← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 187 OF 269

Sashe 187

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"duk baki san mou ba , a yadda ɗan'ouwansa kuma abokinsa ya buncika mouna ya amre ki ne tare da ɗiyar yal ouwakki da ta haifa ba tare da sun yi amre da shi ba shigiyar ɗiya, ya zo nan ya ɓoye kou , yana rayuwar sirri da kou , kin raba tsakanin sa da matayensa , kin ɗauke hankalin sa daga aikin sa , bashi da watta hidima sai taku ke da ɗiyar da gurɓatatciya ce shin yarinya baki gudun jefa rayuwarki ga hargitsi maigirma ?

Cikin wata irin murya Falmata ta ɗamƙi hannun Yakaka ta jijjiga ta tare da cewa

" Yakaka kiyi magana mana , kina ji fa an ƙira Mama shegiya ,

shiru Yakaka tayi tana jin yadda wani abu ya zo mata ƙahon zuci ya takore , ko motsa laɓɓanta ta gaza ,

Juyawa tayi wajen da Youssouf yayi suman zaune akan shamtar sa da Adda Ammi tayi ,

"Baban Mama ka ji wai Hajiya yayar ka tace Mama ba 'yar aure bace , ka faÉ—a musu gaskiya yadda ka faÉ—awa Baba prof lokacin auren mu dan Allah,

Hawayen da suka cika gurbin idanunta suka sauƙo , ta matso gaban su ,

" Hajiya dan Allah ko da ni baza ku karɓeni ba kuyi haƙuri ku karɓi Mama kar ku ɓata mata asali , Mama yarinya ce marar lafiya dan Allah kar ku ....

Tsawar da Ubbo ta daka mata ya sanyata yin shiru ,,

"ke yarinya raba mu da ƙazanta ,yadda kuka zou tare hakka zaku kouma tare , mu karɓi ɗiya mu tai da itta ina ? Muyi me da itta ? Mu 'yan nasaba ne , ɗiyan asali ɗiyan halak ba zamou taɓa yadda da zouwanta cikin mou ba ai daman ɗiyan zina na uwattai ne , can zaku koma da itta ,

Da rishin kuka Falmata ta miƙe tsaye ta tsaya akan su ,

"ƙarya kuke yi Yakaka ba ƴar iska bace bata taɓa zina ba , dan haka Mama ba shegiya bace ,

Juyawa tayi ta ɗago Yakaka da ruwan hawaye ya jiƙa mata gaban riga , ko kusa bata san wannan ranar da zasu shiga tozarta ita da "yar uwar ta a sanadin kuskuren da ta aikata zata zo ba ,

Kuma bata so ba wasu suka riga ta sanar da Falmata ta irin hanyar da ta samar da Mama ba ,

jijjigar da Falmata ta yiwa kafaɗunta da ta riƙe duk biyu shi ya tsorata ta ,

"Yakaka kina jina ki je gaban su ki faɗa musu ƙarya suke miki sharri suke muku ke da Baban Mama ba zina kuka yi ba , ki faɗa musu Mama ba shegiya bace , ki ce musu ƙarya suke yi , Mama ƴar halak ce kamar su ,

Ta karasa zancen tana fashewa da kuka ,

Kukan da ya hargitsa duk wata guntuwar nutsuwar da ta ragewa Youssouf , ya miƙe a ɗimauce , lokacin da muryar Yakaka ya ratsa wajen ,

" Gaskiyar su ne Falmata , Mama shegiya ce , ba muyi aure ba ni da Baban Mama muka haife ta ,

tamkar an harbi ƙwaƙwalar ta haka Falmata ta ji zancen , sai ta wara idanun ta fes akan fuskar yar uwar ta muryar ta babu ƙarfi irin na ɗazu illah tsantsar tashin hankali ta ce 

" Yakaka tsoron su kike ji ? Dan kina tsoron su shine kema zaki ƙira Mama shegiya dan kawai bakya son ta ? ,

sai ta tunkuɗe ta baya  , ta wuce kai tsaye wajen Youssouf da ƙafafun sa ke karkarwa ta tsaya daf da shi ta ɗaga kai tana hangen farar fuskar sa 

"Baban Mama ka cewa Yayar ka ƙarya take ,  ka faɗa musu kai mutumin kirki ne bazaka cutar da Yayata ka ɓata asalin Mama ba ? Ka faɗa musu ba zaka yi zina da Yayata kuma ka aureni ba .

hannun sa dake rawa ya miƙa ya rike kafaɗar ta  , sai dai hannun sa yana sauƙa a jikinta ta doke hannun da wani irin matsanancin fushi , tace "kaima zaka ce gaskiya ne ? Eh ?

Ubbo wacce abunda Falmata take yi ya fara bata haushi a ganin ta tsaurin idanun Falmata ya wuce iyaka da har take ƙaryata su kai tsaye ,ta kuma tsare Youssouf ɗin a gaban idanun su  dan haka sai ta miƙe tsaye ta ƙaraso wajen ,

Ta fuskance shi tana cewa
" Youssoufa menene haka nake kallo ? Macce ke tsare gaban ka Youssoufa ? A gaban ka take ƙaryata Adda Ammi ? Ka sake ta Youssouf a yanzou , ka sau amrenta nace wacece itta da bata wuce bayun mu ba ?

Da dukkanin Fushin sa ya juya gare su   muryar sa da Amo mai ƙarfi laɓɓansa na karkarwa yace.

"Adda Ammi, Adda ubbo , Tafeeda ,  domin Allah ku tafi abunku , ku fita dagga Rayuwa ta , Rayuwata tawa ce ni ɗaya ba tare da ku ba , duk kome nayi a cikin ta domin kai na ne ,

" ba zan saki Matata ba haka kouma ba zan rabu da ɗiya ta ba , naji ban samar da Mama ta halastatciyar hanya ba  , amma ina ƙaunarta fiye da yadda nake kaunar kaina , ni nake da laifi Mama ita wankakkiya ce tsaftatatciya ,

"ba zan danganta Mama da ku ba asalinta ya tsaya ne daga kaina ni kaɗai , ba zan raɓa ta da ku ba ,  samuwar Mama a wajena wani kaddara ne Maigirma daga ubangijina  ,don Allah Adda ku tafi nace ,

"to maras kunya fitsararre , idan kai ka zare mu dagga rayuwar ka mou ba mou fita ba , asalin mu gouda da kai sannan akwai hakkin 'yan ouwantaka da na iyayen mu akan ka  ,

Ubbo tace haka ,

Bata saurare shi ba ta juya ga Falmata wacce ta durƙushe a wajen tana wani irin kuka marar sauti ,

"ke yarinya tunda baki da alkunya  ku tattara yanzou ku fita zouwa wani wajen cen ,  ku tafi kuyi nesa da ƙanina shi ba tsaran amren kou bane ɗiyan matsayitta masu gajeren assali ƴaƴan titi....

Kalamanta sun ƙona zuciyar Yakaka , dan haka ta tako gabanta tana jin duk wata shakkar su na ficewa daga ranta tace ,

" Ya isa , Ya isa nace Ya isa kar ki zagi iyayen mu , da basa raye a duniya ,  ko daman baki faɗa ba Falmata ba zata cigaba da zama da azzalumin ɗan uwanku ba , wanda tushen sa da asalinsa tare da girman da kuke fariya da shi bai katange shi ba daga aikata alfasha , kamar yadda kuka faɗa ya zama dole ya saki ƙanwata ya kuma ba ni ɗiya ta ,

" Nima bazan taɓa yadda ta zauna atare da ku ba , idan kun so a yau ku ɗora shi ya zama sarki , har abada Mama baza ta sake nuna shi a matsayin Uba ba ,

Takawa tayi ta ƙarasa gaban Youssouf , idanunta jazir da ɓacin rai tace

" ka saki auren Falmata na sake maimaita maka , ka kuma fita daga rayuwar mu Youssouf ...

Assalamu Alaikum masu karatu , da fatan duk kuna lafiya ??

Wannan shafin kachokam ɗinsa tukuici ne ga duk wasu masoyan MHR a duk inda kuke alherin Allah ya iske ku ,  ina ƙaunar ku domin Allah 😍❤

Nagode
[11/29/2019, 1:17 PM] +234 806 600 1491: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )

Umm'muaz

43

Ƙiran wayar Youssouf da aka yi ƙarar ita ta ratsa shiru mai ɗauke da tashin hankalin da ya biyo bayan martanin Yakaka ,

Baya cikin nutsuwar sa ya dubi fuskar wayar da take riƙe a hannunsa , ganin wacce take ƙiransa ya sa zuciyar sa ta tsinke ,

Hannunsa na rawa ya ɗaga ƙiran wayar da ya zarce da sanya ta a hands-free batare da ya ankara ba ,

Muryar Hajja ciki kuka ta karaÉ—e falon , da take cewa

"Babban soja , ku zo Dan Allah, ku zo wajen Mama ku ga jikin nata , jikin Mama babu daÉ—i...

Rige-rigen ficewa daga falon aka yi tsakanin Youssouf ,Yakaka da Falmata  da babu wanda ya saurari kansa bare waninsa burin su kawai su isa wajenta ,

Kuma a tsakanin Falmata da Yakaka babu wacce ta nufi motar Youssouf da ya shiga ya tayar dukkanin su biyu kai tsaye mafitar gidan suka nufa ,

Suna fita ya sha gabansu da Motar ,"ku shigo ,
  Yace da wata irin murya

Dukkanin su a lokacin ganin Mama shine burin su , dan haka suka shiga motar ya jaa da gudun gaske ,

A lokacin hawayen fuskar Yakaka da Falmata sun ƙafe kamar yadda yawun bakin su ya ƙafe ya daƙile fitowar wata kalma daga gare su , bayan addu'o'i babu abunda kowannen su yake yi a zuciya

Suna ficewa daga layin gidan motocin da suka yi jerin gwano su kimanin guda biyar suka shiga layin .

Gudun da yake yi ya wuce ka'idar tuki , kiyayewar Allah kaɗai ta kai su asibitin , ba inda ya kamata ya ajiye motar ya ajiye ba , bai ko lura da securities da suke masa magana ba , ya fito daga motar sauƙar ƙarfar sa akan titin da ya ɗau zafin rana shi ya ankarar da shi cewa fa ko takalma babu a ƙafafunsa ,

da gudu-gudu suka nufi É—akin da suka san Mama tana ciki suna rige-rigen kutsa kansu ,

Turus suka yi ganin babu kowa akan gadon nata , da sauri ya fita suka bi bayansa , ma'aikaciyar jinyar da ya fara cin karo da ita zata wuce ya tambayeta ,"ina É—iya ta ?

Ta san shi sosai a saboda yadda suke yawan zaman asibitin da kuma kasancewar sa babban Mutum , sai ta nuna musu É—akin da aka mayar da Mama wanda yake daga ciki sosai ,

Bai saurari me zata sake faÉ—i ba ya nufi inda ta kwatanta masa da sassarfa ,

Bankaɗa ƙofar ɗakin yayi ya danna kai su Yakaka suna bin sa ba tare da sun bi ta kan Hajja wacce take tsaye daga bakin ƙofar tana sharar hawaye da gefen mayafin ta ba ,

Shigar su ya zo dai-dai da lokacin da likitan yake zare trach tube ɗin da yake fuskar Mama ,
Chapter 187 · 0% Book details