Sashe 84
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Kawai ya taimake mu ne bamu san shi ba amma tun farkon zuwan mu garin nan tun muna sansanin mu yake taimaka mana !
 Jimm samy baby tayi tana aunawa tare da juya zantukan Yakaka cikin ran ta ,"
  Meye tsakanin ku da shi ? Ya taɓa cewa yana son ki ne ?
Da sauri ta girgiza kan ta
 A ah ni baya so na !
Bai tambaye ki akan cikin jikin ki ba ? Me kika ce masa game da cikin ?
Cewa yayi waye ya min cikin ? Ni kuma ban faÉ—a masa ba , tun daga ranar bai sake tambaya ta akan cikin ba , sai ya kawo mu gidan su nan , yace mu zauna , yana kula da mu sosai ni da falmata , har asibiti yake kai ni ayiwa baby photo dan Allah kar ki sa su kore mu anty samy bamu da wani wajen da zamu je a yanzu da ya fi nan ,
  Ta ƙarasa zancen hawayen da take tarawa a ido suna silmiyowa ,"
Guntun murmushi tayi
 Ni bazan sa su kore ku ba yaks , ki daina kuka ,!
   iyeeh watau har hoto aka yiwa baby ? kice dai kin shirya zama uwa sosai yaks
  jaan numfashi tayi kafin ta sake wurgo mata wata tambayar da ta sa zuciyar yakaka tsalle ,"
  Ya labarin yarima uban cikin jikin ki ko har kin haƙura da neman na shi kin daina son shi saboda kin samu gidan hutu ?
 Ban - ban daina son shi ba anty samy kullum yana raina inason sake ganin sa , ban san yadda zan yi na gan shi ba ne ,! Ko kin samu labarin inda yake ?
Murmushi tayi
  Nasan inda yake yaks !
Zuruf ta miƙe tsaye batare da ta ji nawin cikin jikin ta ba ta matsa ta kamo hannun samy baby ta riƙe gam.,
  Aina yake anty samy dan Allah ki kaini wajen sa , wallahi ina son shi , ina son na gan shi ki taimake ni !
Koma ki zauna yaks ba abun gaggawa bane , ki nutsu akwai maganar da nake so muyi da ke , amma....
  Shigowar sofi ta katse abun da samy baby take nufin cewa ,
  Da wani irin hargitsatsen kallo ta bi yakaka , kafin ta juya akalar hararar ta ta kan samy baby ,"
  Ke kuma me ya haɗa ki da wannan koɗaɗɗiyar ƴar gudun hijrar ?? Ko wani aiki zata miki ? Nifa na tsane su yi sauri ki sallame ta duk ta cika mana wuri da tsami da hamami ,"
 Ba tare da samy baby ta amsa mata ba tace ga yakaka
Ta shi ki tafi abin ki ,
Cikin sanyin jiki yakaka ta miƙe tana satar kallon sofi ,haushin ta na cinkushe mata rai ," sam ran ta bai so ba da zata bar gurin ba tare da taji wani ƙwaƙƙwaran bayani game da bature kam silum ba ," ta so ta ji ina yake da zama da babu abun da zai hana gobe ta je ta gan shi ko da kuwa da kwatance ne!
Dai-dai tazo barin ɗakin ta waiwayo suka haɗa ido da sofi wacce take bin ta da kallon banza ," bata yi ƙasa a guiwa ba ita ma ta galla mata harara tana mai ƙarasa barin ɗakin ,"
Duka samy baby ta ɗakawa sofi a cinyar ta wacce take ta faman baloƙoƙo akan hararar da yakaka tayi mata sai faman zagin ta take tamkar zararriya
  Ƙawata ke fa banza ce yanzu akan wannan ƙanƙanuwar yarinyar kike ta ɗaga murya haka ? Alhali ma tayi tafiyar ta ," ko dai haushin kaza kike huce akan dami ," hala shi autan mazan ya miki abunda ya saba ?
 Cisge ɗankwalin kan ta tayi jelar gashin dokin da tayi manyan kitson ghana suka watsu akan kafaɗun ta,"
Bari kawai kawata wannan ɗan tahalikin yana son ƙure gejin hakuri na akan sa , " bai san cewa akan sa kaɗai sashin zuciyata mai mutunci take iya tasiri ba , amma tunda yaƙi ta mutunci toh fa ko da tsiya -tsiya wallahi sai ya so ni kuma ya aure ni , sannan na juya shi yadda na so a lokacin da na so , Naga shege ko shegiyar da ta isa yin min katanga da cikar burina , wallahi ko gyatumin sa sun yi tsororo ! Hamza nawa ne ni kaɗai ,
Da kallo samy baby ta bita tana nazarin kalaman ta tare da É—auko kulawar da hamza yake bawa su yakaka tana haÉ—a su tare da yin dogon nazari ,
ita tasan wacece sofi tasan bala'i da kaidin sofi , bata fata ko kusa ko kaÉ—an ace wani sha'ani na adawa ya ratsa tsakanin ta da yakaka ,
wacece yakaka ? Bata tunanin ko uwar yakaka ta isa karawa da sofi akan abun da take ƙwalafacin so bare yakaka ,
tana tausayin yakaka da gaske baza ta so ba ta faɗo hannun sofi ta wannan mummunar hanya , ta sani sarai cikin ƙanƙanin lokaci sofi zata ɓatar da yakaka daga doron ƙasa ,"
Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji sofi tana cewa
  Wai kin kuwa san ma me yayi min ? Bata jira amsar samy baby ba ta ɗora ,
  Tsawa fa ya min a bainin nasi , dan kawai na nemi ya tsaya muyi hoto ,"
  Ta ƙuta , ai wallahi bashi ya ɗauka , zai kuma biya da tsada lokacin da ya shigo hannun na ,
  Ta miƙe tana mai nufar bathroom ,
Da kallo samy baby ta bita ," ya zama dole tayi wani yunƙuri domin ganin ta hana wannan yaƙin faruwa tsakanin ƙaramar yarinya yakaka da sofi , dole ta zare yakaka daga rayuwar hamza muddin ta gano yana da manufar soyayya da yaks ɗin kamar yadda ta hasaso , " ai idan ka ga kare na sunsuna takalmi ɗauka zai yi ," kuma banza bata kai zomo kasuwa ,"
10:30pm
Duk yadda Tafeedah ya kai ga son sanin meke damun Youssouf da har ya firgita shi ya zama barazana ga nutsuwar sa , Youssouf ɗin yaƙi faɗi masa , iyaka yace masa ya gaji ne da zaman nigeria yana son komawa ƙasar su ,
wanda shi Tafeedah ko kusa zancen bai shige sa ba , tayaya Youssouf masoyi ga aikin sa kuma jajirtatcen jarumi a fagen daga zaƙwaƙuri wurin bawa ƙasar sa kariya tare da sadauƙarwa zai ce ya gajiya ? Babu shakka akwai wani abu wanda yayi girman da yake neman jirkita masa tunanin aboki da shi bai kai ga sanin wannan lamarin ba ,"
Kallon sa ya mayar ga Youssouf É—in wanda yake kwance bisa gado ya takure cikin bargo gami da bashi baya , ji yayi duk wani É—an kuzarin da yayi saura a jikin sa yana barin sa , bayan tsawon watanni tara da rabuwa da ganin junan su , yau sun haÉ—u amma babu wani armashi a haÉ—uwar ta su kamar yadda suka saba ya haka idan aiki ya shataa layi ya raba su , toh fa duk ranar da suka haÉ—u kusan raba dare suke suna hirarraki da dararrakin su ta hanya bawa juna labarukan bayan rabuwar su , "
Youssouf amini ne a gare shi ƙari kuma ɗan ouwan sa ne na jini , amintakar su mai ƙarfi ce ta yadda idan ɗaya ya kasance cikin damuwa ɗayan ya kan gaza sukuni har sai sun haɗu sun samarwa da kan su mafita , damuwar sa a yanzu bai wuce yadda Youssouf ɗin yake kokarin boye masa abun da ke damun sa ba , da hakan yake baƙon lamari a tsakanin su sai dai ko ma menene zai bi a sannu har ya kai ga sani ,
Ga Youssouf ɗin kuwa damuwa ce ta yi masa katutu , kan ɓacewar yakaka , mafi girman lamarin shine cikin da aka ce tana tare da shi , tunanin sa idan ba'a kai ga samun ta ba har ya bar nigeria yaya zai yi ?? Shikenan zai tafi ya cigaba da rayuwa alhalin wata na nan ta wanzu tana aikata babban zunubi ana raba musu tare ??
Wannan lamarin ya girmama a gare shi danasani kuwa yayi ta yafi sau shurin masaÆ™i , a bayan kowacce daÆ™iÆ™a damuwa ke sake masa lullubi , ya Æ™agauta gari ya waye ya sake komawa gidan madam Saly ya ji yaya aka kwana ?Â
Yawan damuwar ita ta bayyana kan ta ga Tafeeda wanda a zahiri bai shirya ba baya kuma fatan wani nasa makusanci ya san irin ta'asar da ya aikata a rayuwar sa , duk da yasan Tafeeda aminin sa ne , amma bashi da karfin guiwar sanar da shi wannan auka-aukar da yayi , to ma me zai ce ? Ta ina zai fara ?
Ko babu kome shi É—an nasaba ne , É—an sarauta , É—an manyan mutane wanda wurin su ake hangen kyaun tarbiyya tare da nagarta har mutane suyi koyi ,
yana jin zuciyar sa na nawi a duk lokacin da ya tuno da matsayin sa tare da martabar sa ga idanun tarin wasu mutane YARIMA ne shi wanda ake sa ran bayan shuÉ—ewar wani lokaci idan da rai ya zama SARKI , JAGORA kuma SHUGABA abin KOYI ,
Anya-anya shi bai faÉ—a cikin wata babbar musifa ba kuwa ??
Ya ɗauki tsawon lokaci a haka yana kwance ba kuma bacci yake ba har zuwa lokacin da ya tabbatar bacci ya ɗauki Tafeeda , sannan ya miƙe gami da shiga banɗaki ya ɗauro Alwala ya zo ya fuskanci Al-Qibla yana mai fatan Allah ya kawo masa mafita ya kuma yafe masa zuban sa !