← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 269

Sashe 87

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Ganin sa ya janye daga kan agogon ya maida kan ta , tare da ɗan ƙara sautin muryar sa ,
   Wannan agogon na waye ne ??
A firgice ta ɗago kan ta jin kamar ya mata tsawa , matuƙa take shakkar sa tare da gwada yi masa biyayyah

Ba-ba-baba Agogon - agogon Baba ne !
  Ta harhaɗo kalaman da suka fito a baibai ,"  idanun ta na yin ƙwalƙwal .

Agogon Baba ?

  Hamza da Falmata suka haɗa baki wurin tambayar ta !
wacce take ƙarasowa wajen da lalube daga cikin ɗakin saboda jin tashin muryar doctor hamza domin ta gaishe shi ,

Agogon Baba ? Yakaka ina agogon Baban mu ? Daman Baa yana da agogo  ,
      Falmata ta furta hakan cikin tsananin murna kasantuwar ta mai matuƙar ƙwalafacin iyayen ta , hakan ya sa ta ma manta da abun da ta fito yi ,"gaishe da doctor hamza ," ta himmantu wurin son a bata agogon ta riƙe , doctor hamza ne ya ɗaura mata agogon bisa hannun ta ,

bai sake cewa kome ba ya juya yana barin falon zuciyar sa cike da wasi-wasi akan kalaman da yakaka ta furta na dangana wannan tsadadden agogon ga mallakar mahaifin su ,

A sanyaye falmata ta É—ago kai daga barin shafa agogon da take yi ta saita idanun ta a inda take zaton yakaka na zaune ,
    Yakaka kika ce wannan agogon Baa ??
    Da ido yakaka ta kafe ta kamar tana son ta gyara mata sokuwar ƙaryar da tayi ," wanda ta hango rashin yarda da zancen nata ƙarara a idanun doctor hamza
   Miƙa hannu tayi ta zare agogon daga hannun falmata ,
   Falmata muje ɗaki na kwanta ki ɗan danna min kafafuna ciwo suke min ,

  Da sauri ta amsa da
  toh sannu yakaka

Tun daga ranar yakaka take koƙari wurin boyewa kowa duk wani abinda ya shafi soyayyar da take yiwa youssouf ciki kuwa har da Falmata ,

Da samy baby kaɗai take hirar sambatun soyayyar youssouf , wacce take daɗa ƙaimi wurin shiryawa yakaka gadar zare , tare da bugun cikin ta a koyaushe tana jin tsakanin ta da doctor hamza ,

irin kulawar tare da hidimar da yake yiwa yakaka yake sake bata tabbacin zaton ta gaskiya ne , doctor hamza son yakaka yake , soyayyar kuma mai tsanani ta aure ,

wanda a koyaushe idan ta tuno sofi da irin mahaukacin son da take yi masa da irin mummunan alwashin da ta sha a kan sa , sai taji abinda take kokarin yi da nufin raba tsakanin sa da yakaka dai-dai ne, a ganin ta taimakon yakakar zata yi , har ma tana danganta yunƙurin ta a matsayin CETON RAI ," 

Lokacin da yakaka ta shiga watan haihuwar ta hamza ke sanar da ita daga wannan satin zata daina zuwa makaranta , baza ta dunga zuwa ko'ina ba daga awu , sai dai ta fita motsa jiki da dare ,

Da farko ta shiga damuwa , da hukuncin da ya yanke na hana ta zuwa makaranta ganin cewa a makarantar take samun damar haÉ—uwa da samy baby duk lokacin da samy baby ta so ,"

Amma lokacin da ta sanar da samy baby sai ta ga bata wani damu ba , suka cigaba da hirar su da fiye da rabin hirar maimaici ne tare da tisawa akan yadda tsarin samy baby yake da yadda kome zai kasance , har zuwa gamuwar ta da muradin zuciyar ta kamar koyaushe yakaka ke ƙarasa hirar da sambatun yadda haɗuwar tasu zata kasance da youssouf da ɗokin zuwan ranar ,

Bayan gama hirar su , sai samy baby ta ciro ƙaramar wayar ta , ta kamo hannun yakaka ta danƙa mata ,"
    Zamu cigaba da tattaunawa akan waya yaks , saboda kin ga bana son mutanen gidan su san da alaƙar mu domin kar a zarge ni har a bibiye ni bayan kammaluwar kome , ki tabbatar babu kowa a wurin a duk lokacin da zamu yi waya , ki dunga min flashing idan kina son magana da ni , sannan kuma daga mun gama magana ki dunga kashe wayar , kar ki bari kowa ya san da wayar ,

Idan chaji ya kusa ƙarewa ki sanar da ni , ni zan san hanyar da zan yi na karɓi wayar nayi mata chaji ,"

Abu na ƙarshe shine kar ki manta da tsarin mu ko cikin dare kika ji ciwon haihuwa na zama mutum na farko da zaki fara sanarwa kafin kowa , kin san dai shirin mu zai fara ne daga haihuwar ki ,  ai kin gane ko ?

  Naji anty samy kuma bazan manta duk tsarin da kika shirya min ba , nagode sosai da taimakon da kike min a kullum tunda muka haɗu , Allah ya saka miki da Alheri ,!

Murmushi mai wuyar fassara samy baby tayi,
    Ameen yaks ,

Tun bayan da doctor hamza ya sawa yakaka dokar hana fita unguwa , ya zama kullum da dare tare suke fita ita da Rahima , da misalin karfe 8pm , su É—an yi tattaki su zagaya unguwar zuwa 9pm sai su dawo gida ,

Ƙwarai yakaka take jin daɗin fitar tasu saboda yadda a kwanakin take jin nawin cikin kafafun ta duk sun ɗan kumbura , ga kwonkwason yana mata tsuku idan ta daɗe ,"

Tare suka fito da Rahima daga sashin su , Rahimar tana ta mitar Yakaka ta katse mata kallon TV da take ta dame ta akan tazo su fita ta raka ta motsa jiki ,"
     Yakaka ni fa yau baza mu yi wani nisa ba , zamu dawo kin ga dai garin da sanyi ma , ga duk hazo ya rufe sama , ni ba dan kin nace ba ma wallahi yau baza mu fita motsa jikin nan ba duk ƙura ta bi ta shigewa mutum hanci ta sa mura ,"

  Gyara zaman burmemen hijabin ta yakaka tayi tana murmushin jin daɗi domin tun basu yi nisa ba ma ta fara jin kafafun ta na warwarewa ,"
     Ni kuwa Rahima daɗin yanayin ma nake ji , kiyi haƙuri kin san ba laifi na bane yaya dakta ne ya ce kar na dunga fashin fita motsa jikin ,"

   Doctor hamza ne ya shigo ta ƙaramar ƙofar gidan jikin sa sanye da ƙananan kaya ya rufe bakin sa da hancin sa da abun tare ƙura ,"Mask ,"

Idon sa ya sauke a ƙan su lokacin da suke ƙarasowa ,"
     Gaishe shi suka yi ya amsa musu ya ɗora da
    Za'a je motsa jiki ko ?
Da sauri Rahima ta tari numfashin sa , big bro daman an bar zuwa motsa jikin nan yau sai gobe , ji fa garin duk hazo wallah ,"
       Rahima dan Allah kiyi haƙuri muje yakaka ta ce , tana marairaicewa ,"
      Cuno baki Rahimar tayi taƙi cewa kome , "
     Murmushi hamza yayi ,
   Koma ciki abin ki Rahima yau an ɗaga miki ƙafa sai gobe ,
     Da sauri Rahimar tayi juya tana dariyar murna , dan kar yace ta dawo ma har da ɗan gudun ta , ta ƙarasa shigewa sashin su , "

   Ganin sa ya mayar kan Yakaka , wacce ta sunkui da kai tana wasa da hannun ta ,"
      Noori
  Ya ƙira ta
   Na'am
  Tace tana ɗago kan ta ta dube shi kafin ta sake sunkui da kan ," ba wani sanin ma'anar sunan tayi ba , ita dai tasan yakan ƙira ta da kalmar a irin lokuta haka da suke su biyu kaɗai !

         Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji yace mata ,
  Bismillah mu tafi ,' ya buɗe mata ƴar ƙaramar ƙofar
  Tare da shi zan tafi ?
Ta tambayi kan ta lokacin da take sanya ƙafafun ta da ta cusa wasu ƴan takalman roba na mata ," kumburin da ƙafar ta ta tayi ya sa takalman suka ɗan kama kafar ,"

    Ta ina-da-ina kuke bi idan kuka fito ?
      Ta nan muke bi tace da shi da ƴar siririyar murya ,"
    To yau ba nan zamu bi ba , zo mu bi ta nan , ya ce mata haka yana nuna mata hanyar da tayi baya wacce take da rangwamen mutane da hayaniya ,"
   Ba musu ta bishi ,
  Suka fara tafiya sannu ,sannu ,  rabin hankalin sa baki ɗaya na ga inda take sanya kafafun ta , "
    Ɗan takaitatcen shiru ne ya biyo bayan fara tafiyar ta su ,"
   Kafin Hamza ya lalubo hirar da yake ganin zata fi armashi ga yakaka ,"
    Noori , ya ƙira ta ,"
    Wanne suna kike tunanin zamu sawa baby ?
     Yana hango lallausan murmushin da ya bayyana a fuskar ta da taimakon hasken fitulun bakin hanya, kafin ta ɗan sunkui da kan ta ,"

    Nima ban sani ba yaya dakta , kawai duk wanda ka zaɓar mata ,"
 
  Ɗan murmushi yayi kafin yace ai uwa ita ce mafi soyuwa ta zaɓarwa ƴaƴan ta suna ,
    Ni mata ta duk ita zata dunga zaɓarwa yaran mu suna , dan haka mu fara da wannan babyn , ki tuno suna mai kyau da asali a addini da za'a sa mata , "
  Kasaƙe tayi ita a dole tana son tuno da sunan ,!
     Mama ?
tace masa da sigar tambaya ,"
    Mama! 
shima ya maimaita yana kallon kwarar idanun ta ,"
    Eh
tace da shi tana sunkui da kai ,"

Toh kin samar mata da laƙabi ," ya furta hakan yana mai yi mata murmushin da ke bayyana sautin sa ,
Chapter 87 · 0% Book details