacce bala ya nema ,"

   Wani kallon sheƙeƙe madam saly ta jefawa ɗan liti ,
   Lalle kuwa liti , yo yaushe daren yayi nasa tuwo a ido ?? To idan ka fasa kaiwa juwai me kala kala harkar ka ta samun kuɗi nan gaba kai ba ɗan halak bane liti muna nan da kai zaka dawo da ƙafafun ka ni ɗuwawu ce dole a zauna da ni ,

  Rama kallon banzan yayi ya murza yatsu,"suka bada sautin ," ɓas
    Ni ce ma ke saly fara , nace ni ce ke , gaba asara baya asara ai wallahi , ki ji ni da kyau idan ido ya mutu kwalli bai tada shi , ke da kan ki dai kin san kome yanzu ba irin na da ba ne , anbar yayin 504 Yanzu 406 ce ke kada maza ahaayye ji min saly fara zata gwadan salon su na tsofin bariki ??
 
   Ta buɗe baki da nufin maida masa martani suka ga ƙartin mazan da ke karta ta waje suna shigowa da gudu suna tsalleke katangar da take ta ƙarshen filin gidan, miƙewa su duka biyu suka yi , dai-dai da shigowar wani gabjejen ɗan busa hayaƙin da ya sha yayi manƙas da gudun ma da ƙyar yake wondan sa a hannu ,

   kai idi meye ya faru na gudu ? Inji madam saly

   Ta wajena ki arce kiyi ta kan ki idan ba gungun rundunar sojojin Nigeria kaf ne suke shigowa gidan nan ba ," 

Mts É—an liti ya jaa tsaki yana komawa ya zauna ,
   Zauna muyi hirar mu saly fara yanzu haka wannan na maliyan sha yayi tafi ƙarfin ƙwanyar sa , yazo yana mana subaɗaɗi , wai gungun sojojin nigeria ?  Ahayyee asha ruwa ayi tamɓele .

   Anya kuwa ɗan liti baka zuwa ka dubo mana ko ƴan sanda ne ? Kasan su fa matsayi ta ne ba mutunci ne da su ba yanzun nan sai su chafke mutum su sha janin sa ,"

  Bazai wuce su," Corporal garuje " ne suka zo samame ba suna neman na shan matala Kin fa san wata yayi nisa kum...
        Kamar ɗaukewar wutar lantarki madam saly ta ji ɗan liti ɗif,"
   Kan ta ankara ta ga gungun sojojin da suke ɗurowa cikin gidan , " cikin ta taji ya murɗa nan take laɓɓan ta suka ɗauki rawa ta gagara cewa ƙala ,"
   Na ƙale , wallahi na ƙale , nayi surrender !
   Ɗan liti ya furta haka yana kai guiyoyin sa ƙasa bayan ya ɗage hannuwan sa sama

Kai tsaye sojojin suka dunga kutsawa  ɗakunan gidan suna wurgo mutanen cikin ɗakuna waje ta ƙarfin tsiya , cikin mintoci kaɗan sai ga mutanen gidan rankatakaf a filin gida ,
   Kowannen su ciki ya ɗuri ruwa, sai waige waige suke , suna bin sojojin da suka saita su da bakin bindigogin su da kallo ,"cikin son sanin meke faruwa ? Wanne laifi suka yi ? Amma ba halin tambaya soboda tsoro 

Tsakiya colonel Youssouf ya fito cikin muryar sa mai amo da yake buÉ—e ta ya haka a bakin daga yace
   Ina yarinyar da kun ka boye a cikin gidan nan ? Ina take ? Ina Kun ka kaita ? Kuyi gaugawar fiddo ta kafin harsashai su sauƙa a kawukan ku baki ɗayan ku ,

     Cikin maƙyarƙyatar muryar da tsoro ya riga ya bayyana kan sa a ciki ɗan liti yace
   Wallahi Tallahi ranku ya daɗe ni ban san kome ba , ni yanzu shigowa ta gidan ma karbar saƙo wallahi ko jinjirin kiyashi bazan iya cutarwa ba bare ɗan mutum , ɗan mutum ma irin wannan mai darajar dan ....
   Dukan da sojon kusa da shi ya kai masa da ƙafa ya sa shi sakin ihu tare da zaman ƴan daɓaro a ƙasa ,

  Matsowa Youssouf yayi , kan madam saly
   Kin samo ta ko kouwa a ah ? Zaki fiddo ta ko kouwa sai kin ji ƙamshin mutuwa ,??
    Idanun madam saly da suka sake shigewa ciki saboda tsoro suka kawo ƙwalla,
   Wallahi ranka ya dade na duba ,  mun duba mun cigita , mun yi neman saƙo da lungu amma ko wanda yace ya ji ɗuriyar su ma ita da ƙanwar ta bamu ji ba , wallahi ranka ya daɗe ba ni na kori yarinyar nan ba raina yana son ta ina ƙaunar ta ita da abun....

Marin da ya ɗauke ta da shi ya hana ta ƙarasa dogon labarin ƙanzon ƙuregen da ta kwaso ,"

  Ku musu duka ku kai su mota mu wuce da su barrack , idan sun ɗanɗani azaba zasu faɗi inda take , " cewar Yaoussouf

  Kamar jira suke suka fara ƙwallo da su nan take guri ya ruɗe da ihun matan banza da kururuwar ɗan liti da ya buɗe maƙogoro yana zurma ihu tamkar ana watandar tsokar jikin sa , ya buɗe muryar sa ta asalin garjejen namiji ,"

   Kora su suka fara yi waje da shirin tafiya da su barikin su na soji ,"

  Nan fa idanun Yagana ya fara raina fata wacce ta sha manyan bulalai huɗu ,
   Ita tasan aka kai ta wannan barikin sojin sai ɗan buzun ta ,"  ta tsoraci soja ba kaɗan ba domin ta ga irin yadda basu ɗauki kisa a bakin kome ba ,
     Bulalar belt ɗin da wani soja ya sake sauƙe mata a gadon baya yana tunkuɗa ta ita ta gigita ta ,"

  Wayyo Allah bayana , fatar bayana ta sulluɓe , dan Allah ku tsaya wallahi na san inda take zan kai ku , zan kai ku Dan Allsh kuyi haƙuri kar ku tafi da ni ,
    Matsowa gaban ta yayi ya bar chasa madam saly da ta riga ta fara galabaita da bulalar soji ,

    Kin ka ce kin san inda take ?  Tana ina ? Ki kai ni yanzu - yanzu idan kin ƙi zan harbe ki ,"

    Muryar ta tana sarƙewa tace

Nasan inda take kuma ma ai Æ´ar uwa ta ce zan kai ku yanzu , Dan Allah kar ku ji min ciwo kar ku tafi da ni ,wallahi nasan inda YaKaKa take ,"

Finciko ta yayi ya miƙar ta tsaye , muje ki kai ni
     Yace yana tunkuɗa ta gaba , kafafun ta ko takalmi babu ,

   Ku cigaba da tsare su , idan mun same ta zan sanar da ku ta téléphone sai ku ƙyale su idan bamu same ta ba zaku zo mouna da su barrack ,

ÆŠaya daga cikin motar suka hau , Yagana da Youssouf da Tafeeda ,

  Ki gouda muna hanya," yace da ita
Chapter 99 · 0% Book details