← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 192 OF 269

Sashe 192

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"a ah yarinya batun ba na kuka bane kin ga itta motar Borno dagga nan ai wahala take batta samuwa haka a sauƙaƙe , sabadda Borno daga nan tahiya ce miƙaƙaƙƙa ya ta mai yada shege , sai kin tai zouwa zender dagga nan ki shiga ta diffa kafin ki tsallaka boda ki shiga yankin Mobar ta jahar Bornon Nigeria , anya yarinya kina mace budurwa ɗanya shakaf kya iya wagga tahiya ta mazaje ?

" zan iya Baba , Allah zan iya , zan tafi ga taimaka min .

Tace , zuciyarta na sake haƙaƙewa kan tafiyar ita ce kaɗai mafita a gareta ,

" to babu laifi , bara shi malam Amadou gayu ya isso domin shi É—ai yake wannan dagon zagon Allah sa dai Æ´an tangaran basu riga sun kama kujerun motar ba , dawo dagga nan ki zauna , nan ba da jimawa ba ike isowa ,

A ɗarare ta zauna akan wani ɗan dandamali ba dan ranta ya so ba domin a matse take ƙwarai da ta bar yankin ,

Zaman mintoci goma kawai tayi sai ga motar Ahmadou gayu , wata wankakkiyar golf wagon ce da ta ci uban dilken da ake yiwa tsoffin motocin da ake son tada musu da komaɗa tare da ɓoye musu tsufan su .

Tayi zaton za ta ga wani matashin saurayi jin ana masa inkiya da "gayu , sai ta ga wani dattijon da ya tasamma shekaru sittin amma ya ƙi sarewa daga yin gayu domin kuwa a tsuke yake cikin ƙananun kayan da suka ɗau guga , ya ci zanzaro ,  kan nan nasa da sanƙo ya cinye rabi rabin kuma gashi ne a tare himili guda da aka yiwa shamfo a taje tsaf-tsaf yana sheƙin Mai .

Da fitowar sa gurin ya ɗau ƙamshin ƙaƙƙarfan turarensa na 999 for male .

Bai jinkirta ba ya fara goge jikin motar da a zahiri babu wani datti sai ƴar ƙura da ba'a rasa ba ,

ÆŠan kamashon nan shi yayi sauri ya samar mata wajen zama domin kuwa , kamar yadda yayi zato har an riga an kama kujeru huÉ—u na bayan motar ,wajen mutum É—aya tak ya rage ,

Dan haka Falmata bata jaa ba lokacin da aka yanka mata adadin kuɗin da zata biya , ta ƙirga kuɗin daga ciki ƴar karamar jakar hannunta da ita ce tal abunda ta riƙa , ta basu ta shiga gaban motar ta zauna .

Sauran mutane huɗun da yake daman sun riga sun kama kujerar motar suna zuwa shiga suka yi ba ɓata lokaci ..

Ƙarfe shidda cif motar su ta bar cikin tasha ta ɗau hanyar da tafiyar da zata iya kai su kwanaki biyu kafin isar su Yankin jahar Borno Nigeria  .

***

Tunda suka kama hanya ta kwantar da kanta jikin gilashin , bayan ta rufe rabin fuskar ta , A zahiri ta ɗora idanun ta ne bisa kan titi da ƙura irin ta juyin yanayin shigowar bazara ke tashi daga kan rairayin hamadan dake gefen titin ,

Sai dai can cikin tunanin ta ruhi da ƙwaƙwalwarta sun zurfafa ne cikin tsinkayen makomar rayuwarta tare da rarrabe fari da baƙi ,

Tun a jiya da ta san haƙiƙanin gaskiyar kome take jin tamkar mafarki ne tayi ba ido biyu ba ,

Tayaya za'a ce Mutane biyu masu girman daraja a rayuwar ta sun yi mata irin wannan mummunan rufa-rufa ?

Ashe Baban Mama da ta ɗau duk wani aminci da yarda ta ba shi , ta riƙe shi a matsayin mafi nagarta cikin mutane ,

shi ɗin mayaudari ne , fasiƙi , yayi zina da yayarta , ya gudu ya bar ta da cikin , tsakanin rayuwa da mutuwa , sannan daga baya ya dawo yayi ƙarya ya aure ta , ? Shiyasa mana yake shiga gigita da ɗimuwa a duk lokacin da tayi yunƙurin sanin irin alaƙar da ta kullu tsakanin sa da Yakaka , ashe Azzalumi ne .

Yakaka ta cutar da ita tun farko da bata taɓa sanar da ita irin alaƙar da ta kulla har ta kai ga samar da Mama ba ,

Ashe son da Yakaka take iƙirarin tana yi mata bai kai nan ba , tunda har ta iya gudu ta bar su ita da Mama jaririya akan ɗa Namiji bata ko tausaya musu ba  ,

ta tuno irin yadda fitar Yakaka daga rayuwarta ya jiggata mata rayuwa , ta tuna irin halin ƙunci da ciwon rai da tayi fama da shi , ta tuna da cikin kowanne irin yanayi na farin-ciki ko baƙin-ciki a rayuwarta tana yin su ne tare da tarin kewar Yakaka , bata taɓa sabawa ba da rashin ta , bata taɓa daina kukan mutuwar ta ba kamar yadda cikin duk wasu sallolinta bata tashi ba tare da tayi mata addu'ar samun rahamar Ubangiji ba , da yafiyar sa .

Amma ashe wai duk tsawon lokacin nan Yakaka tana raye cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali bata taɓa waiwayar su ba ? 

kuma wai da son ranta ta bar cikin rayuwar su ?  shin wanne irin so ne maigirma haka Yakaka take yiwa Youssouf ? Babu shakka tana iya tuno kaɗan daga cikin soyayyar da Yakaka take yiwa Bature kam silum ɗin ta ,

Dan haka tun jiya ta riga ta sulluɓe Youssouf daga ran ta , take kuma kankare duk wani ɗiso na ƙaunar sa daga ran ta , tana ƙenƙesawa zuciyarta Youssouf ya haramta a gareta .

Tunanin irin cutar da su biyun suka yi ga ɗiyar su Mama yana nuƙurƙusar ran ta tare da ƙara mata baƙin-ciki a duk bayan ƴan daƙiƙoƙi ,

Cikin ƴar taƙaitatciyar Rayuwar da Mama tayi babu shakka bata yi maraicin uwa ba , ta cikace mata gurbin da Yakaka ta bari ƙarƙashin son zuciyar ta ,

A ganin ta daga Youssouf har Yakaka bata su dace da zama Iyayen Mama ba , mutuwar Mama kuma hutawarta ne daga shan takaicin gori da aibatawan mutanen duniya ,

Ta zaɓi da ta tafi ta barsu tare tunda su biyun babu abunda suka sani sai tsananin son zuciyoyinsu , su zauna tare domin su biyun ai sun dace da juna ,

Ita zata koma Maiduguri , ta roƙi Prof kan ya raba auren su da Youssouf , babu wani sauran zama a tsakanin su tunda wacce ta aure shi a domin ta bata raye a duniyar ,

Abunda yake cikinta kuma ko Mace ko Namiji nata ne , zata riƙe abunta tayi rainon sa ita kaɗai ko da kuwa zata ɗora kwanon talla ne akanta tayi yawo bakin kasuwanni zata kula da ɗiyanta ba zata taɓa barin ɗan ta yayi maraici ba Alhalin tana raye .

***

Duk tafiyarta tsakanin Niger da Nigeria ta yi su ne a halin makanta , ƙarƙashin kulawa da jagorancin Hajja , kuma a motar gida da suke sake babu wata takura ,

Dan haka bata san kome ba game da hanya , ba gani take ba lokacin da aka yi tafiyar , yanzu kuma da take ganin hanyar dusu-dusu ba zata iya fahimtar cewa an nausa da ita wata hanya ta daban ne saɓanin wacce suka saba bi ba ,

Tsakanin Niamey da Diffa tafiya ce ta yini da kwana , kusan awanni ishirin , kuma hanyoyin ba sosai suka cika kyau ba musamman idan hanya ta sauƙa ta tsakanin rairayin hamada ,  ga kuma ranar da ta buɗe sosai take bada zafi .

Dan haka a wahale sosai take ga kiɗa da ya ƙi yankewa a motar tamkar ɗan wani ƙaramin gidan rawa , waƙoƙi daga na Sa'adu bori , sai na Hajiya Sa'adatu Aliyu "Barmani mai-coge"

bayan ƙarar kiɗan ga ta muryar shi kansa Ahmadou gayu da yake bin kowacce waƙa tamkar da shi aka rereta , bakinsa ko gajiya baya yi ,

Tafiyar su tayi nisa kasancewar Amadou gayu ƙwararren direba ne , azahar tayi musu suna wucewa ta cikin garin maraɗi ,

Falmata tayi lamo a motar gajiya gami da yunwa da ƙishirwa sun kai ga jiggata ta , babu kome a cikinta sai ruwa da ƙosai da suka saya tun safe a hanya da ba wani cin kirki ta yiwa ƙosan ba .

Lokacin da Amaudou gayu ya tsayar da motar sa , a gefen titi kusa da wani wajen sayar da abinci , domin a ci abinci , ayi sallah , daga sama ta tsinci muryar sa , yana cewa ,

"Maraɗi muke , cibiyar noma da ciyar da Al'umma to ayi harama , ayi sallah a ci abinci ayi kuma gurinsa , idan da mai laruri , ya tai ya sauƙe , domin idan na danna totur , banni dakatawa nan kussa sai mun dangana da Diffa , dan hakka kowa ya ɗau shiri , yauwa .

Ji tayi tamkar ta cigaba da zaman ta cikin motar , kar ta taka ƙafar ta a ƙasa domin tunda ya ambaci sunan Maradi tashin hankalin ta ya sake hauhawa , domin idan ba ta manta ba , Maradi shine sunan garin su Youssouf , ita fa a yanzu ƙyamatar duk wani abu da ya shafe shi take yi .

ganin idan ta cigaba da zama ita zata kwan ciki , yasa ta yunƙura ta fito , zagayawa ta fara yi neman banɗaki , saboda mararta da take cike .

Bayan ta idar da Sallar da tayi akan mayafinta , sai tayi zaune jugum daga inda take tana iya hango kai kawon jama'a ko ta ina a farfajiyar wajen tamkar ƙaramar kasuwa , masu abinci da masu shayi zuwa kan masu sayar da kayan sanyi sune birjik a wajen ,

Tashin hankalin da take ciki ya hana ta ji wata yunwar kirki tun ranar rasuwar Mama , sai dai tausayin abunda yake cikinta da tasan zai samu ne kaɗai daga abinda ta ci , ya sa ta miƙe ta ƙarasa wajen wata ƴar rumfar sayar da abinci da ta ga mutane na saya sosai , tuwo ta ce a kawo mata miyar yauƙi da kuma kunu bayan ta miƙa kuɗinta ga wata matashiya .
Chapter 192 · 0% Book details