← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 182 OF 269

Sashe 182

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuruf Hajja ta miƙe daga kishingiɗar da tayi tana jaan chasbaha , ta buɗo kofar tare da leƙowa ,

"uwarÉ—akina ai Yayar ki tayi bacci tuni , ki koma kiyi kwanciyar ki ki huta kun haÉ—u gobe da safe ko kuwa ,

Murmushi tayi , "kai Yakaka har tayi bacci ikon Allah ,

ÆŠan jim tayi sai kuma ta sake cewa ," Hajja to ko cikin dare idan ta farka ki faÉ—a mata na zo muyi hira tana bacci , ai ta ci abinci ko ?

"ta ci abinci sosai ta cika cikinta dam ,

"to Hajja sai da safe ,

" yauwa uwarÉ—akina maza a je ayi bauta a huta ,

Har ta juya sai kuma ta sake dawowa ,

"amma , un, un Hajja nace da dai kin taso ta ta koma É—akina , ina da filo mai laushi irin wanda take so , Yakaka bata son filo mai tauri irin naki Hajja ,

Wani kallon yatsu-tsu Hajja tayi mata ,

"aifa Lalle , ita Yakaka jaririya ce kenan ?  To ai wannan surutun da kike ba kai ba ƙafafu ya isa ya tayar miki da ita daga baccin da na lallaɓata da kyar take yin sa , ni wuce Dan Allah ki tafi Allah ya tashe mu lafiya ,

Ƴar dariya Falmata tayi jin yadda Hajja take yi mata shaguɓe akan Yakaka , juyawa tayi ta kama hanya cikin ranta ba haka ta so ba , so tayi su raba dare suna hira da Yakaka , bata so Yakaka ta ga kamar ta kyale ta ta maƙalewa mijin da bata da tabbacin cigaban zaman su ,

Youssouf da sauri ya taryeta a cikin ransa yana hamdala da rashin ganawar su ,

Hajja tana komawa ɗaki ta dubi Yakaka da take zaune akan sallaya riƙe da Alkur'ani tana karatun ta hankali kwance , duk zantukan Falmata a kunnen ta , tausayi gami da ƙaunar 'yar uwar ta suna bin jinin jikinta da gudu ,

Hajja ta mokaÉ—e baki , lokacin da take komawa ta zauna a wajen da ta tashi ,

"ai a wani ƙaulin irin wannan ƙaryar tana iya zama makaruhi , ko kuwa ba haka ba Babba uwar Mama ?

Yakaka bata kulata ba ta cigaba da karatun ta , can ƙasan ranta diramar Hajja ta fara bata dariya , 

**

Youssouf , Yakaka , da Falmata kusan kowannen su raba dare yayi bai yi bacci ba musamman Youssouf da ƙiran sallan farko na ƙarfe uku da rabi a kunnuwan sa a hankali ya zame Falmata daga jikinsa wacce itama bata jima da samun bacci ba , ya miƙe tare da shiga banɗaki ya ɗora Alwala , jallabiya ya zira yazo ya tada sallah

Nafila yayi tayi har zuwa lokacin da masallatan unguwar suka sa Assalatu , sai ya sallame ya miƙe ya ɗau turare ya fesa tare da ɗaura agogon sa ,

Fita yayi ya nufi masallaci , bayan ya ja ƙofofin gidan gabaɗaya ,

Yana bada baya , mutumin da yake maƙale da jikin katangar , ya siɗaɗa kansa tsaye ya shiga gidan ,

Yakaka wacce ta shiga banÉ—aki domin É—aura Alwala sallah ta ga inuwar mutum ya gifta ,

Tsam tayi tana tunanin waye ?

Haka kawai ta ji zuciyarta ta tsinke , sai ta juya da sauri ta fito , sannu-sannu take tafiya , hasken lantarki ya game ko'ina , gabaɗaya unguwar ƙiran sallah ne ta ko'ina ,

Mutum ta gani a tsaye ya bada baya yana nufar ƙofar falon Youssouf ,

"Waye ne ta ce

Idanunta ƙyar akansa ,

Chak aka tsaya ba tare da an jiyo ba ,

Matsawa tayi ta sake cewa waye ne nace ?

Ba'a amsa ba ,

Taku ta fara yi tana kusantar sa , ta zo kusa da shi bata ankara ba ta ji an kifa mata marin da ya gigitata ,

Tayi taga-taga tana jin wani tsuu a kunnuwanta saboda ƙarfin marin , ta ji takun gudunsa sai dai ta kasa watsakewa daga zafin marin da yayi mata dan haka bata yi wani yunƙuri ba ,

Lokacin da ta watsake babu kowa a wajen ,lokacin an idar da sallah gari har ya É—an yi shaa ,

Yawatawa ta fara yi a wajen tana raba ido ko Allah zai sa ta ga azzalumin da ya mare ta haka ?

Ƙarar buɗe ƙofar gidan ya sa ta juyowa a tsorace , wanda ta hango ya shigo ya sa zuciyarta bugun uku-uku ,

Da sauri ta gyara zaman hijabinta , ta fara tattaro duk wata dauriya da ƙarfin halin da take da shi ta kuma shiga harhaɗa manyan kalmomi masu kaushi da take son yin amfani da su domin su taya ta tunkarar sa ,

Tirus , Youssouf yayi yana hangota , sarai ya gane ta , wani É—an guntun yawu ya haÉ—iye lokacin da tunaninsa ya gama ba shi dalilin tsayuwar ta anan ,

Gyagijewa yayi a matsayin sa na soja bai kamata ya tsorata har haka ba .

Kai tsaye ya nufi ƙofar falonsa yana yin kamar ma bai san tana wajen ba ,

bai ƙarasa ba ya ji tashin muryarta ta ƙira cikakken sunan sa ,

" Youssouf Abdul-Aziz Baskore ,

Sai ya juyo a hankali ya fuskantota da takunsa mai girma , fuskar sa babu alamun É—aukar wargi ,

"Gani

Yace da ita muryar sa a kwance tamkar fuskar sa ba a murtuke take ba ,

Cikin zallar ɓacin ran da yake tunkuɗo kansa daga ƙasan ranta da ta wanzu tana ɗauke da shi tsawon shekaru , ta ƙaraso daf da shi da taimakon hasken Alfijir da ya ƙeto ya dusashe hasken lantarkin wajen suke iya kallon fuskokin juna ,

" Nasan baka san wannan ranar zata zo ba , baka san cewa zan dawo ba , shiyasa har ka samu damar kutsawa cikin rayuwar ƙanwata,  ka cuceni ka yaudareni , ka ɓata min rayuwa , ka lalatamin Asalin 'yata , ka sa rayuwata ta shiga garari  kuma ka zo kana sake cutar min da ƙanwata , a karo na biyu kana sake gurɓata mata rayuwa , Allah zai saka mana abunda kayi mana , kai wanne irin marar imani ne macuci Azzalumi , Mayaudari kuma fasiƙi mazin ....

" KI MIN SHIRU .

Baisan lokacin da ya daka mata tsawa ba saboda kalamanta da yaji suna tayar masa da hankali , take jijiyoyin kansa suka fito ruÉ—u-ruÉ—u , idanunsa suka sauya launi , jikinsa har tsuma yake yi , irin tashin hankalin da yake ji , da akwai bindiga a hannunsa zai iya kai harbi .

Tsawar da yayi ita ta farkar da Falmata wacce taji tashin muryar sa a tsawace , shafa ɓangaren da yake tayi ta ji baya nan ,

Sassauta murya Youssouf yayi yana kallon Yakaka da take masa kallon sheƙeƙe kallon tsana kallon baka isa ba , , zata yi magana ya sake katse ta ,

"Nace kiyi shiru ,

zuciyar sa ya ji tana kai kawo wajen tuno masa da girman kuskuren sa , girman laifin da ya yiwa Yakaka , sai ya shiga ƙoƙarin sassauta fushin sa tabbas kome Yakaka zata faɗa masa ya cancanta  , shi ɗin ai ya cutar da its dayawa kamar yadda tace ,

"ki yiwa Allah kiyi haƙuri , kiyi shiru mu bar kome a tsakanin mu ko dan saboda Albarkacin Fatima da Mama , ki faɗa min duk abunda kike buƙatar nayi miki zan yi ,

Ya furta hakan muryar sa a ƙasa yana satar kallon ƙofar falonsa,

Cikin rashin sanin sa Falmatan tana tsaye daga jikin ƙofar ta bayan labule kalmomin sa na ƙarshe kuma sun cigaba da sauƙa a kunnuwanta tarwai .

"Abunda nake so shine kawai ka sakar min ƙanwata , ka sake ta Youssouf ka kuma bani 'yata , Falmata baza ta taɓa cigaba da zama matarka ba muddin ina raye , ka auri Falmata Alhlin babu sanina ba kuma tare da amincewar wani nata ba , ya zama dole ka saki Falmata , ka sake ta nace .

Ganin yadda ta birkice masa tana ɗaga sauti tamkar bata cikin hayyacin ta yasa Youssouf ruɗewa yana gudun kar Falmata ko Hajja ɗayar su ta ji maganar , dan haka cikin yanayi na lallaɓa yace ,

" to naji naji , zan SAKE TA ,

Wani irin kallon kar ka raina ni Yakaka tayi masa ,

" yanzu nake son ka sake ta anan idan kuma ba haka ba wallahi zan je masarautar maraÉ—i a yau ba gobe ba ,

Da tashin hankali Youssouf yake kallon Yakaka , wacce ta tsattsare sa da ido babu alamun shakku a tare da ita ,

Gani yayi gabaÉ—aya ta rikiÉ—e masa tamkar ba yarinyar nan da ya rainawa wayo , ya kuma yi wasa da rayuwar ta a shekarun baya ba ,

Falmata wacce hawaye suka riga suka wanke mata fuska kamar ruwan fanfo, ta sanya tafukanta duk biyu ta rufe bakinta ta hana sautin kukan da take yi fitowa , a hankali ta silale ƙasa ta durƙusa tana jin yadda marar ta ta wani irin curewa guri guda ..

Assalamu Alaikum masu karatu da fatan kun wuni lafiya ?😍❤

Wai-wai , kai-kakai , yau wacce rana ?? 🤓😂

Uhmmm ai idan har baku daina sakar min bama-baman Comments da likes din ku irin na jiyan nan ba ( ko ma fiye da haka )  Nima kuwa ba zan yi k
ƙasa guiwa ba wajen cigaba da sasukar rubutu ba,  "Ah to meye? Ai tuwon girma miyar sa nama,  sannan kuma yaba kyauta tukuici. ❤😍

Amma kuyi hakuri da yadda bana samun damar maida muku da martanin sharhin ku,  idan nace zan dunga daukar waya ba zan kammala aiyuka na da wuri har na samu damar typing ba , duk da haka nayi alkawarin zan bibiyi comments din ku baki daya na bada amsa inshaallah .

Nagode.

Na manta ko da wacce take buƙatar hayar ɗan Biri saboda tsaro ?! 🐒😂[11/26/2019, 3:24 PM] +234 706 503 6187: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa)

Umm'muaz

42

Wani ɗan kuka ciki-ciki da Mama ta fara daga can cikin ɗakin kwanan su mai haɗe da nishi shi ya sa Falmata miƙewa daga inda ta durƙushe tana rishin kuka ,
Chapter 182 · 0% Book details