Sashe 190
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A zaune suka tarar da su shiru tamkar kurame , shi Tafeeda yana aikin latse-latsen waya shi kuma Youssouf yayi tsumu irin yanayin da yake ciki tun bayan mutuwar Mama ,
Babu karsashi suka gaisa , bayanan suka yi shiru ,suna nazarinsa da ya sunkui da kansa , baki ɗaya yayi wani irin sanyi har ƴar rama yayi , ba kaɗan ba mutuwar ƴar sa ya taɓa rayuwar sa ,
Cikin taushin Harshe Ammi ta fara masa nasiha kan laifinsa na aikata zina da ta kai shi ga haihuwar Mama , har zuwa yin aure ba tare da sanin iyayensa ba , bayan haka ta tambaye shi tsakanin Yakaka da Falmata waye uwar Mama ?
Nan ya basu amsa da cewa Yakaka ce mahaifiyar ta ,
Ta tambayeshi kuma ta yaya yake auren Falmata alhai ƙanwace ga Yakaka kuma suna tare guri guda ?
  Nan ya basu labari a taƙaice kan yadda aka yi ya auri Falmata da zaton cewa Yakaka ta mutu ne , sai kuma kwanakin da suka dawo daga USA ya ganta a gidan bashi da wani masaniya kan labarin da ya shafe ta .
 Duk shiru suka yi , kafin ubbo tace
" to tunda Allah ya gwada karshen kome da ya zare wannan ɗiya a tsakani domin kawo maslaha a gare ka, sai kayi ƙoƙarin gyara duk wasu kuskuren ka ,
"tunda daman domin riƙon ita ɗiyar kake amren innar ta ai sai yanzou ka sau amren su yi tafiyar su , kai ma ka koma ga iyayenka ka biɗi afouwarsu , su yafe ma sabadda rayuwa tayi maka kyau Youssoufa , ka fuskanci aikin ka cigaban rayuwarka ka ji kou ?
Ba tare da ya É—ago kan sa ba yace
" to naji ,
Kallon rashin gamsuwa da amsar sa suka bi shi da shi , amma basu jaa zancen da tsawo ba suka rabu da shi , saboda sun san muddin ya tafi Maradi sai ya saki auren Falmata ba zai yiwu ya bijirewa iyayensa ba bayan tarin laifin da yayi masu muni .
Basu bi ta kan su Falmata ba bare su yi musu Sallama suka fita a gidan cikin motar Tafeeda , suka bar Youssouf shi ɗaya tal a ƙofar gidan ,
Matsawa gefe yayi ya samu waje ya tsugunna , kewar É—iyar sa tare da ciwon rashin ta suna taso masa ,
kwanakin da suka biyo bayan mutuwar ta basu zo masa da sauƘi ba sanin da yayi bata raye a duniya yana murƙushe duk wani kuzarinsa ,
baya iya bacci daga ya rufe ido fuskarta ke yi masa gizo muryarta na amsa kuwwa a kunnuwansa ,
baya son doguwar magana da zata katange shi daga yin addu'o'i , ko abinci sai yunwa ta kai masa maƙura yake iya tsakura ya ci .
Ƙaunar Mama dabance a wajen sa ko cikin abubuwan da yafi so a duniya tana a sahun farko , yasan a cikin 'ya'ya ba zai samu ya ita ba a samun zallar so da ƙauna daga wajen sa tayi zarra , sai ga shi tafiya bata miƙa ba , mutuwa ta shafe tsakanin su , ta ɗauke masa sanyin idaniyar sa .
'yar da silar ta ya haɗu da Fatima zahra har tayi sanadin ƙulluwar aure a tsakanin su ta wanzu tsawon lokaci tana ƙulla kusanci a tsakanin su , har sai da ta sa bai farga ba ya faɗa tsundum cikin ƙaunar innar ta ,
Tunanin Falmata ya zo masa , a tun ranar mutuwar Mama rabon da ya sanyata a ido ko ya ji muryar ta , ya san tana cikin halin É—imuwa kwatankwacin wanda yake ciki tana kuma buÆ™atar lallashinsa ,Â
Sai dai ba shi da wani sauran dauriyar sake fuskantar wani tashin hankalin da zai iya tasowa daga gareta bayan sanin da tayi cewa shi da Yakaka sun rufeta akan alaƙarsu da haihuwar Mama , bashi da tabbaci kan yadda ta ɗau lamarin , Dan haka ya zaɓi ya bata iska ,
Kafin zuciyar sa ta gama yanke shawara kan hukuncin da yake son zartaswa a gobe .
***
Yakaka da Falmata sun yi kwanaki biyun cike da kewa da jin ciwo na rashin Mama ,
Koyaushe su na ƙule a ɗaki , basa fitowa falo wajen da su Ubbo suke bare su ga juna , Hajja ita ke kai kawon kula da lamuran gidan, ko abinci kai musu take har ɗaki , duk kuwa da cewa basa yi masa wani cin kirki ,
Wani irin zaman shiru suke yi marar armashi da tunda suke su biyu irin shirun mai kama da na tsakanin baƙi juna bai taɓa gifta tsakanin su ba , kowacce tana jinyar ruhinta
Yau bayan sun idar da Sallar Azahar, suna bisa sallayun su , Falmata ta dubi sashin da Yakaka take , ta ƙira sunanta a hankali ,
" Yakaka ,
Yakaka ta ɗago kan ta ,daga karatun da take yi , ta amsa ƙiran da tayi mata tare da tasowa ta dawo kusa da ita ta zauna ta riƙo hannun ta da irin kulawar da ta saba bata tun tasowar su ,
Falmata ta ƙure kallonta ga Fuskar Yakaka da take iya hango haskenta , tace
"Yakaka , ki faÉ—a min , ki bani labarin tsakanin ku ,
  Tayi shiru kaɗan ,
"ki bani labarin na gaskiya tsakanin ku da Baban Mama , kuma ki bani labarin rayuwar da kika ki bayan haihuwar Mama Alhalin bakya tare da mu ? Ki bani labarin gaskiya Yakaka .
Shiru Yakaka tayi cike da zullumi sai dai ta san abune da tasan da faruwar sa ,tun gabannin ta tambaye ta dan haka ya zama dole ta sanar da ita dukkanin wata gaskiya da ta nemi da ta sani ,
Muryar ta babu kuzari ta fara bata labarin tun daga Rana ta farkon haɗuwar su da Youssouf , har zuwa ranar rabuwar su ta ƙarshe , ta ɗora da cigaba da sanar da ita irin gadar zaren da Samy Baby ta haɗa mata tun kafin zuwan ranar haihuwar Mama da a ƙarshe tayi nasara ƙarƙashin jagorancinta da mummunar huɗubar ta tayi tasirin rabata da rayuwarsu ita da Mama 'yan mintoci kaɗan bayan haihuwar ta ,
dakatawa tayi tana jin tashin hankalin yadda Falmata ta zare hannunwanta dake cikin nata , ta É—ago kai tana kai kallon ta ga fuskar ta ganin yadda hawaye suke zuba daga gurbin idanun Falmata ya ruÉ—a ta ,
Sai dai bata da wani zaɓi illa cigaba da sanar da ita gaskiyar kome kamar yadda ta alƙawarta , bata tsahirta ba ssi da ta gama tas da bata labarin rayuwarta a garin Abuja gidan samy baby , taimakon da Malama Maryam da ƴar ta Lubna suka yi a rayuwarta , har zuwa komawarta gida Maiduguri wajen Prof .
Ta ɗago kanta tana nazarin Fuskar Falmata wacce tayi ƙasa da idanunta ya zuwa yanzu ta daina hawaye , riƙe hannunta ta sake yi muryarta na rawa ta cigaba da cewa
" Falmata na san ni mai laifi ce a wajen ki , amma dan Allah kiyi haƙuri ki yafe min , nayi kome ne gurin ƙoƙarin na baku rayuwa mai kyau bansan cewa ace na kama hanya ne na rusa mana rayuwa ba , ki yafe min ki zo mu koma Nigeria wajen Baba prof shine kaɗai mutumin da ba zai kore mu ba , ki rabu da Rayuwa da Youssouf kamar yadda Mama ta bar mu , shi ɗin ba kowa bane da ya wuce Maƙaryaci Mayaudari da ......
Miƙewar da Falmata tayi ita ta hana Yakaka ƙarasa zancenta , da kallo ta bi ta lokacin da ta nufi ƙofar banɗaki ta tura ta shiga ta rufo ƙofar ba tare da ta waiga gareta ba , zama tayi cikin wani irin yanayi mai cike da rashin madafa , nadama na sake lulluɓar ta , ko Falmata bata buɗe baki tace mata kome ba ta fahimci tana fushi da ita , fushi kuwa mai tsanani , da ya sa taji tsoron sake yin wani yunƙuri domin tana gudun faruwar wani abu marar daɗi a tsakanin su ,
Fiye da minti talatin ta kwashe a zaune tana jiran fitowar Falmata daga banɗakin da tunda ta shiga bata jiyo motsinta ba , har ta fara tsorata tana tunanin tashi ta ƙira ta , sai ta ga ta murɗo ƙofar ta fito , daga fuskarta har tufafin jikinta a jiƙe suke , sai tayi kasaƙe tana bin ta da kallon tsoro , ganin yadda idanunta suka kumbura alamun kuka tayi mai tarin yawa ,
Kayan jikinta ta sauya ta zo ta janye sallayarta da take gaban Yakaka ta matsa gefe guda ta fara sallah ,
Gaɓɓan jikinta baki ɗaya sun daɗa sanyi Shirun Falmata kuma ya sa ta ɗeɓe tsammani , cikin zuciyarta sai ta fara tunanin mafita ,
Ta shiga bijiro mata da kome da ya wakana daki-daki tsakanin da Youssouf wanda tuni ta fahimci kason nata laifin yana neman zarta na Youssouf tun a farkon fari , ai ita ta fara bada kanta cikin salama , sannan ta cigaba da zama rakuma da akala wajen biye masa aikata zunubi , mafi girman laifin da ta aikata shine gudu da tayi ta ƙyale Mama da Falmata ,
wanda ta nan Youssouf ai ya fita amfanarwa ga Rayuwar Mama da ya haɗa su da ita da Falmata ya tallafa har ma ya zamto sanadin samun lafiyar idanun ta wanda tun akan hanyar su ta zuwa Niger Hajja ta sanar da ita samun lafiyar idanun Falmata , ranta kuma ya cika da farin-cikin da ta ƙi nuna shi a fili saboda kada ta nuna yabawa ga Youssouf bayan tarin laifin da take tuhumar sa da shi da kuma ƙudirin da take tafe da shi na son raba zaman su ,
Sai dai a yanzu da irin yanayin da Falmata ta nuna bata hango alamun zata samun haɗin kanta cikin sauƙi ba , ita kuwa ai bata da sauran ƙarfin zuciya , mutuwar Mama ta kwace mata duk wani karsashi nata ,
Jin an ƙira sallah ya sa ta miƙewa ta ɗaura Alwala ita ma ta tada sallar la'asar ,