← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 269

Sashe 21

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A firgice ya dago kan sa a sakamakon tunowa da yayi dawowar sa daren jiya da faduwar da yayi a harabar lambun sa wanda daga nan bai sake sanin inda yake ba a sakamakon kakkarfan baccin da yayi awon gaba da shi a wurin a yashe , da hakan baya rasa nasaba da sabuwar sumfurin dahuwar burkutun da ya sha a jiyan wanda gaba ɗaya ta hargitsa masa ƙwanya .

Aina ka tarar da ni ?

Shine kawai tambaÆ´ar daya jefawa tafeedah bai koh kula da irin kallon da tafeedan ke jifan sa da shi ba mai cike da tarin ma'anoni .

A jefa a inda kaga yafi dacewa da kai cikin kuma irin yanayin da ka zabarwa kan ka ."amsar da tafeedah ya bashi kenan " yana me miƙewa cikin yanayi na nuna alamun tafiya yake da niyyar yi ,"

Wani boyayyar ajiyar zuciya biyamuradi youssouf ya sauke a sakamakon fahimtar da yayi cewa tafeedah ne ya kawo sa É—akin nasa ,"

Da misalin karfe nawa ka shigo gidan ? Su wa ka tarar a haraba ta ina nufin ma'aikata na sun yi chanji ?

Mts! Idan kasan kana gudun zubewar mutuncin ka me zai sa ka jefa kan ka cikin rayuwar da kake youssouf ," tafeedah ya furta hakan cikin ƙufula yana me komawa ya zauna a inda ya tashi ,"

Cigaba yayi da cewa karfe uku na asubah na shigo sashin ka bayan tasowata daga wurin taron mu (meeting) ,inda masu tsaron gidan suka tabbatar min kana ciki tun farkon dare ,"

Amma abun mamaki nazo na gama neman ka ƙasa koh sama baka nan har nayi niyyar fita na sanar da masu tsaron ka , sai nayi tunanin zagayawa har cikin lanbu inda na tarar da kai kwance a ƙasa , da farko na tsorata amma daga baya na fahimci abun da ka min alkawarin ka daina sha kayi min rantsuwa da Allah akan baza ka sake sha ba ita ka sha youssof , ƙarin abun takaicin ma a cikin gidan nan , bayan ka san duk cikin ahalin gidan nan babu wanda ya taɓa sanin kana ta'amali da barasa ," kafi kuma kowa sanin masifun da fallasuwar wannan mummunar ɗabi'ar taka zata iya jawowa a garemu baki ɗaya ,"haba youssof , haba youssof , duk cikin tarin ababen zubda mutunci da jawo tozarta ka rasa wanda zaka zaɓa sai BARASA ? Bayan kasan itace shugaba ummul'aba'isi na jaan ɗan adam ga aikata kowanne irin sabon ubangijin mu ,"

tsagaitawa yayi lokacin da yaji muryar sa ta fara karkarwa alamun gaf yake da fara kuka sakamakon ƙona masa zuciya da wannan ɗabi'ar ta abokinsa ,amininsa kuma ɗan uwan sa youssouf da ya jefa kansa a ciki tun yana da ƙarancin shekaru sosai domin shi da kan sa ba zai iya cewa ga lokacin da youssof ɗin ya fara shan barasa ba , kawai dai ya farga ya gane ne shi da kan sa a saboda kusancin da suke da shi da juna ta yadda wasu lokutan dayawa zai taradda da youssouf ɗin cikin maye ,"

wanda tun yana ƙaryata kan sa cewa youssouf giya yake sha ,a dalilin tsawaita bincike da yayi bai taradda alamun barasa ba a duk inda youssouf ɗin yayi bigire da kuma boye masa tare da waskewar da ya dunga yi , har dai ya zo ya yadda, kuma yayi amanna aminin sa mashayin giya ne , ya kuma tabbatar lokacin da ya bi shi har zuwa wani tsohon kuchakin gidan saida burkutu wanda yake chan tsakiyar unguwannin talakawan gari inda anan youssouf yake zuwa yayi tatul , amma baya guzurin ta .

A ranar yayi kuka har kan sa yayi ciwo ,kuma ya girgiza matuka musamman da yayi duba ga matsayin youssouf a garin na kasancewar sa É—an sarki mai jiran gado , wanda ake sa ran watarana shi zai jagoranci dubannan al'ummar yankin ya zama shugaba a gare su abun koyi ,

Yaya hajiya umma (mahaifiyar sa) da mai martaba ,haɗi da ƴan uwan sa zasu ji a lokacin da suka farga , uwa uba yaya al'ummar gari zasu dubi lamarin yayin da labarin ya bazu ga kunnuwan su , haƙiƙa maƙiƴan sarari da na boye zasu ji daɗi suyi murna , sannan kuma da akwai yiwuwar subucewar samuwar mulkin jahar maraɗi daga hannun sa domin rashin chanchantar sa ta wannan fuskar ! Wane irin mulki ake zato ga mashayin sarki ????

Tun daga lokacin tafeedah ya nuna cikar amintakar dake tsakanin su da biyamuradi youssof ta hanyar yi masa faɗa da nasiha mai tsanani a kullum, gami da boye masa sirrin sa tare kuma da toshe duk wata hanyar da zata iya sa asirin youssof ɗin ya tonu , sosai yake koƙarin kare masa martabar sa da mutuncin sa , ta inda har ta kai yasamu nasara a wani dare shekaru biyu da suka wuce ,biyamuradi youssouf ɗin yayi masa alkawarin daga ranar ya daina shan barasa bayan fada da suka yi kacha-kacha inda tafeedah har yayi wa youssouf ɗin barazanar daina shiga sabgar sa idan har ba zai daina ta'amali da barasa ba .

Farin ciki tare da kwanciyar hankali suka wadata ga tafeedah bayan jin alkawarin da youssof yayi masa ",cikin rashin sanin tuban muzuru youssouf ɗin yayi ya kuma ninke sa a baibai domin daga ranar ya sauya lokutan shan barasar sa muddin yana cikin garin maraɗi , ta yadda ya maida tsakanin sulusin dare lokacin fitar sa ya sha abar sa , yayin da idan yana wata ƙasar koh wata jahar a duk lokacin da ya samu sarari yake zuwa ko'ina ne ya nemo barasar gargajiya da aka fi sanin ta da " *BURKUTU* " zazzafa ya sha iya shan sa babu abun da ya fasa .

Janye idanun sa da suka ciko da ƙwallar takaici tafeedah yayi , cikin rashin kuzari ya sake miƙe jin youssof ɗin ya rasa abun faɗa , toh me ma zai faɗa masa ? Soke hannayen sa yayi cikin wondon sa ,"ni zan shiga na gaishe da hajiya umma daga chan zan wuce ,sai kuma Allah ya kaddara saduwar mu , ina mai fatan Allah ya kiyaye ka ya baka nasara akan waɗanda zaka tunkara ,"

Daga haka ya sanya kan sa gaba da sauri youssof ɗin ya miƙe daga kan dardumar da ya idar da sallar sa ,"Jira ni nima babu abun da zan yi da wuce wanka sai mu fita tare ," bai jira amsawar sa ba kamar yadda shima tafeedah bai tsaya domin saurarar sa ba ya sanya kai yana me ƙarasa barin katafaren ɗakin youssouf ɗin .

Yana shiryawa yana tunanin maganganun aminin sa tabbas duk wasu kalmomin da ya É—auki shekaru yana furtawa agare shi gaskiya ne ," kuma shima a karan kansa yana mai bakin cikin halin da ya wayi gari ya tsinci kan sa a ciki sannan yayi iyakacin kokarin sa dan ganin ya daina shan burkutu amma hakan ya gagareshi duk kuwa da addu'o'in da yake yi a koyaushe yayi sallah akan Allah ya yaye masa, amma abun kamar tiri ,

ji yake idan bai sha burkutu ba a kowacce rana , yana iya rasa numfashin sa , burkutu ta zama jinin jikin sa , mahaÉ—in rayuwar sa kuma abar dake samar da nutsuwa da farin ciki a rayuwar sa ( a ganin sa kenan )

Ajiye matajin hannun sa yayi bayan ya kammala taje ƙwantatciyar sumar sa wanda yake yawan yi mata saisaye luf-luf da ita ," yayi yawo da idanun sa a ɗakin cikin son gamsuwa da bai bar wani abun sa mai muhimmanci ba ,"duk da cewa tun a daren jiya sojan dake kula da shirye-shiryen tafiyar tasa ya kammala haɗa masa kome cikin umarnin sa da yake zaune a gefe yana gwada masa abubuwan da yake bukatar tafiya da su ,"ya shirya su tsaf tare da kai su motar da aka shirya zai yi tafiya zuwa Niamey inda daga nan zasu daga zuwa Nigeria.

Cikin takun sa na ƙasaita wanda yake bayyana cikar jarumtar sa irin na gwarzon soja , jaan tunga yayi ya tsaya "ɗan mitsitsin murmushi yayi ganin tafeedah da yayi a zaune cikin ɗaya daga cikin kujerun falon fuskar sa kadaran kadahan ya dago ya dube shi gami da miƙewa tsaye yayi gaba ," da sauri ya bi bayan sa suka jera .

Cikin nutsuwa suka yi sallama a babban falon hajiya umma , da ya jawo hankalin siyama da merama aisha da suke zaune bisa wadatattciyar darduma suna ƙarin kumallo ," gefe guda masu hidimar zuba musu abincin da tsaftace wurin ne suke durƙushe zaman jiran su kammala , zumbur aisha ta miƙe

Da ɗan gudu da tsalle ta ƙaraso gare su dai-dai lokacin da suke yiwa kan su mazauni akan jerun kujerun falon ,"zama tayi a gefen biyamuradi gami da ɗaura kan ta bisa kafaɗun sa ",barka da safiya hamma nah ,
nayi kewar ku sosai na same ku lafiya . ?

Shafa kan ta yayi lokaci ɗaya fuskar sa tana sake faɗaɗa da yalwatatcen murmushin da yake bayyana tsananin  ƙaunar sa ga ƙanwar tasa yace ",

lafiya lau meramar mai martaba yaya karatu ?
Yaushe kika zo ?
anyi muku hutu koh ?

Anyi hutu hamma jiya da yamma nazo .

ÆŠan gyaran murya tafeedah yayi ,

Murmushi ta sake yi tana me sunne kanta a jikin hamman nata tace ,"ina kwana hamma tafeedah na same ku lafiya ," ?
    Bazan amsa ba tunda abun ma wariyar launin fata ce ,"

    Leƙo shi tayi ta bayan biyamuradi tana ɗan murmushi tace yi hakuri hamma tafeedah kasan nayi kewar hamma na watanni uku fa ,"

    Kallo yake mata me kama da harara amma kuma fuskar sa ɗauke da sassayan murmushi wanda sai shi ya san ma'anar sa , sai kuma ita da duk lokacin da yayi mata irin wannan murmushin da kallon take tsintar kanta cikin wani irin yanayi na fargaba da mutuwar jiki ,"

Cikin sanyin jiki siyama ta ɗago idanun ta tana mai sauke su akan abun ƙaunar ta ," hamma youssof antashi lafiya ,? Hamma tafeedah barka da asuba ,?
Chapter 21 · 0% Book details