Sashe 62
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba ɗaya sun fara lalacewa kasantuwar su duk biyun ba ma'abota son tashin hankali bane daɗi da ƙarin tsoron madam saly da suke yi kamar me ,!
Allah Allah yakaka take yi samy baby ta dawo , ko zata ɗan samu sa'ida da wurin fakewa , bakin cikin ta ɗaya akan bacewar ƴar takaddar da samy baby ta zana mata lambar wayar rta bisa ,ta nemi ƴar takaddar ta rasa sama ko ƙasa babu , tafi zaton a tun ranar da ta bata ta yar ba tare da sani ba ,
a haka kwanaki suka tura , zuwa lokacin da lamura suka fara tsananta gare su , laulayi tuƙuru ya sako yakaka a gaba , kome ta ci amai take ,bata da abun so da kuma yake ƙwantar mata da hankali irin ƙamshin turaren youssouf da yake manne da jikin kuɗin sa na Niger da kuma agogon sa, duk dare da su take ƙwaƙume cikin zanen rufuwar ta , idan ba haka ba babu ita ba bacci , ɗan ƙaramin hoton fuskar sa ya zamar mata abu ɗebe kewa a duk lokacin da ta ji son sa ya mintsine ta !
ga aikin da madam saly ta walle ta ce bata janyen shi daga kan ta a wai domin tana laulayin shegen cikin ta , a cewar ta ma ita ake ƙwara , kullum cikin zagi da aibata yakaka take da munanan kalamai iri-iri a duk lokacin da taji tana amai ,"
A halin yanzu duk wani mai shigowa cikin gidan ya san yakaka tayi ciki , ciki kuwa har da ƙawar ta da suka zo gari tare yagana , wacce tun daga lokacin da ta ji da kunnen ta yakaka tana da cikin shege , ta janye mata , magana ta kirki bata haɗa su , haka yakakar zata yi ta bin ta tana so ta bata dama suyi magana amma fir yagana ta juya mata baya taƙi kula ta , ɓaro-ɓaro take nuna ita fa kƴamar ta take yi , da har ta kai a wani yammaci ta gaggasawa yakakar magana ta kuma nemi da ta fice a harkar ta ita ba karuwa bace mai abun kunya irin ta ,"
  a ranar kusan raba dare yakaka tayi tana kuka a cikin zanin rufuwar ta bisa teburin kwanan ta , ji take gaba ɗaya ta muzanta domin a zuwa yanzu ta fara amincewa da tana ɗauke da cikin shege a jikin ta ,"
Sannu sannu rayuwa tayi wahala da tsanani ga yakaka da falmata , domin kuwa a halin yanzu haka suke wuni jibge a gefen ɗakunan gidan cikin yunwa da ƙishirwa , saboda yakaka bata iya yin aikin dalilin rashin lafiya , amai da take ta faman yi ya ƙarar da ruwan jikin ta ga kuma ba abincin kirki wanda hakan ya sa gaba ɗaya jikin ta ya shika yayi yaushi idanun ta har kore-kore suke , babu mai kula ta sai ƙanwar ta wacce ita ma yawan tashi ta zo wurin yakaka idan taji tana amai ko kuma idan tana buƙatar ruwan da take shan sa take dawo da shi , ko kuma ta kawo mata abincin ta da ba iya ci take ba , wannan zirga-zirgar da take yi ya jaa madam saly tace ta dakatar da ita daga yi mata wanke wanken da take yi a cewar ta baza ta yadda falmata ta dunga gwamutsa mata aikin wanke wanke da wankin amai ba ," ta maye guraben su da wasu fallallun ƴan mata biyu , a cewar ta tun da sun zame mata ƙarfan ƙafa , baza su bar gidan ba to su nemi abincin su wurin kwana kuwa su tsaya daga tsakar gidan zuwa cikin rumfa ,"
Da hakan suka amince domin kuwa basu da wata mafaka bayan nan É—in yini suke bin inuwar gaban É—akuna da baccon kayan su da shi ma aka wurgo musu abun su kan su ,Â
babu mai lura da su , sai idan falmata taji yunwa na neman galabaitar da su ta daidaici lokacin kammala cin abinci ta lallaɓa zuwa bakin makwarari inda take ɗan tattaro musu guntattakin abinci da ƙanzo-ƙanzo da a yawan lokuta ita ɗaya take ci domin yakaka ko son kallon abincin bata yi bare ta kai ga ci ,"
Idan dare yayi kuma su koma cikin rumfa su kwana bisa tebura.
Falmata ta so ta fara fita bara sai dai rashin ɗan jagora ya hana ta , tayi yunƙurin neman taimakon yagana akan ta dunga kai ta bakin hanya wurin barar ta amma sai yakaka ta hana ta yiwa yaganar magana ,"
a cikin wannan halin na tsanani suka shafe fiye da sati uku suna watangaririya cikin rashin galihu , tare da yunwa da kirshirwa ,Â
kwatsam rana ɗaya sai ga samy baby ta dawo bayan ta shafe kusan watanni biyu da ƴan kai bata nan , nan ta tarar da yakaka cikin mummunan yanayin mutu Kwakwai rai kwakwai , ba shiri ta kwashe su zuwa wani ɗan jeka na yi kan asibiti mai zaman kan sa ,"
Nan aka shiga bata taimakon gaggawa , har jini aka ƙara mata leda ɗaya bayan ruwa da tarin allurai da ta sha ,
Ba ƙaramin faɗa likitan yayi ba da yadda aka bar yarinya ƙarama da ciki jikin ta cikin irin wannan mummunan yanayi , har ma ya nemi da ya ga mijin ta domin su gargaɗe shi
  sororo samy baby tayi tana kallon likitan , kafin ta buɗe baki tace
  ciki fa likita ? Waye ke da cikin ?
Ita marar lafiyar da kika kawo/ƙanwar ta ki
 kina nufin baki san tana ɗauke da ciki ba har na tsawon sati goma sha biyar da kwanaki shidda ? ?
  Goge gumin da ya tsatsafo mata a goshi tayi ,"
  Ban sani ba likita kasan bama tare jiya na dawo daga tafiƴa , ta furta hakan cikin rashim sanin takamaimai amsar bayarwa , cikin sanyin jiki ta miƙe ta fito daga ofishin likitan bayan ya sake jaddada mata lalle ta nemo mijin yakaka !
wai yaks ke da cikin??har na tsawon watanni kusan huɗu , wannan wanne irin ɓata wasa ne yaks take son yi masu ? Ita da ta je abuja ta ga yadda alhazan birni ke rububin ƙananun ƴan mata irin yaks , har tayi mata sha'awar samun irin wannan damar ta dawo da niyyar ta sake wanke ta ta shigar da ita aJi na musamman ta samu ilmin bariki yadda zata ci ribar sa su wuce abuja tare ,"
ta huce takaicin duniya ", hatta waɗanda suka raɓe ta ma su huta , amma shi ne dan rashin sa"a zata zauna da ciki a jikin ta har tsawon wannan lokacin , waye ya gaya mata ana haɗa harkar bariki da jego da rainon ƴaƴa ?
Ya zama dole a fidda cikin nan muddin tana so tafiyar ta tayi kyau !
BAYAN SATI ÆŠAYA .
Jikin yakaka yayi kyau ta murmure babu laifi duk da cewa shi laulayi bashi da wani magani takamaimai amma dai ta samu farfaɗowa daga halin galabaitar da ta shiga , sai ɗan abun da ba'a rasa ba na daga larurar masu ɗauke da ƙaramin ciki , kamar kasala , tashin zuciya , yawu da sauran su .
dan haka yau likitan ke sallamar ta bayan ya kafa mata dokokin kula da kan ta da lafiyar jaririn cikin ta , ya kuma sake jaddada mata da ta fara zuwa awu cikin wata mai kamawa ,"
Yakaka wacce zuwa yanzu ta amince tabbas tana ɗauke da ciki a jikin ta domin kuwa ga cikin ya ɗan fara tasowa kuma kaɗan kaɗan tana ɗan jin taurin sa yana dunƙulewa guri guda ,"
  Cikin ladabi ta amsawa likitan tare da sake jero kalaman godiya tana mai satar kallon samy baby wacce tayi kicin-kicin da fuska ta ɗauke kai ,"
  Cikin da za'a a markaɗe shi shine har ake jero ka'idojin kula da shi ? Ai suna komawa gida gobe zasu shirya ta kai yakaka a fidda mata wannan alaƙaƙai ɗin , abun da ma yasa bata fitar da nufin ta anan ba saboda ana iya chafke su idan aka ji nufin su ,"
Kai tsaye ɗakin samy baby suka wuce , bayan isar su gida , nan ta shige banɗaki domin watsa ruwa ta bar su a raƙube daga bakin kofar ɗakin , sun yi shiru basa cewa juna ƙala kowacce tana saurarar zuciyar ta , fargabar su ɗaya hukuncin da itama samy baby zata iya aiwatarwa akan su . Ko ita ma korar ta su zata yi kamar madam saly ?
Bayan ta gama wankan ta , ta shafa mai ta shirya ta zo ta zauna ta tisa su a gaba ,
   Falmata ɗan bamu waje zan yi magana da yayar ki ,"
Â
Toh anty ,
da lalube ta ƙarasa ficewa daga ɗakin ta fice chan farfajiyar gidan ta tsugunna daga jikin bango .
Yakaka ashe har rashin wayon ki ya kai ki zauna da ciki tsawon wannan lokacin a jikin ki ba tare da kin É—au matakin rabuwa da shi ba ? Kin kuwa san barazanar hakan ga rayuwar ki cikin wannan halin da kuke ciki ke da Æ´ar uwar ki ?
Anty kiyi hakuri nima ban san yaya zan yi ba ," ta furta hakan tana me share ƙwallar da ta silalo bisa kumatun ta ,"
To wai ma ba na kai ki an miki allurar hana É—aukar ciki ba ?
Kin kaini anty , kiyi hakuri !
Mts kome dai aka yi da jaki sai ya ci kara ,!
  yanzu sai ki shirya gobe mu je a fidda cikin nan daga jikin ki ,"dan bazai yiwu ki zauna tare da shi ba
Ɗas Ɗas Ɗas zuciyar ta ta buga ,"
  A jirkice ta ɗago kan ta dake sunkuye ta dubi samy baby da raunanan idanun ta cikin sanyin murya tace
  A kai shi ina anty ?
Galala samy baby ta dube ta
  a kai shi ina kike tambaya ta ? a subda shi a kwata ya bi makwarari toh meye amfanin sa ?