← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 269

Sashe 38

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da cewa ba duka kalmomin sa yakaka da falmata suka gane ba amma sun fahimci dai falmata tana da wani ciwo wanda yake riƙe numfashi a irin fahimtar su , sai dai daga yakaka har falmata babu wacce ta wani damu sosai saboda suna ganin ta samu sauki saboda falmatan ta bada tabbacin bata jin kome a halin yanzu lafiyar ta ƙalau sai ko ɗan rashin karfin jiki dan haka su ran su yau ƙwal zasu yi kwanan sabon wuri kwanan ƴanci , kwanan cikin haske , ga falmata kwanan kan gado da katifa duk da ba wani taushi bane da katifar asibitin amma ga falmata abun daɗi ne tun da kuwa yau ne karon farko da ta hau gado da katifa a gaba ɗaya tarihin rayuwar ta ,"dan haka da walwala akan fuskokin su suke yiwa dakta hamza godiya wanda yake bin su kawai da ido tare da gƴaɗa kan sa ,"ya kuma juya yana mai sake jaddadawa wata ma'aikaciyar jinya wacce ya kira da suna zahra akan ta tabbatar tayi musu bayanin kalmar fyaɗe tare da nisantar hulɗa da duk wani ɗa namijin da ba muharramin su ba , "wanda shi da kan sa bai san dalilin da ya sa yaji ya damu akan son su nisanci hulɗa da maza har yake jin da yana da dama da ya killace yaran , sai dai kawai ya ɗauki hakan a zuwan tausaya musu da ya fara yi da fahimtar da yayi basu da wani gata bayan Allah sai su biyun da junan su suka dogara ,'

Har ya taka ya nufi bakin kofar ficewa daga É—akin bayan yayi musu sallama domin barin asibitin , sai kuma ya juyo gami da nufo wurin da yakaka take zaune akan kujera daga gaban gadon falmatan ,"

Janyo wata kujerar yayi tare da zama a daf da yakaka wacce tayi wuri wuri tana tunanin me kuma zai sake zaunar da shi ? Domin ita dai sam bata sakewa idan yana wurin wani irin nawi take ji daga ƙarƙashin ran ta da zuwa yanzu ta kasa fahimtar menene , abu ɗaya ta sani shine daga farkon haɗuwar su da tsiya suka faro ta tare da kullatar shi gami da jin tsanar sa cikin ruhin ta, sai dai daga ranar da ya fara taimakon ta zuwa yau ,ta kasa sanin takamaimai a wane mizani ta ajiye shi , ta dai san ƙwarai ta fara ganin girman sa daga haka baza ta ɗorar da kome ba bayan faɗuwar gaban da take ji a duk lokacin da idanun su suka sarƙe cikin na juna , shi yasa sam bata son kallon idon sa ,

Umarni ya bada aka miƙo masa ƴan kananun kayayyakin wankin ciwo idanun sa akan laɓɓan ta da na ƙasan ya kumbura ,"

Da kansa ya wanke mata ciwon da ta ji a sanadin dartse laɓɓan , yana yi yana kallon idanun ta da suke runtse gam a saboda ɗan radaɗin maganin wanke ciwo , a hankali kalmar , "sannu" ta subto daga bakin sa bayan da ya gama wanke mata ciwon ,yana bin fuskar ta da kallo
," ya daina zafi ko ?

A hankali tana me kaucewa kallon idanun sa ta 'gyaÉ—a kan ta ," nagode

Miƙewa yayi ,"ki zo ki sayo muku wani abinda zaku ɗan ci a waje ,"

Tare suka jero duk inda suka wuce tsirarun ma'aikatan asibitin da suke aikin dare , sai sun isar da gaisuwar su , har suka fito bakin asibitin babu me cewa ƙala a tsakanin su ," zaro gudan dubu ɗaya yayi a aljihun sa ya miƙa mata tare da gwada mata tsallaken titi wurin wasu mata masu toye-toye da kuma masu sayar da shayi ,
    Tare da ɗan durkusawa ta miƙa hannu biyu ta karbi kuɗin tana godiya , bin bayan ta yayi da kallo har sai da ta tsallaka titin kafin ya juya cikin asibitin inda ya ajiye motar sa ya shiga gami da bata wuta ya bar harabar asibitin ,'

Bayan sun ci masa/waina tare da ruwan bunu shayin da yakaka ta sayo musu a waje , sai suka tattara hankulan su baki É—aya ga sister zahra da take yi musu bayani dallah-dallah game da fyaÉ—e ta kuma tsoratar da su sosai game da yin tarayya koh wasannin banza da maza , sun kuwa tsoratu har cikin rayukan su fiye da zaton ta domin su dukkanin su biyu kwana suka yi tare da tunanin maganganun da ta faÉ—a musu , wanda ya sa suka ji baki É—aya zaman sansanin nasu ya fita akan su , ga zaton falmata mazan sansanin su ne kaÉ—ai suke iya yiwa mace fyaÉ—e su yi mata ciki ,"

    Yakaka nikam bazan koma sansanin mu ba dan Allah mu samu wani waje mu dunga kwana koh aina ne ' cewar falmata kenan lokacin da gari ya waye likitocin aikin safe suka zo suka duba su tare da basu sallama bayan sun tabbatar da ta samu lafiya ,bata kuma cikin hatsari ,"

Nisawa yakaka tayi wacce itama har ga Allah bata son komawar sun sansanin su , ko kusa bata son abun da zai ɓata rayuwar falmata , duk wani abun da ya shafi falmata bata ɗaukar sa da wasa ,"

Falmata nima bana so mu koma sansanin mu , toh amma bamu da wurin zuwa da ya fi chan É—in , bamu da kowa ba mu san kowa ba ,"

Mu tafi wurin uwarɗakin ku yakaka , mu roƙe ta  , ta yadda ta bamu wurin kwana koh da a zaure ne ,

Zubawa falmata ido tayi tana juya shawarar ta ta cikin nazari , tana hasashen madam saly baza ta ƙi taimakon su ba toh amma gidan madam saly ma ai sansanin maza ne , mazan ma tambaɗaɗɗu ƴan iska , har ma gwara na sansanin su ,"

Girgiza hannun ta falmata tayi , ta É—ago ta dubi fuskar falmatan da hawaye ya silmiyo ,"
  Yakaka dan Allah kar mu koma sansani , ajus baza ta daina aikena wurin ƴan maza ba ni kuma tsoro nake ji yakaka dan Allah kar mu koma ,"

Da sauri ta sanya hannu ta goge mata hawayen ,"kiyi shiru falmata baza mu koma ba ,"

A hankali suka tako zuwa wajen asibitin , duk da cewa yakaka ta so su jira dawowar dakta hamza domin ta bashi chanjin sa naira ɗari takwas da yake hannun ta , toh amma kukan falmata ya kaɗa mata hankali bata jure damuwar falmata , sai dai har zuwa yanzu da suka fito bakin titin suka jaa suka tsaya hankalin ta ya kasa kwanciya da zama a gidan madam saly tare da ƙanwar ta ,

Kamo hannun falmatan tayi ta zaunar da ita lokacin da wani tunani ya É—arsu a ran ta ,"

   Zamu je gidan madam saly mu roƙe ta mu zauna zuwa wani ɗan lokaci , sai dai da sharaɗi falmata ,

SharaÉ—i ?
  Eh sharaɗi falmata , gidan madam saly matattarar ƴan maza ne , ba kamar yadda kike zato bane falmata , gidan madam saly gidan ƴan iska ne , kin ga ke kuma falmata baki da lafiyar idanu zasu iya cutar da ke kamar yadda na sansanin mu suka so yi , dan haka na samo mana wata dabara , idan zaki yadda ,

Zan yadda koma menene yakaka idan har baza mu koma sansanin mu ba ,"

Zaki koma namiji falmata
Zaki koma saka kayan maza
Zan aske miki kan ki , domin ta haka ne kaÉ—ai a yanzu zan iya kare ki daga Æ´an maza kin yadda ??

Baki buÉ—e falmata ta ware manyan idanun ta tana juya su a saitin wurin da take jiyo sautin muryar yakaka tamkar dai tana kallon ta ,' !!!!
.

  
Kar ku manta da kankaro mutunci ,
Iya adadin sharhi da nuna kulawar ku iya karfin da zan samu wurin cigaba da rubutu
     Nagode.

#umm'muaz
#fikhr
#son so[6/24, 10:57 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association

MAFARI...
( Hargitsin Rayuwa)

umm'muaz

16

Tafe suke su biyu akan hanyar su ta zuwa gidan madam saly , idan ba wanda yayi musu farin sani tar-tar ba , babu ta yadda za'a yi a gane falmata mace ce , sakamakon askin tal kwabo da yakaka tayi mata da sabuwar rezar da ta saya , sai walwali da ƙƴalli mummulallen kan ta yake , jikin ta kuwa sanye take da wasu afarangiya da wondo na maza da suka yi mata bururum-bururum wanda yakaka ta saya mata a kasuwar tsaye da sauran chanjin dakta hamza ,

Fuskar falmata sam babu walwala saboda dole kawai yakaka tayi mata har ta amince kan ta ya sha askin da tun da aka yi mata shi take jin kan ta sakayau tamkar zai faÉ—o ga uwar ranar damina da ta fara É—agawa "hantsi ya dubi ludayi" , wannan karon hantsin kan falmata ya duba ,"

Yakaka nikam gaskiya bazan iya sake yadda ki min wani askin ba idan har gashi na ya sake fitowa kamar yadda kika ce ,"saboda gaskiya zafin rana tana ƙona min fatar kai ,sannan kin ga kullum a rana nake wuni a zaune ,"

Cikin tausayawa tare da ganin laifin kan ta yakaka tace ,"

   Ki daure kiyi hakuri falmata ni da kaina ba'a son raina ba ne na aske miki suma ,bamu da wani zaɓi ne bayan hakan ,kina sane dai da yadda mazan gari nan suke ƴan iska ," kiyi hakuri nan gaba bazan sake suɗe miki kai tal kamar haka ba zan dunga bar miki kaɗan ,"

    Me zai hana ki saya min hula kawai ?? Ki barmin kaina ba tare da kin aske ba idan ya so na cigaba da sanya kayan mazan a zuwan ni tamiji ce , tunda ba wanda ya san mu a gidan madam ɗin sai yagana da kolo ,"

Yakaka bata samu zarafin amsa mata ba sobada sun kawo gidan madam saly ,
      Cikin yin ƙasa-ƙasa da murya tace kiyi shiru falmata mun zo gidan , kar kiyi wani abun da zai sa wani ya fahimci ke mace ce ,"
  Fuska a turɓune falmata tace " toh"
Chapter 38 · 0% Book details