← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 269

Sashe 15

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsugunne su yakaka suke a bayan hilux ɗin, sojoji biyu sun sanya su a tsakiya a zaune a kan ɗan tudun da aka tanada domin zama ," ji suka yi iskar shaƙa ta musu yawa a saboda gudun da motar ke yi ,"nan take maƙoshin su ya bushe ƙemas , idan ban da sharar hawaye babu abun da suke yi ,tun da suka hau motar babu me cewa ƙala ,"

Gware yakaka da falmata suka yi ," a sakamakon wani irin birki da motar da suke ciki ta jaa," wani marayan kuka falmata ta fashe da shi a dalilin zafin da ya ziyarci ƙwaƙwalwar ta a dalilin gwaren da suka yi ",

Dira sojojin da su ke tare da su a bayan motar su ka yi kafin su yi musu umarni akan su sauƙo ,

Tsayawa yakaka-da-yagana suka yi suna ƙarewa wurin da aka kawo su kallo ,"wata babbar kofa ce a gaban su me kama da kofar gari a ganin su, sai da ƴaƴan hanjin cikin su yakaka ya kaɗa sakamakon ganin wasu gungun sojoji da suka yi daga cikin wata rumfa a gefen kofar ,"
Yakaka ina aka kawo mu ,? Inji falmata ,"
Nima ban sani ba falmata ,amma dai kamar wani babban gari ne shima gashi dai har da wata babbar kofar sa ," ta furta hakan tana me satar kallon sojojin da koh kula da su basu yi ba,"

Ku zo mu je nan shine camp (sansanin Æ´an gudun hijira ) inda gwamnati ta tanadar ga ire-iren ku ," a cewar wannan sojan da ya wuce gaba ,"

Da sauri su ka bishi ransu yana wani É—an motsin daÉ—i-daÉ—i ! Duk da cewar dai basu gama aminta da zancen sa ba domin basu tabbatar ba ,'

Yakaka da yagana su na sanya kafa cikin wurin suka fahimci ba ƙaramin babban fili bane ta ciki , a yayin da suka fara yawata idanun su zuciyoyin su cike da mamakin ganin mutane birjik fululu iyakar ganin su suna ta harkokin su ,"

Hayaniyar jama'ar da falmata ta fara ji yana tashi cikin yaren su , shi ya sanya ta ji kaso goma na tsoron da yake cike da ranta ya kau ,!

Bayan ƴar gajeruwar tafiyar da suka yi , bakin wani gini sojan nan ya tsayar da su yayin da shi ya taka ya shiga cikin ɗan wurin mai kama da ɗaki ,"(Office)" bai kai minti biyar ba ya fito ba tare da yace da su kome ba yayi wucewar sa cikin rashin kulawa da gaisuwar da wasu mutane maza da suke zaune turmus a cikin ƙasa da suke yi masa ,"

Cigaba da tsayuwa su yakaka suka yi a wurin har dai zuwa lokacin suka fara jin ƙafafuwan su sun fara sagewa a gefe guda yakaka da yagana cikin ransu suna nazarin tsarin wajen ," daga gefe gine ne a jere reras tamkar ɗakuna da barandar su doguwa wanda aka yi ginin da bulok tare da rufin kwanon da suke iya hango rufin sa da duk rana da ruwa suka gama illata sa ya zama jazir ," babu abun da yafi yawa a sararin wurin irin bishiyoyin darbejiya wanda suka lura karkashin kowacce bishiya a cike yake da mutane maza waɗan da suke zazzaune wasu kuma a kwance ,yayin da wasu suke a kishingiɗe turmus a cikin ƙasa ," daga inda suke tsaye suna iya hango matan da suke cike a cikin kowanne ɗaki har zuwa barandar ,' dukkanin su mata ne da ƙananun yara da kallo ɗai-ɗaya su ka yi musu suka fahimci halin tagayyara da wahalar da suke ciki ( makamanciyar ta su ),

Daga farfajiyar wurin da babu wadatar bishiyoyi wasu manyan ɗakuna ne wanda aka yi su da ƙarafuna tare da rufin leda mai nawi ,"tantinan wucin gadi ", nan ma a cike yake da mutane maza da mata ," wata boyayyar ajiyar zuciya yakaka ta sauke lokacin da taga wasu maza sun zo sun wuce ta gaban su ,"hannun su riƙe da buhun-hunan da ta gane na abinci ne ,

Yakaka wai tsayuwar nan kam ba ta ƙare ba ce koh ? Yagana ke furta hakan a lokacin da ta karya gwaiwar ta da nufin tsugunnawa , "sai dai bata kai ga tsugunnon ba taji ɗaya daga cikin mutanen da suke zaune karkashin bishiya daga gefe ya ce ," kai kai ku tashi daga nan chan za ku tafi ku nemi wurin zama," yana yi musu nuni da sashin ɗakunan nan. "

koh kafin yagana ta samu abun faɗi ,"suka ga an fito daga wannan ɗan ɗakin da daman suke dakon jirin fitowar mutum daga cikin sa ," da sauri suka zube ƙasa suna gaishe da ɓakin jibgegen mutumin da yake yi musu kallon sheƙeƙe ,"

Ba tare da ya amsa gaisuwar ta su ba ya fara cewa to menene ,? Menene kuma ? Kai Duba ni fa na fara gajiya da ku da ƙorefe-korefen ku , ku koma can daga wurin ku idan waɗanda Alhakin faɗa musu ƙorefe ƙorefen naku ke wuyan su , sun zo kuna iya zuwa kuyi dafifi ku faɗa musu , amma nikam bazan iya wannan halayyar taku ta rashin godiya ba

," wuce su yayi tinƙis-tinƙis yana tura cikin sa tare da mita ,"haba ace mutane sam baku da godiyar Allah a ɗau nawin ku ci da sha da gurin kwana ba tare da koh sisin kobo ba amma duk da haka kullum ta Allah sai kun zo da sabon tsirfa ,"yau ku ce wance gobe wannan koh da yake ba laifin ku bane ," gwamanati da ta ƴanta ku daga noma da shan ruwan kududdufi ita ke da laifin ",

An ɗauki tsawon mintuna biyu babu wacce tace ƙala tsakanin su ukun , kowacce da abun da take saƙawa cikin ran ta ,"

Yaraf ,"yakaka ta ƙarasa bajewa a ƙasa daga durƙuson da suke ," a sakamakon bangaje ta da wata mata tayi wacce take tafe tana ta zabga sauri har zanen ta na kuncewa bayan ta kuwa wasu mata ne su ma gungu sun doshi wajen su hamsin koh fin haka ," wucewa suka yi tare da nufar sashin da su ka ga ɗazu wasu maza sun bi da buhunhunan abinci .

Cikin sanyin jiki suka miƙe tsaye Falmata tana me sake lalubar jikin yakaka wacce ta ke riƙe da ɗayan hannun ta ,"
Yakaka ya akayi kika faÉ—i baki ji ciwo ba koh ?
Banji ciwo ba falmata ," ku muƙarasa daga can .

Watau nan shine masaukin da gwamnati ta tanada domin ɓaki ƴan gudun hijira ,"? Yagana ke furta hakan dai-dai lokacin da suke zama a bakin ɗaya daga cikin fasasshiyar barandar wurin ,"

a toh ga zahiri dai kin gani ,"cewar yakaka wacce gaba É—aya ta gama tsinkewa da irin rayuwar da ta hango musu a wannan matattarar kazo na zo É—in ,"

Wai yaya fasalin tsarin wajen yake yakaka ?. Yanzu fa ba zama yakamata muyi ba , dacewa yayi mu fara zuwa mu ƙarbi abinci mu ci sai muyi sallah mu bazama neman mama kamar yadda muka tsara ko kuwa ?

Haɗa ido yagana da yakaka suka yi kafin yagana ta ce hmmm ai falmata bamu kai ga fahimtar tsarin wajen ba tukun ," ga mu nan dai kara zube kamar yadda muka lura kowa ma a zuɓen yake a wurin nan ," amma bari naje na fara da tambayo mana inda banɗaki yake domin ni mara ta ma cike take dam ,"
***************
Lalee ,sannun ku jama"a dan Allah ina ne inda banɗaki yake ? Sannan kuma ina ne wurin cin abinci mu ɓaki ne yanzu muka zo ," yagana ke yin dogon bayanin nan bayan da ta tadda wasu gungun mata da su da ƴaƴan su a zaune cikin ɗaya daga cikin ɗakunan nan ,

Ga mamakin yagana ba wacce ta ɗago kan ta ta ɗube ta bare ma ta sa ran za'a amsa ma ta ," duk kuwa da cewa cikin yaren su tai maganar kuma zanen da yake ɗauke a fuskokin mafi yawan matan wurin da suka kusan tasamma su arba'in ya isa sanar mata cewar daga ƙabila ɗaya suke ita da su ,"

ɗai ɗaya take kallon su yayin da ta ke jin wani irin ɗan banzan wari da zarnin futsari yana cunƙushe mata kofofin hancin ta ,' ƙudajen da suke yanyame cikin ɗakin da babu koh shimfiɗar tabarma sai ɗaben suminti ," sai kuka suke yuyuyuyu , gami da kukan ƙananun yaran da wasu ma koh ɗan kanfai babu a jikin su , sai tarin layu da zaren jigida a ɗaure a ƙugun su ," shi ya sanya yagana tayi hasashen koh hayaniyar cikin ɗakin ne ya sanya wasu basu ji ta ba ,"

Sake maimaita bayanin da tayi da farko tayi ," Can baya zaki zagaye kiyi abun da zaki yi maganar abinci kuma ba'a kai ga kammalawa ba ," ki adana sauran tambayoyin ki domin mu ma nan duk da kika ganmu riƙe mu ke da tarin tambayoyin da muke son samun amsoshin su ,"

Tsam yagana tayi a tsaye bayan da ta gama jin bayanin matar nan ,"jan ƙafafun ta ta soma yi da nufin barin wurin alokacin da taji matar nan ta ɗora da cewa kika ce ku ɓaki ne ? Ke da su wa ? Ba tare da ta jira amsar yagana ba ta ɗora da cewa kun kaima barka domin kuwa a yau gwamna ke kawo ziyara ƙaron farko a sansanin nan ," nan da kika gan mu a zazzaune dakon jiran sa muke ," domin ance tafe yake da tarin kyautukan alkhairi .

Ai nan take yagana ta washe baki ji da tayi sun taki sa'a lokaci ɗaya ta ji ta nemi sanyi jiki da taraddadin da ya fara mamaye ta a sakamakon bayanin matar nan na farko ta rasa ," farin cikin albishirin da matar tayi mata na ganin gwamna ra'ayul'ain a yau ya wanke mata bacin ran da take ta shaƙa tun fitowar ta daga garin su ai da gudu ta kwasa har tana murguɗe kafa tayi wurin da ta bar su yakaka .
[6/24, 9:58 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association

*MAFARI......*
( _HARGITSIN RAYUWA_ )

*Umm'muaz*

5
Chapter 15 · 0% Book details