Sashe 17
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin razana yakaka ta maida duban ta ga falmata , ganin ƙanwar ta ɗurkushe dafe da kumatun ta duka biyu ya sanya ba shiri ta saki robar ruwan , nan kuwa take ruwan ya tuntsure ya fara malala a wajen , amma koh ta kan ruwan yakaka bata bi ba ta karasa ga falmata wacce take ta shishiƙar kuka ta ɗago ta tare da rungumo ta baki ɗaya zuwa cikin jikin ta .
Falmata meye ya miki ? Dukan ki yayi me ya same ki ? WaÉ—an nan sune tambayoyin da yakaka take ta faman furta su ga falmata,"
Ɗagowa tayi tare da falmatan da ta kama jikin rigar yakakan ta maƙalƙale kamar zata koma cikin ta saboda tsabar tsoro da zafin marukan da ta sha , wanda tun da take ba'a taɓa yi mata makamanta su ba ," sai shishiƙar kuka take ta kasa buɗe baki ta bawa yakaka amsoshin tambayoyin da take jero mata, ita burin ta ɗaya kawai su bar cikin wurin da aka kira da offishi ,"
Da matsanancin bacin rai yakaka ta É—ago idanun ta ta sauke akan fuskar sa wanda yayi kicin-kicin da ita kamar zai kurma ihu hannun sa harÉ—e a kirjin sa yana É—osane daga baki-bakin kofar da alama baki É—aya ma kyamar offishin yake ji a yanzu ,"
Sauke idanun ta tayi ba domin ta ji raguwar bacin ran da ta tsinci kan ta aciki ba a dalilin fahimtar da tayi ya dokar mata kanwa sai dan wani girma tare da kwarjini da ta ga ya yi mata , gefe ɗaya kuma zuciyar ta na tunasar da ita tare da girmama mata girman laifin da kanwar ta ta aikata da ya sa har wannan gabjejen ƙaton ya mare ta.
Ka-kayi hakuri dan Allah bamu sani ba ne , ' shine kalmar da yakaka ta furta a dai-dai lokacin da ƙara taku biyu cikin son ficewa daga offishin ,
Wani sabon bacin rai ne ya taso masa ganin yadda falmata ta wani ƙwaƙume a jikin yakakan ta ƙi ko da duban sa bare ta bashi hakuri duk kuwa da cewa ita ce mai ɗauke da kaso chasa'in cikin ɗari na girman laifin ,
Ganin bai motsa ba bare yayi magana ya sa yakaka tayi zaton koh ya haƙura ne ,' dan haka ta saƙalo hannun falmata suka fara taku da shirin barin wajen , sun zo dai-dai ficewa daga offishin
Cikin bazata ta ji ya fizgo wuyan rigar falmata ta baya da nan take rigar ta bada sautin ɓarr alamun ɓarkewa , wurgi da ita yayi cikin fitsarin ta faɗa ciki ragwaf ,
Mahaukaciya waye zaki bar wa aikin goge fitsarin da kika yi min ? Sunkuya maza ki goge shi tas idan ma kuma zuƙewa zaki yi da bakin ki ki maida abun ki inda ya fito ya rage naki , bukata ta kawai kar na ga damshi ,"
Ke ma kuma ya juya ga yakaka wacce fuskar ta tayi jawur , tare da wani irin mabayyanin bacin rai da har ya sa laɓɓan bakin ta karkarwa , ki sunkuya ki goge ruwan da kika tuttular a nan kafin na kira sojoji su baku horo ,( ya tsora ta su )
Ai kuwa koh dakika ɗaya ba'a ƙara ba falmata ta tattara fiye da rabin zanin ta tare da sanya hannayen ta duk biyu tana laluben daga inda ta fi jin damshin fitsarin ta sanya zanen ta tana guza gurin tare da gogewa da dukkanin ƙarfin ta , idanun ta suna zubar kwallar buguwar da raunin ƙafar ta yayi dalilin wurgi da ita da aka yi , "
Da gudu yakaka ta karaso ta sanya hannayen ta biyu ta ɗauke hannun falmatan , " falmata ki bari zaki yaga zanen ki bari na goge ," ba tare da jinkirin kome ba ta warware ɗankwalin kan ta , " tare da sanya guiwar ta a ƙasa ta fara goge wurin ," lokaci guda hawayen da suka taru cikin gurbin idanun ta suka fara sauka , "
Yakaka zan iya gogewa nima dai-dai lokacin da ta kai hannun ta tana lalubar jikin yakakan , " zan iya... Sauran kalmomin bakin ta suka maƙale lokacin da hannuwan ta suka sauka akan lallausan yala-yalan gashin ƴar uwar ta, Yakaka ina ɗankwalin ki ? A gaban namiji kike zaune babu rufin kai ? Kwance ɗankwalin kan ta tayi lokaci guda ta rufawa yakakan a bisa kan ta , cikin sauri kuma ta sake tattara bakin zanen ta tare da cigaba da goge kafet ɗin tun karfin ta ,
Ji yayi idanun sa na son zowa da ruwa , baya raba ɗaya biyu tausayin su ne ya mamaye ransa , sanin da ya yi yana daga cikin mutane masu raunin zuciya ," a hankali ya fara taku har ya ƙaraso cikin office ɗin ,"ba tare da ya dubi fuskar hamza ba ya ce kai ku tashi haka ku tafi abun ku ya isa , nan gaba kuma ku dunga lura da wurare kun ji koh ?
Da sauri yakaka take gyaÉ—a kai lokaci guda kuma ta fara yi masa godiya ," É—an gyaÉ—a kan sa yayi idanun sa yana kan fuskar falma da shatin marin da ta sha ya kwanta rudu-rudu .
Kamo hannun falmata tayi ta É—ago ta lokaci guda kuma ta zare É—ankwalin falmata daga kan ta tare da rufa mata shi daga kan ta zuwa kafaÉ—un ta,( da yake É—ankwalin na da girma kaÉ—an )
Yakaka ke da me zaki rufe kai ? Ba tare da ta jira amsar yakakan ba ta ɗaura hannu da nufin sake cire ɗankwalin ta mayar mata ,"dafe hannun falmata yakakan tayi , idanun ta na cigaba da son taro ƙwalla saboda kumburar da taga fuskar kanwar ta yayi , ba tare da tace kome ba ta dora hannun falmatan bisa kan ta , anan falmatan taji jikakken ɗankwalin da yakaka ta ɗaura akan ta wanda ta goge wurin nan da shi ," da sauri falmata ta buɗe baki da niyyar sake cewa wani abun ," katse ta yakaka tayi cikin cewa mu tafi falmata ,"
Taku suka fara yi hannayen su saƙale da na juna ," sun zo dai-dai kofar yakaka ta maida duban ta , kan sa sarƙewa idanun su yayi cikin na juna ," kallon-kallo suka yi na ƴan dakiƙai ,'kowannen su zuciyar sa na bugawa da yanayin da take ciki , "
A bangaren sa haushin su duka biyun ne fal a ran sa! Tare kuma da jin takaicin me ya sa suleiman bai bar shi ya hora waɗan nan gidadawan ba son ran sa ta yadda gaba baza su sake gigin yin ganganci makamancin wanda suka yi a yanzu ba , yayin da wani bangare me rangwamen rinjaye yake jin wani abu me kama da bai fa kyauta ba , musamman a yanzu da ya kalli cikin ƙwarar idanun ta masu ruwan zaiba-zaiba ,sai ya ji wannan yanayin kamar yana sake ƙarfafa acikin ran sa ,! Tsaki ya jaa a lokaci guda yana mai kau da kan sa ,
Ga yakaka kuwa ,' lokacin da take kallon ƙwarar idanun sa baƙar shaida take yi masa tare da jin tsanar sa tana mamaye baki ɗayan zuciyar ta tana jin shine mutum na farko da ta fara tsana a cikin rayuwar ta , sakamakon rashin tausayi ƙarara da ya nuna a gare su uwa uba , shi ɗin ne mutum na farko da ya taɓa lafiyar ƙanwar ta abar ƙaunar ta akan kuskuren da ta aikata shi cikin rashin sani ,ba tare da ya dubi naƙasar da ke tare da ita ba ," ɗauke kan ta tayi lokacin da suke sanya kafafun su domin barin ofishin ,
Baku ji ba ," waiwayowa yakaka tayi lokaci guda tana me jin faɗuwar gaba ," a hankali ya ƙaraso hannun sa a aljihu , zare hannun sa yayi daga aljihun ya fiddo da sabuwar naira dubu ɗaya ," ungo ku sayi hijabi ku dunga sanyawa ," ganin basu ƙarba ba ya sanya yayi ƙasa da hannun sa dai-dai hannun falmata ya taɓa hannun nata da kuɗin cikin buɗe muryar sa yace ,"
Ƙarbi mana ,' duk da cewa falmatan ba gani take ba hakan bai hana ta juya fuskar ta inda take jin hucin numfashin yakaka ba ," da alamun neman izni bisa fuskar ta ,"
Mungode Allah ya saka da Alkhairi amma baza mu karbi kuɗin ka ba a wurin Allah muke neman taimako ta hannun gwamnati muna tunanin gwamnati ke da Alhakin ɗaukar nawin mu ,? Dan haka baza mu ƙarbi kudin ka ba mun gode sosai ," cewar yakaka daga haka ta jaa hannun falmata suka ƙarasa barin wajen.
ÆŠan murmushi suleiman yayi lokacin da yake bin bayan su da kallo , lokaci guda yana jin tausayin su yana ratsa shi , gefe guda na ran shi ji yayi kyakyawar tarbiyyar da ya ga alamun ta a tare da su ta burge shi , juyawar sa yayi bayan ya maida kuÉ—in sa aljihu ,"
Amma wallahi hamza baka kyautawa a wasu lokutan ,abun da kayi ga waɗan nan yaran sam bai kamata ba , baka ganin ƙauyawa ne ? Ya kamata ka dunga rage zafin zuciya tare da tausayawa na ƙasa da kai Dan Allah .
Mts toh uba na idan ka gama min faÉ—an sai ka fita ka samo Cleaner ya zo ya goge wurin tun da ka sallami masu É—auke da alhakin gyaran kaji koh waliyyin Allah ?
Yakaka , Falmata wanka kuka yi ne naga jikin ku du a jiƙe haka ? Falmata meya ya same ki haka fuskar ki a kumbure faɗuwa kika yi a banɗakin ?
Ganin sun wuce basu tanka mata ba ya sa yagana bin bayan su tana me sake ƙare musu kallo daga sama har ƙasa ," a ranta kuwa ta fara jin haushin irin halayyar da suke gwada mata a wasu lokutan ,' musamman ma dai falmata ,