Sashe 163
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sallama suka shiga gidan Amne , tana zaune kan barandar ta tana ƙunsa lalle a ƙafafunta da basa rabuwa da ƙunshi ,
Tayi mamakin ganin su saboda Rahima bata sanar da ita zuwan nasu ba ,
ta tare su da fara'a tana yiwa baƙi barka da zuwa , idanunta da hankalinta baki ɗaya akan yakaka .
Bayan sun gaisa ta dubi Rahima ,
" aina kika sake samo min mai kama da Rahima ta ? Da ace shekaru basu jaa dayawa ba zan iya cewa Rahima ta ce wannan ,
 " dariya Rahima tayi , Amne baki gane ta ba ko ? Yakaka ce fa , 'yar gudun hijarar da suka zauna a gidan mu shekarun baya da akayi zaton ta rasu wajen haihuwa ?
duk da ba wani jimawa tayi da yaran ba amma sunan su ya tsaya a ƙwaƙwalwar ta ,
" Yakaka ke ce ?
 " ni ce Amne ,
" Alhamdulillah ashe Yakaka kina raye ? Ina kika tsaya tsawon lokacin nan ? Ina ƙanwar ki tare da 'yar ki ?
 hannun ta ta ɗora akan na Amne da ta miƙo mata su , fuskar ta ɗauke da murmushin jin daɗin zallar ƙaunar da ta hango a idanun Amne ta matso kusa da ita ,
"Falmata su na America wai .
Hajja tace ,
" Wai ne ma ? ai ya wuce wai .,
Amne bata tsananta tambayoyi ba ga Yakakar domin ta bata damar sakewa ,Â
Lallen da Amne take sawa ta karɓa , tare da cewa
" kawo na sa miki Amne .
tana murmushi ta miƙa mata 'yar robar da lallen ke ciki , ta shiga sanya mata sannu kan hankali ,
da sauri Rahima tace
"Daman kin iya lalle ne Yakaka ?
tana murmushi tace ,
" ko ban iya ba zan koya a ƙafar Amne .
Hajja da Amne suka cigaba da hirar su ,
zuwa lokacin da Rahima tace ,
" Yauwa Amne ki nunawa Yakaka Hoton Khaalty Rahima da kike cewa suna kama Yakaka tana son ganin ta...
"eh Amne ina son ganin Khaalty Rahima , Yakaka ta furta hakan cike da É—oki ..
Assalamu Alaikum masu karatu maza da mta , ina miƙo sakon gaisuwa ta tare da fatan alheri , ɗauke da yabawa bisa ga yadda kuke bin littafin nan cike da bani ƙwarin guiwa nagode ƙwarai da gaske Allah ya bar so da ƙauna ( sunan wani littafi 😂 ) sharhin ku a fejin da ya gabata ya min daɗi matuƙa da fatan za'a ɗore da haka ? .
Ghost readers muna nan da ku , za'a ji kan mu watarana .
😡
Nagode .
  Â
 Â
 Â
Â
[10/26, 11:28 PM] +234 706 503 6187: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )
Umm'muaz
37
Cike da zumuɗi Yakaka ta karɓi wani ƙaramin envelop ɗin da Rahima ta ɗauko mata daga ɗaki tana cewa
" Yakaka ga hoton Khaaltƴ Rahima duba ki gani, ita ce takwarata ai ina kama da ita ko ? .
Da murmushi bayyane kan fuskar ta , ta zaro hoton bayan ta goge hannun ta da yake da ɗan danshin ruwan ƙunshi .
Ƴar ƙaramar budurwa ce a jikin hoton na farko da baza ta wuce shekaru sha huɗu zuwa sha biyar ba , fara ƙal tamkar baturiya , ƙibabbiya 'yar dumur-mur jikinta sanye da doguwar rigar iya ƙwauri mai guntun hannu irin shigar su ta shuwa ,kanta ba ɗankwali sai manyan kitson guru da aka mata gwammon sa a ƙeya ,
" wai Masha Allah Rahima mai sunanki ta fiki kyau gaskiya ,
Ta furta tana 'yar dariya kafin ta zame hoton na bayan sa ya bayyana da bai kai wancen a tsufa ba domin a wannan ta ƙara girma ta zama budurwa da a lokacin zata iya kaiwa shekaru sha bakwai , da alama a makaranta ta ɗau hoton ganin jikinta sanye da uniform ,
Tsam , tayi tana ƙurewa cikakkiyar fuskar ta kallo da take dariya , tamkar dai tana rikiɗe mata zuwa fuskar da tayiwa sani na haƙiƙa ,
"fuskar wa ?
Ta tambayi kan ta da kan ta .
"Fuskar maman mu ," babu shakka dariyar ta da zubin haƙoranta irin na maman mu ne , sai dai maman mu bata da jiki da kyaun wannan mai kama da turawan,
Tunanin ta ya katse lokacin da ta tsinkayi muryar Amne wacce ita ma ta kafe ta da ido tana nazarin yanayin da take hangowa a tare da ita ,
" Yakaka ko kin san ƙanwata Rahima a wani waje ne ?
Kallon Amne tayi kamar zata ce wani abu sai kuma tayi ɗan yaƙe , tare da girgiza kanta lokacin da take ƙoƙarin mayar da hotunan cikin gidan su ,
" A ah Ban san ta ba Amne ,"
"Allah sarki , Rahima kenan ƙanwata da muke uwa ɗaya uba ɗaya jal a duniya , Yaa Allah ka san halin da na wanzu cikin sa tsawon shekarun nan akan rashin Rahima , Allah ka dawo min da Rahimatullah , ka sa muna da rabon sake ganawa a duniya .
"Amin Amne ,
suka amsa mata su duka fuskokin su na bayyana alhini , musamman Yakaka wacce ta shiga wani irin hali na ruɗani da ganin hoton khaalty Rahima ya jaza mata .
Ƙwarai fuskar ta tsaya mata a zuci da cikin tunaninta , Babu wadatar nutsuwa na sosai a tare da ita suka ƙarasa yinin su zuwa gefen La'asar suka kama hanyar komawa gida ,
Rahima ta dubi Yakaka bayan mai adai-daita ya sauƙe su a daf da ƙofar gida ,
"Yakaka ya naga duk kin yi wani iri , akwai damuwa ne ? Kafin mu fita a gida ba haka kike ba ,
Kafin Yakaka ta amsa Hajja tayi charaf ta amshe zance ,
"Ahaf zai wuce batun wannan ɗan banzan , ɗan hamsin yake ko ɗan daudu ? Idan har kika ce ƴar huɗubar wofin nan da ya wassafa miki zaki ɗauka ki aza a rai to kuwa kin kama kumfar teku , domin wannan da kike ganin sa rabon sa da alasambarka tun kwanansa bakwai ran suna , babu Alheri a tare da shi ko na aninin kobo atoh .
A ɗan kaikaice Yakaka ta dubi Hajja zata yi magana , aka buɗo babbar ƙofar gidan , Doctor Hamza ya turo kan motar sa , kallo guda ya yiwa gefen da Yakaka take ya ɗauke kan sa ,
Da sauri Yakaka ta wuce tana gyara zaman hijabinta , ta bar Rahima da Hajja suna gaisawa da shi , inda yake tambayar su daga ina suke ??
Suka sanar da shi daga gidan Amne suke , sosai ya ji daɗi tare da tambayar su yadda suka baro ta ? Suka amsa masa da tana lafiya ƙalau ,
Daga haka ya wuce yana satar kallon madubin motar sa inda ya hango Bayan Yakaka tana tafiyar ta a hankali dogon hijabin jikinta da yake kusan taɓa ƙasa bai boye salon takun tafiyar ta irin na barewa ba ,
ÆŠauke kai yayi lokacin da yake dai-daita kan motar sa ya hau titi ya cilla zuciyar sa cike da zullumin tunani kan inda ya nufa ,
Kai tsaye ya tasamma unguwar da aka bashi tabbacin anan gidan da matar nan da yake zaton innar sa ce take aiki , duk kuwa da cewa duk cikin binciken da ya gabatar na tsawon satika biyu bai samu wani abu da zai bashi tabbacin cewa ita ce ko ba ita bace ? Amsa guda ɗaya ta tabbata a gare shi , shine matar kurma ce kuma ƴar gudun hijira ce daga yankin Bama , da take rayuwa tsakanin gidajen masu kuɗi tana yin aikace-aikace da ita da tilon ɗan ta mai kimanin shekaru takwas .
Yana shiga unguwar ya bi kwatacen gidan da aka ce tana aiki da su , ya tsaya daga bakin babbar ƙofar gidan ya nemi iznin shiga daga dattijon dake gadin gidan ,
Ganin sa da dattijon yayi cike da haiba da alamun wadata ya sa shi yin tunanin ko ire-iren mutanen da suke mu'amala ne da masu gidan , dan haka kai tsaye yayi masa iznin shiga da motar sa harabar gidan ,
Bayan ya fito daga motar sa ya miƙawa dattijon hannu suka yi musabaha ,
"Baba ina neman Mamar Bulama ne ance nan gidan take aiki ?
"To oho Kurma Mamar Bulama ƙwarai kuwa nan take aiki idan ka miƙe wannan yar hanyar ka ƙure sashin su yana nan daga hannun ka na dama nan za ka ga wata ƙaramar ƙofa ,
" toh sannu Baba nagode sosai .
Har ya fara taku , sai kuma dattijon da yake bin bayan sa da kallo ya dakatar da shi ,
" Amm bawan Allah nace ko dai lafiya kake..
 Wata bangazar da ɗan yaron da ya kwaso da gudu yana gara gare-garen sa ya yiwa dattijon shi ya hana shi ƙarasa zancen sa yayi taga-taga , hular kan sa ta faɗo ,
Da sauri Doctor Hamza ya kama masa yana masa sannu ,
A fusace ya É—ago kan sa ,
" wannan akwai hatsabibin yaro , Bulama , Bulama , ai ko dan kai nayi fatan a kori uwarka daga gidan nan kafin ka kassara ni ko ma ka kar ni baki É—aya ,Â
" wallahi bawan Allah a rana Bulama bai kuskureni ba ya kuskureni sau takwas , ka ga nan "
ya nuna masa dai-dai muÆ™a-mukin sa da ya É—an kunburoÂ
" jiya-jiyan nan iwar haka Bulama ya auno min jifan wani mulmulelen dungur , haba me ake da giggiwa irin ta 'ya'yan sansanin gudun hijira ,
Da tausayawa Doctor Hamza yake ba shi haƙuri tare da yi masa sannu , kafin ya sanya hannu cikin aljihunsa ya zaro gudar dubu ɗaya ya miƙa masa ,
"Sannu Baba ga wannan ka saya manzafi ka shafa a wajen ka kuma dunga sa ruwan É—umi ,
Da sauri dattijon ya wafci kuÉ—in yana Æ´ar dariya ,
"Kai to madalla , Madalla bawan Allah nagode , ai ka gane kwatancen da nayi maka ko ? Ko na raka ka ne ?
"Nagane Baba zan shiga da kaina ,