Sashe 7
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kwanci tashi yara suna girma Arzikin iyayen su yana sake bunƙasa ,cigaba da wayewa yana sake yawaita , sauye-sauye suna samuwa , yanayi yana juyawa ,
*2005*
yanayin ya juya ta inda ya mayar da kananun yaran nan wasu matan aure wasu kuma samari " inda Æ´aÆ´an sarki Abdoul azezou Baskore suka cika su Goma sha biyar cif-cif , siyama da ita ma take amsa sunan É—iyar gidan ta cikace su suka zama su goma sha shiddah cif cif "safiyyah tana da takwas ,HuÉ—u maza huÉ—u mata "Saratu tana da bakwai shiddah mata É—aya namiji ' , An rufe haihuwar da É—iya mace kamar yadda aka buÉ—e ta da diya macen ,"
Biyamaradi yousoufa tun tasowar sa mutum ne miskilin gaske marar son hayaniya "yana da tsananin tausayi ko ma ace rauni akan mata da yara kanana " , baya shiga harkar kowa a gidan babu me ganin fara'ar sa idan aka ɗauke iyayen sa , sai kuma abokin sa , kuma Aminin sa Tafeedah da ya kasance ɗan uwan sa domin da mai martaba da mahaifin tafeedah da yakasance me riƙe da sarautar ɗan malikin maraɗi , ƴa ƴan wa da kani ne uwa ɗaya uba ɗaya .
Tun tashin su tare suka tashi tamkar ƴan tagwaye ance sai hali ya zo ɗaya ake abota toh abotar Biyamaradi yousoufa da tafeedah ta ƙaryarta hakan domin idan aka ɗauke ra'ayin su da yazo ɗaya akan karatu da aikin da suka yi haɗakar ra'ayi akan sa ,"watau aikin ɗamara " da ya kasance su dukkanin su sojoji ne sai dai shi tafeedah sojan sama ne , saɓanin yarima yousoufa da yake sojan ƙasa .
Bayan hakan kowannen su halayen sa saɓani da na ɗan uwan sa ne , inda Tafeedah ya kasance mutum me barkwanci , surutu da saukin kai, saɓanin yarima yousoufa , hakan ya sa suke yawan samun saɓani akan halayyar juna in da kowannen su yake ƙalubalantar ɗan uwan sa , a ganin yousoufa tafeedah ya cika sakarci da sakewa mutane , yayin da shi kuma tafeedah yake ganin yousoufa a matsayin bauɗaɗɗen mutum miskili marar dadin sha'ani ,
A tsakanin su ɗaya ya kasa sauyawa ɗaya halayyar sa kamar yadda saɓanin halayyar su sam-sam bata taɓa karfin aminci da abotar su ba ,tun suna yaran su har yanzu da suke kan shekarun girma ,basu da abokan da su ka wuce junan su , duk wasu shawarwarin su tare suke yi , sun san sirrin junan su daɗi da rashin daɗi basa rabuwa duk inda dare yayi idan har suna cikin gari ɗaya ,"aiki bai tura ɗayan su wata jahar koh wata ƙasar ba "toh dare yana yi ka gansu tare koh dai a sashin biyamaradi yousoufa koh kuwa a sashin tafeedah da shima yake bangare guda a gidan su da yake baya kaɗan daga shiyar gidan sarki " sosai abotar su me tsafta ce irin wacce take wuyar samu a wannan zamani "
Bayan Tafeedah babu wanda Biyamaradi yousoufa yake so da ƙaunar gani irin karamar kanwar su A'isha wacce ake kira "meram" kasancewar ta (meramar sarki) .
ƙwarai Biyamaradi yousoufa yake kaunar meram duk da cewa kanwar sa ce da suke uba ɗaya , domin meram ita ce ƙaramar ɗiya ga hajiya mama ( Saratu ) a cikin ƴaƴan gidan mata ita ce karama , A'isha"meram" yarinya ce ƴar kimanin shekaru sha uku a yanzu tana aji na uku a makarantar gaba da primary .
Aisha irin yaran nan ne da gatan da suke da shi bai sa sun lalace da rashin tarbiyyah ba , ta samu tarbiyya sosai a wurin uwar goyon ta "Safiyyah" uwa ga Biyamaradi yousoufa , hajiya umma "kamar yadda ƴaƴan ta suke kiran ta" ita ta ɗauki Aisha tun daga yaye wanda hakan yana da nasaba da ƙaunar da ta ga ɗan ta mafi soyuwa agare ta yana yi wa kanwar ta sa da tun daga lokacin da aka haife ta ya ƙyalla ido ya ganta ,Allah ya dasa masa kaunar ta ciki ran sa fiye da duk sauran ƴan uwan sa ciki har da waɗan da suke ciki ɗaya da shi da su .
Lokacin yana matakin farko a jami'ah ai kuwa ya mayar da sashin mama wurin yada zangon sa a duk lokacin da ya dawo daga ɗaukar darasi haka zai kwace aisha daga hannun masu rainon ta yayi ta faman hidima da ita, hakan sam baya yi wa hajiya umma daɗi ganin yadda ɗan ta ya tare a sashin da a da kafin haihuwar aisha sai yayi shekara ma bai taka kafar sa bakin sashin ba " hankalin ta ya tashi akan sanin da tayi cewa garin su baya jiƙuwa a ƙoƙo ɗaya tare da saratu"hajiya mama "
Baza ta iya hana yousoufa zuwa sashin hajiya mama kai tsaye ba kasancewar ta san shi kaifi ɗaya ne ,miskilin gaske da ba'a iya sauya masa ra'ayi ta daɗi , hakan ya sa ta bi hanyoyin da take ganin zasu taimaka mata ta dakatar da ɗan ta daga shiga sashin hajiya mama domin tana gudun ta janye mata ɗa tsaf "sanin halayyar saratu "(hajiya mama) " da tayi na tsantsar kissa da siyasa tare da hilatar mutum ya so ta a dole karshe kuma ta cuce sa "macijin sari ka noƙe ce " ( cikin rashin sanin hajiya umma aikin gama ya riga ya jima da gamawa )
Dan haka tayi mata shigar sauri ta bi duk hanyoyin da take da damar bi ya haɗu kuma da ita ke jaan ragamar gidan ta ɗauke Aisha can-cak daga wurin mahaifiyar ta a lokacin tana shekaru biyu a duniya ta dawo sashin ta baki ɗaya , ai kuwa murna gurin yousoufa ba'a cewa kome " yayin da hakan da tayi ya baƙan ta ran hajiya mama sosai amma sai ta boye bacin ran ta. (sanin da tayi ta riga ta gama rarake ƙasan hajiya mama )
Cigaban labari .
Yana shiga tamfatsetsen (palourde-parlour )falon nasa ko kafin ya karasa zama akan É—aya daga cikin kyawawan fararen kujerun da suka sake haskaka falon wayar sa da take cikin aljihun sa ta hau ruri .
Ciro wayar yayi daga cikin aljihunn sa tare da tsira mata ido tamkar me nazarin ta ,har sai da ta kusan tsinkewa tukun ya É—aga gami da yin sallama ya É—ora da faÉ—in "Comment vas-tu aujourd'hui princesse"?
Daga dayan bangaren aka amsa cikin wata narkakkiyar murya " je vais bien Mon amour comment va le travail"?
Ya amsa da Alhamdulillah daga haka suka ci gaba da hirar da ake yin ta cike taf da kasaita daga dukkanin bangarorin biyu da shi da wacce ga alamu budurwar sa ce .
Idan ɗaya ya furta kalma sai an biyo bayan wasu ƴan ƙananun daƙikai (seconde -seconds) kafin " ɗayan ya bada amsa , inda daga baya ma ya koma budurwar ita ke jaan ragamar hirar, shi daga yayi murmushi sai yace eh ko a ah.
Har dai zuwa lokacin da ya sako mata zancen tafiyar sa akan aikin sa har na tsawon lokacin da yake zaton zai iya kaiwa shekara .
Nan take ta katse shi tun ma kafin ya karasa yi mata bayani cikin tashin hankali take tambayar sa akan ina lamarin bikin auren su ya kwana ? Wanda ake sa ran zuwan ranar da aka yanke nan da Æ´an wasu watannin da suke gaza da uku "lokacin da zata kammala karatun ta" ?
Cikin jin haushin tarar numfashin sa da tayi wanda yake ganin kaf duniya yana iya kirga mutanen da suka isa yi masa haka ,yace ke dakata MAIMOUNA lamarin ayki matsayin shi ya wouce douk yadda kike tounani don haka ki ajiye komi a guefe har sai bayan na cimma matsaya bisa aykina.
Ko kafin ya gama bayani budurwar da aka kira da maimouna ta fara shishiƙar kuka gama bayanin sa yazo daidai da fashewa da kukan ta bata ko kuma saurarar sa ba ta kashe wayar ta ,
Ta barshi riƙe da kan waya a kunne , ɗan jim yayi yana son fahimtar abun da ya sanya ta kuka cikin kalmomin da ya furta ,?
Rashin gano dalilin ya sa shi ɗaga kafaɗun sa biyu cikin nuna alamar rashin damuwa ya miƙe tare da nufar daya daga cikin fankama-fankaman ɗakunan da suke cikin falon nasa yana shiga ɗaki ya nufi ƙaton window ɗakin gami da buɗe sa a take ƙamshi damina da wata sassayan iskar maraice da ta fi ta ac da yake ɗakin dadi ,ni'ima da sanya nishaɗi ta buso zuwa cikin dakin .
Rage kayan jikin sa yayi tare da nufar bayi da alamun wanka yake da niyyar yi ,sai dai wayar sa da ya ajiye gefen gado ta É—an jaa hankalin sa sakamakon hasken da tayi ,É—an guntun murmushi yayi ganin sunan princesse da alamar sako a fuskar wayar ,ba tare da ya É—au wayar ba ya faÉ—a bayi domin yin wanka.
Yana kammala shirin sa ya fito falo jikin sa sanye da uniforme riga da wondo me dabbare-dabbaren kore , ruwan kunkumadi, ruwan madara, da kuma jaa Wanda ko ba'a faÉ—i ba za'a san kakin soja ne .( Tenue Saharienne ).
Da sallama ɗauke akan harcen sa ya sanya kai cikin katafaren Palourdes (falon) mahaifiyar sa wanda yake kama da ɗakin taro "hall" dakatawa yayi daga gefe ya sunkuya tare da kwance igiyoyin jikin takalman sa da suke ɗaure gam-gam da kafar sa har kusan ƙwarin sa ,
Wucewa yayi niyyar yi (zuwa ciki wurin umma ) bayan ya amsa gaisuwar jakadiya wacce ya tarar tana zaune daga gefe a cikin palourn amma sai jakadiyar ta dakatar shi cikin cewa "Ranka ya dade biyamaradi " yanzu kuwa nake shirin zuwa sashin naka "ta furta hakan tana me satar kallon bayu uku da suke ta faman goge-goge da ƙwal-ƙwale cikin palourn daga can geufe ( umartar su tayi da su kauce su basu wuri ).