Sashe 26
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
   Yakaka bata iya ɗinkin hula ba koh riƙe allura a soka bata iya ba, asalima a cikin wannan halin bautar da muke ciki ina yakaka zata samu damar da zata zauna ɗinkin hula , yakaka kar ki ƙarbi abun mutane ki zo ki ɓata musu abu ya zo ya zama rigima da muguwar rawa gwamma ƙin tashi mu cigaba da addu'a Allah zai kawo mana mafita ,"
Falmara ta furta hakan karon farko tana me jin ciwon rashin idanun ta da babu abun da zai hana tayi ɗamarar karba kwangilolin ɗinkin hula har sai ta samar musu rayuwar da ta fi wacce suke yi yanzu inganci ita da yayar ta domin babu dare ba rana zata duƙufa soka allura da zarewa koh da zata tsire ƴan yatsunta da allura ," sai dai tana jin baza ta iya barin yakaka ta yi ba saboda sanin irin tarin ayyukan da suke jibge akan yakakan wanda mafi akasarin su na wannan azzalumar matar ne fanne " idan dai ba tsakar dare yakakan zata tashi yin ɗinkin hular ba bata hango tana da lokaci ba , tsakar dare kuma da wanne haske zata soka allura a matsayin ta na ƴar koyo ? Su da basu da koh ashana bare tocila ? Zata fi so yagana ta zo da shawarar wata sana'ar da ita ma za'a iya haɗuwa da ita ayi .
Shiru ne ya biyo bayan katse musu hanzari da falmata tayi ,kafin yakaka ta yunƙura cikin karfin zuciya
   " zan iya falmata , yagana yaushe zamu samu kwangilar ɗinkin hular kuma aina zamu samu ? Wallahi zan yi koh da a tsaye koh a durƙushe ne zan kuma koya na kware cikin karamin lokaci ni dai fatana mu samu na kan mu ,"
ta ƙarashe zancen tana mai kamo hannun yagana wacce tayi shiru tana jimamin bahagon halin falmata ,
Toh bari mu fara tuntuɓar kolo koh zata shige mana gaba domin ita ta san masu bada kwangilar saboda ta fimu daɗewa a sansanin ,"
    _____
Saɓanin tunanin su yakaka akan saukin samun kwangilar ɗinkin hula sai ga shi har yau da suke kwanaki huɗu da fara neman aikin kwangilar ɗinkin hular ,amma koh hula ɗaya ta gagara samuwa a gare su , daga ita har yagana ,saboda kowa shakkar basu ɗinkin hular sa yake domin gudun kar su ɓata masa dan babu wanda ya tabbatar da ƙwarewar su , kamar yadda ita kolo tayi suna wurin ƙwarewa da saurin ɗinkin hula hakan yasa take samun kwangila sosai,"
Har dai yanzu da suka gama hakiƙancewa baza su samu ba ,"kolo wacce ita ma ƙwarai ta so su samu ɗinkin koh dan ɗasawar da suke ita da yagana a yanzu ,"
   Mai zai hana toh ku nemi wata hanyar neman kuɗin yagana ? Cewar kolo
  Â
   Kolo kenan ina muka ga jarin neman kuɗi ? kina ganin aikatau ma mun gagara samu .inji yagana wacce duk mamakin halin mutane na rashin taimako ya cika ta,
 Akwai hanyoyin neman kuɗi mana ba iyaka ma mu da muke cikin birnin maiduguri ,"
Tun kafin ta ƙarasa yakaka ta tari numfashin ta toh ai kolo bakya ganin mu a kulle muke cikin sansanin mu ba'a kuma fita sai da dalili mai karfi kamar idan kana saye da sayarwa koh kuwa ka nemi iznin zuwa ganin wani naka cikin gari ka ci sa'a an bar ka
  Idan dai har kun tabbatar kuna son fita domin zuwa neman kuɗi cikin gari ni kuwa zan muku hanyar da koh kwanaki nawa zaku je kuyi ku dawo idan ma kuma zuwa zaku dunga yi kullum kuna dawowa duk zan taimaka muku , ku dai da farko yanzu kuyi tunanin sana'ar yi , idan kun fitan
Cikin zumuɗi yagana tace toh ai ke kolo da kike fita cikin garin ke zaki fi mu sanin sana'o'in da zasu dace da mu kuma wanda zamu samu , ni dai ko ma meye zan yi , haka kuma nasan kawayena ma zasu yi ta furta hakan tana mai maida kallon ta ga yakaka wacce tayi shiru kamar ruwa ya cita , cikin ran ta wasi-wasin fitar su daga sansanin su take da fargabar abun da ka iya zuwa ya dawo a matsayin su na ɓaki da basu san ko'ina ba ,muryar kolo ta katse mata tunani
Toh kun dai ga ana aikatau a gidajen mutanen gari ,"ana bara , ana aikatau a gidajen saida abinci idan baka tare da ƙazanta ,ana yin aikatau har a cikin kasuwanni , idan kana so tashi biya idan kuma kana so biyan wata yanzu haka nima ina wanke-wanke da shara gidan wata mata amma tashi biya muke , kullum naira ɗari biyu take biyana kuma na ci abinci nasha ruwan leda ga kaya kuma tana bani ,
bata tsagaita ba ta cigaba da cewa tun da ku baku da naƙasa zaku iya yin aikatau ita kuma ƙanwar ku tayi bara a bakin kasuwa wallahi zaku yi mamakin kuɗin da zaku samu akalla ɗari bakwai zuwa dubu ɗaƴa a kullum banda kuma kwancen kaya da za'a dunga baku da sadakar ɗanyen kayan abinci ,
Cikin nazari yagana da yakaka suke kallon kallo yayin da falmata tayi jugum ta ƙurawa guri ɗaya idanu tana tunani ,"
  *Toh mana bari mu É—an huta koh* ?ðŸ˜ðŸ˜
  *Mu bar su Yakaka/Falmata/Yagana su yi tunani cikin tsanaki*
 Â
#Comnents
#Vote
#Share
#Fikrh
[6/24, 9:59 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association
*MAFARI.......*
( _hargitsin rayuwa )_
*umm'muaz*
10
Shiri yakaka take sauri-sauri , tana yi tana taya falmata yin nata shirin , cikin mintocin da basu gaza goma ba har sun kammala , duk da dai kayan su na jikin su da suka cire suka sake mayarwa amma bisa ga dukkan alamu da su da kayan nasu sun ɗan samu tsafta domin sun ɗan yi haske , hakan kuwa bai rasa nasaba da wanka da wankin da suka samu damar yi tun a dare jiya bayan da suka tsaida shawarar fara fita neman na kansu cikin gari a ƙarƙashin jagorancin kolo da yagana ,
Kamar yadda kolo ta tsara musu shine su yakaka da yagana kowacce zata fita neman aikatau , yayin da falmata kuma zata zauna a bakin kasuwa tayi bara ,"
Da farko yakaka bata amince da yin barar falmatan ba , turjewa tayi sam tace sai dai falmata ta bita inda zata samu aikin ta zauna ta dunga jiran ta har zuwa lokacin da zata kammala ayukan sai su koma tare , abun da duk ta samu tayi musu hidima tare , kuma abun da duk ta ci , ta bawa falmatan ,
Sai dai ga mamakin ta firr falmata taki ta amince da tsarin ta , ta tsaya kai da fata akan lalle ita ma sai ta nemi hanyar taimakawa kan su wanda kuma hanyar a yanzu É—aya ce ita ce yin bara , idan har kuwa baza ta amince tayi bara ba toh sai dai tayi zaman ta kawai a cikin camp domin bata ga amfanin bin ta da zata yi kawai ta zauna ba .
Ala tilas ta amince mata domin gudun bacin ran ta, da kuma sanin cewa baza ta iya fita daga camp ɗin ta bar falmatan ba , toh ta bar ta a hannun wa ? Ga larurar da take tare da ita , amincewar ta shi ya zama dole sai dai bisa sharaɗin baza su nisanta da juna ba , dole a tsukin gurin da falmatan zata yi zaman barar ta anan ita ma zata nemi nata aikin .
                _____
Yakaka , falmata ku fito mu tafi mana kar muyi rana , kolo ta riga ta gama magana da mai tsaron kofa
      ,"yagana ke furta hakan dai-dai lokacin da take ƙarasowa bakin kofar ɗakin da su yakaka suke ,"
    Gamu nan yagana mun gama shiri sai tafiya ,"
        cewar falmata fuskar ta ɗauke da yalwatatciyar fara'a a karo na farko da yagana ta gan ta cikin farin ciki kwatankwacin wannan , wanda bata raba ɗaya biyu murnar zasu fara dasa harsashin cigaban su ne a karon farko cikin tsananin rayuwar da suka tsinci kansu ,"
  Hannunwan su sarƙe da na juna suke sanya kafafun su domin barin cikin sansanin su da suka wanzu a cikin sa tun ranar da suka shigo birnin na maiduguri , yayin da sashi guda na zuciyoyin su ke cike da fata tare da burin zuwa su nemo na kan su ,gefe guda na zuciyoyin nasu kuma fargaba ne tare da taraddadin yadda fitar ta su zata kasance ,
   Sansanin su a bakin babban titi yake dan haka basu sha wahala ba wurin samun motar bus da take jigilar mutane zuwa kowanne sashi na garin ,
   Kasuwa monday market
    Kolo ta furta bayan ta tsaida wata kwaraɓabɓiyar motar bus da take ɗauke da mutane jingim a cikin ta ,"
     Shiga muje
    Cewar conductor ( karen mota ) wanda ya wangale musu kofar motar ,
   Ni ɗaya ce zan zauna akan kujera su akan inji zasu zauna ,"
     cewar kolo dai-dai lokacin da take shigewa cikin motar domin yi wa kan ta matsugunni ,"
     Wata zamiya kondoktan yayi tare da zabura ya babbake kofar motar ,"
    Nai gamma waɗannan ƙattin ƴan matan har su uku ne zasu hau kan inji kut ? ,"
   Kayi hakuri dan Allah yayana ka taimaka mana wallahi naira ɗari daya ce jal da ni , kuma ni zan biya musu domin su da ka gan su nan koh sisi basu da shi mu ƴan gudun hijira ne , " cewar kolo cikin marairaicewa da karya wuya ,"