Sashe 232
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Riƙo ta yayi lokacin da ya lura tana jaa baya daga kusan sa cike da tsoron kar ta sake tafiya ta bar shi ya shiga share mata hawayen ta yana cewa " ke kika bar ni Fatima kin manta ke kika tafi ba tare da izni na ba , baki ko min sallama ba kika bar ni ? Fatima ke ma bakya sona ko ?
Kan ta ta mayar kirjin sa da ƙarfi tana jin farin-cikin sake ganin sa tana jin kamar an bata maganin wata cuta dake cinye mata nishaɗin ta , ta kewaye shi da hannuwan tana riƙe shi ƙam-ƙam .
"Oshh , yace yana É—an É—aga ta daga jikin sa saboda raunin sa da ta fama .
"Fatima ina da rauni a jiki , baki san nayi jinya ba kou ?
Idanun ta suka yi rau-rau tana kallon a hankali ta motsa bakin ta tana faÉ—in "sannu ,
Da ido ya amsa mata da yasan ba lalle ta gani ba da nishaɗi cikin muryar sa yace "Ya babyn mu ? Lafiyar shi lau kou ? Naga yayi girma , ya zama babba alhalin bana ganin sa .
Bai jira ta ba shi amsa ba ya ɗaga ta suka miƙe tsaye yana ɗora faɗin " mu tai ciki ki bani labarin yadda kika zou nan kuma ki nuna min Baby na na gan shi sosai .
Ƙin motsawa tayi a hankali ta zare hannun ta daga cikin nashi kafin tace " nan ba shine masauƙin mu ba a can wajen Umma muka sauƙa can zan koma .
Sake riƙo hannun ta yayi ya ja ta jikin sa ɗan tunbin ta ya tokare haɗuwar fuskokin su muryar sa a ƙasa da wani irin yanayi yace "to ai nan ne gidan ki nan da muke tsaye nan ne shiyar gidana nan shine ɗakina ya mata nuni da ƙofar ɗakin su .
Cike da son samun haÉ—in kan ta ya cigaba da cewa ko kin koma yanzu tunda na dawo gobe nan za'a kawo ki , kin ga nayi rashin lafiya ma baki ko min ya jiki ba , muje ciki na nuna miki inda aka min fiÉ—a .
Da sauri ta ɗago kan ta muryar ta tana rawa tace "yanka ka aka yi ? Aina ? Amma ka warke yanzu ? Ni fa ban san kana rashin lafiya ba sai da suka je tahowa da ni suke faɗa .
Langwaɓe kai yayi da son ta tausaya masa yace " nayi jinya iriyar wacce ban taɓa makamanciyar ta ba Allah shi ɗagga ni da war haka na daɗe a kushewata .
Ta buÉ—e buÉ—e baki zata yi magana suka fara jiyo muryoyi ana hira da dararraki ana kusanto su ,
A tsorace Falmata ta zare jikinta daga nashi a kunnuwan ta masu saurin ɗaukar sauti ta tsinkayo muryar Ubbo cikin masu maganar ,
Muryar ta tana É—an rawa tace " ni ni zan tafi ga mutane suna zuwa kar a ganni ace kuma na biyo ka .
Yana ƙokarin sake riƙe ta taƙi yadda da sauri ta sauƙa daga barandar tayi bayan shuke-shuken da suke kusa da ita .
Da wani irin yanayi yayi tsaye hannuwan sa biyu zube cikin aljihun wondon sa har Siyama da Ubbo suka ƙaraso wajen bayan su bayu ne su uku suna bin su ɗayar saɓe da Yumna a ƙafaɗar ta biyun suna riƙe da manyan tire-tire da aka jera abinci bisa .
Kallon su yayi kafin ya É—auke kai ya juya yana buÉ—e musu É—akin
"Biyamuradi daman kana ta tsayuwa nan ? Ko kouwa yanzou kaima kake isowa ?
Ubbo ta tambaye shi ,
Bayun da suke gaishe shi ya amsawa gaisuwar kafin su wuce ciki Siyama na gaba tana musu jagora.
"Tun-tuni na zou Ubbo , ya amsa mata yana satar kallon inda Falmata take maƙale ran sa sam babu daɗi damuwar sa kar wani ƙwaro ya cije ta .
" To ni zan koma sai da Safe ku kula da kan kou .
GyaÉ—a mata kai yayi lokacin da take juyawa Bayun da suka ajiye sakonni hannuwan su suna rufa mata baya bayan Siyama ta sallame su daga ciki .
Suna ɗan bada tazara ya sauƙo daga kan barandar da sauri ya nufi inda Falmata take kafin ya ƙarasa daga bayan sa Siyama tace " Baban Yumna wani wurin kake tahia ? Na haɗa ma abinci fa kouma ga wanka ma na tsumayen ka .
Juyowa yayi yana kallon ta ya ga yadda ta ƙarya wuya tana tsare shi da idanun ta , a dai-dai lokacin ya rasa takamaimai amsar bata yana ganin ta ta taho har gaban sa tana murmushi ta saƙala hannun ta cikin na shi .
"Ka bar koume zouwa gobe yanzou lokacin hutu ne Maimartaba da kan shi yace Umma ta sanar da kai ka huta yau sai daren gobe za ku gana .
Jan hannun sa tayi tana 'yar dariya ta sake cewa "mu tai ciki na kula da kai Vous êtes mon patient pour aujourd'hui et je suis votre médecin.( kai marar lafiyan da zan kula da shi ne a daren yau nice likitar ka )
Cikin idanun ta ya mayar da duban sa yana lalubo fassarar kalmomin ta a cikin su, murmushi ta sake yi masa tana kashe masa ido da yasa shi yin dariyar da bai shirya mata ba , cikin ran sa yana mamakin yaushe Siyama ta falle ya haka ? ya jaa ta jikin sa hannun sa riƙe da kugun ta suka juya tare muryar sa ƙasa-ƙasa yace mata " Fille, es-tu sûre que tu peux prendre bien soin de ça, ta patiente? ( Yarinya kin tabbatar za ki iya kula da wannan marar lafiyan naki da kyau ?
Dariya ita ma ta saki tana rufe fuskar ta da tafukan hannun ta cike da jin kunya gefe guda zuciyar ta na madallah da 'yar uwa irin Ubbo da duk wasu shawarwarin ta basa wuce akan yadda zata yi ta karkato da hankalin mijin ta kan ta.
Sun kai kan barandar sa ya juyo yana sake kallon inda Falmata take a idanun sa ya ga motsawar ta a wajen .
Siyama ta jaa hannun sa zuwa ciki suka turo ƙofar .
A hankali Falmata ta fito daga inda tayi maɓoya idanun ta shaɓe-shaɓe da ƙwalla zuwa yanzu ta tabbatar ita 'yar karo ce a wajen sa da kaddara ta haɗa su marar yanci ce ita da koyaushe take duƙunƙune a gefe.
Siyama ita ce matar da take da 'yanci na yin duk yadda ta so da shi a lokacin da duk ta so amma ita ai a ɗosane take da kuskure kaɗan zata yi dangin sa su tunɓuke ta .
Idanun ta suna ruwa ta baro sashin da kyar saboda bayan ta da yake rirriƙewa sai dai lokacin da ta tasamma komawa masaukin ta sai ta rasa hanya ,
Sai lokacin ta lura da sashi-sashi ne a ainahin gidan da duk gine-ginen su iri É—aya ne sai ka lura da kyau zaka iya tantancewa ko kuwa idan daman ka san gidan sosai .
A idanun ta da suke da rangwamen lafiya ga kuma duhun dare ba zata iya tantance ina ta fito ba sai dai tayi amfani da hagu da dama dan haka tayi hasashen sashin da yake hagu daga nan ta fito dan haka ta kama hanya .
Ko a tsarin harabar sashin bata ga sauyi daga wanda ta gani a É—azu ba shiru sashin yake babu kowa duk hadiman sun kammala aiyukan su sun tafi ga makwantan su .
dan haka kan ta tsaye ta dunga ratsa falukan da ita take tura ƙofofin su da hannun ta har ta tarar da wanda ya mata iri ɗaya da nasu sai dai wannan ta lura kamar ba wancen ɗin bane saboda wannan babu kujeru sai wasu irin katifu da aka yiwa falon ƙawanya da su da ta tsaya da kyau ta lura sai ta ga kamar har labulayen falon ba irin waɗancan ɗin bane .
Tana ƙoƙarin juyawa ta nemi wanda zata tambaya ko nan ne sashin Umma kamar yadda ta ji ana ƙiran surukar ta da wannan sunan , dogon kunnen ta ya fara jiyo mata tashin muryar wata mace daga ɗakin da tayi zaton masauƙin ta ne dan haka ta ɗan taka gaba kaɗan zuwa kusa sa ɗakin tana saurarar kalaman matar da take yin su cikin tashin hankali da hargagi .
" Hafsatouwa ya zamo dole ki kouma wajen sa ki daɗa masa bayani da jaan kunne kada a samou watta matsala ga wannan karon wannan shegiyar ɗiya ta mutan agades da ta ɗora min jakar tsaba kaji sunka bini da tsattsaga ina buƙatar ya lalata min ƙwanyar ta , ta wanke ni ta wanke ɗiyana da bakin ta da ta min wannan sheri ta tona min asiri na da shike binne tsawon lokaci ina so ta lahe ɗoɗɗoyan aman da tayi da bakin ta .
" shi kouwa wannan taƙadarin yaro ɗan tamri Youssoufa da ake kome bisa kan sa ina so a sabunta min aikin sa yayi tsamri fiye da na baya a ƙara hargitse shi a gigitar shi ya fice hankalin sa , itta hegiyar ɗiyar da ya amro dagga Nigeria a sanya shi i mata shika ukku russ tunda na lura shina ƙamnar ta sosai hakan zai ci ran sa ya zaburar sa komawa ga ruwa ina so ya zama tamre wurin bibiyar mata a baya ya kwana da ya ya auri ƙamna gaba 'ya da uwa nake fatan ya haɗa kada kouma ya saurarawa barasa ya zuƙe ta tamkar nonon uwatai ya zama lalattace irin lalatar da zata sa iyayen sa su yahe shi dagga cikin 'ya'ya mutanen gari su masa korar kare dagga birnin Maradi .
"Daga nan na san baƙin-cikin haka shi zai kai Safiya ramin ta...tayi wata dariyar hango cikar buri .
Daga ƙasan ta inda tayi gurfano Hansatuwa da take sauraron ta tana taya ta dariya tace " Ranki shi daɗe maganin kukana ai wannan kullin magani da na kawo miki shi ita uwar ta su anka ce ana so ta ci domin barin ta haka nan tsakani yana lalata mussu aiki kin san ta da ibadar ganin ido .