Sashe 231
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da ya shigo gida sashin Hajiya Umma nan ɗin ma a cike ya tarar da sashin da katafainin 'yan uwansa waɗanda dai suke cikin ƙasar kama daga waɗanda suke ciki ɗaya har 'ya'yan Hajiya Mama da suke gidan tuni sun yi zangon a ɗakin mamar su labarin tabbatuwar shigowar sa yasa suka yi ɗango zuwa sashin Hajiya Umma.
Haka ya dunga gaisawa da wasu wasu na rungume shi wasu har 'yar ƙwalla suke na jin dadin sake ganin sa a tsaye kyam bisa diga-digan sa irin taryar da suka masa ya sanya shi jin hawaye bai taɓa sanin haka yake zakara a cikin 'yan uwansa ba sai yau , babu shakka da mutuwa yayi da ya bar musu miƙin da bazai gogu ba a zuci .
Daga can lungu ya hango Siyama ita ma ƙwallar farin-cikin ganin sa take tare da tasowar ciwon kewar sa da take yi , ɗan bakin nan nata yaƙi rufuwa daga murmushin da take kamar yadda ta kasa janye idanun ta daga kan sa.
da hannu ya yafice ta yana 'yar dariya tare da jin raguwa ciwon da yake ji a cikin ran sa kan abunda ya same shi yana yin ƙasa da kusan kaso 50% ganin soyayyar 'yan uwan sa ya ishe shi farin-ciki .
Tana murmushi ta ƙaraso zata tsugunna daga gefen sa ya sa hannu biyu ya ɗago ta ya matsa tare da yi mata wajen zama daga gefen sa da fara'a cikin sautin sa yace " Mata ai geufen Mijinta take da mazauni ƙaƙa za ki ɓuya bayan Aicha kina leƙe na ? Ina ɗiyata ban ganta a masu tarɓa ta ba .
" tana bacci' ta bashi Amsa tana sake riƙe hannun sa da yasa cikin nata a lokacin ji take kaf duniya ba wanda ya kai ta jin farin-ciki har wani narkewa take jin zuciyar ta na neman yi bata ƙi ba kowa ya watse a bar su tare .
Wajen ya ɗau dariya wasun su na tsokanar Siyama suna cewa kunyar kinibibi take yi bayan tun ɗazu ta ishe su da leƙe-leƙe .
A cikin su duk babu wanda ya tado da batun abunda Maimounatou tayi masa da wannan kuma umarni ne daga Maimartaba da kan sa da yace " kada a maida zancen labarin tattauna akai .
Hajiya umma ta miƙe tana barin wajen zuwa cikin ɗakin ta a lokacin Allah kaɗai yasan Halin da zuciyar ta ke ciki tayi rauni bata taɓa zaton zai dawo haka ras da shi da lafiyar sa ba babu shakka Allah shine mai yin yadda yaso da bawan sa wani ɗan Adam can bai isa tasiri ba.
Bayan Miƙewar ta bai fi mintoci uku ba shima Youssouf ya mike cikin ran sa ya fahimci Mahaifiyar sa na son ganawa da shi dan haka ya bi bayan ta zuwa cikin ɗakin .
Bayan yayi Sallama ya tura kai ciki , bisa sallaya ya hango ta riƙe da Alkur'ani , ta ɗago kan ta tana saita ganin ta a kan shi fuskar ta ɗauke da Murmushi ya ƙaraso daf da ita ya zauna yana riƙo hannuwanta baki ɗayan raunin da yake ji a lokacin shine ya taso masa " Umma Allah shi min dawowa ban mutu ba kamar yadda suka so .
.. ya furta hakan hawayen da suka cika idanun sa na sauƙa , yana jin yadda zuciyar sa ke yin kuka.
a take ita ma zuciyar ya ta karye tun faruwar lamarin yau ne rana ta farko da Youssouf É—in yace wani abu yau ne kuma rana ta farko da ta ga kukan sa a tunda ya zama cikakken mutum.
Kan shi ta ɗora hannun ta kafin tace " ka dawo Youssouf ita cuta ai ba mutuwa ba wani kuma bashi da tasirin datse rayuwar wani sai fa idan kwanaki sun ƙare ka yi godiya ga Ubangiji doumin shi ya baka kariyar da basu idda nufin su ba Allah ya sa hakan ya zama kankara na daga zunuban ka .
" Amin-Amin Umma, ya amsa yana goge ƙwallar sa da hannuwan ta duk biyu ta taya shi tamkar dai lokacin da yake ɗan yaron sa.
" Kar ka yiwa maƙiya kuka kamar kai ba jarumi bane ? Hakan zai iya barantaka da matsayin da kake kai na Soja mazan Fama sannan kuma Yarima sarkin watarana jarumi bai yiwa maƙiya kuka idan sun kai shi ƙasa ya samu dama miƙewa yake ya gyagije a cigaba da fafatawa .
" hakan ba kome bane da ya wuce ƙarin ilmi cikin zaman duniya ka lura ka gane ba kowanne so bane yake zama na gaskiya , ba kowanne murmushi bane yake zama na ƙauna wasun ai shiga suke irin ta burtu suyi aron halayya da kamanni domin cimma wata mummunar manufa tasu su idar da mugunta ka kiyaye Yossoufa .
Kallon ta yake bai ko ƙifta idanun sa zuciyar dake ƙirjin sa ya buɗe yana ƙarbar duk wasu kalmomin ta yana musu adana saboda dayawa daga cikin zantukan ta bai kai ga gane me take nufi ba a yanzu ? Har kawo yanzu cikin ruɗani yake mai yawa '
har kawo yanzu zuciyar sa bata bar nacin tambayar sa me yasa Maimounatou tayi masa haka ba ? yana son ganin ta domin ita kaɗai take da amsar tambayar nan .
Ga mammadou ya kasa amincewa kiyayyar da yake masa har ta kai ya kashe shi ? Mammadou É—an uwan sa ne da yake kusa da shi a haihuwa cikin jerin 'ya'yan gidan mutane biyu ne kaÉ—ai a tsakanin su Bilal da kouma Yacouba da suke É—aki guda.
Hajiya Mama kouwa da É—ai ba zai yafe mata ba da ta zama jagora na lalacewar rayuwar sa da zama tsanin faÉ—awar sa a duk wasu munanan aiyuka da yayi a baya.
Muryar Hajiya Umma ta katse masa zurfin da yayi cikin tunani inda take miƙa masa 'yan mukullin ɗakunan sa tana cewa "Magarib ta gabato ka tai kayi haramar Sallah nasan Maimartaba zai nemi ganin ka doumin ku tattauna ya ji ra'ayin ka kan duk waɗanda suka maka ƙeta kada ka cutar da kan ka wajen hanawa a bi ma hakkin ka , ka yafewa wanda duk zuciyar ka ta amince da yi masa yafiya , kada kouma ka ɗaukarwa kanka aniyar zama da wanɗanda zuciyar ka bata aminta da su ba ka saukakewa kanka sake faɗawa ga hatsari irin wanda ka fito a baya Allah ya ƙara ƙiyaye mouna kai sannan ka tsanan ta addu'a .
"Amin Umma na kouma gode sosai Allah ya ƙara nisan kwana tare da lafiya .
Lokacin da ya fito mafi yawan 'yan uwansa sun watse sun tafi hidindimun su wasu kuma suna haramar sallah Ubbo ce kaɗai a zaune da ya fito dariya suka yiwa juna shi da ita yana wucewa tace " Fita kake yi Yarima ?
" zan tai Sallah , ya ce mata yana ƙarasa ficewa .
Bayan ya idar da Sallah gajiya duk ta taso masa tun yana sallar yake hamma dan haka bai tsaya sauraran masu son gaisawa da shi ba ya nufi cikin gida sashin sa ya tasamma saboda so yake yayi wanka da ruwa mai É—umi ya É—an huta kafin lokacin isha'i da yasan bayan sallar isha zasu gana da Maimartaba .
Masu gadin shiyar sa suka buɗe masa ƙofa ya shiga , haske ya wadaci harabar da taimakon security lights dan haka ya nufi sashin sa kai tsaye yana janye ganin sa daga shiyar da Maimounatou tayi zama da ƙoƙarin son raba zuciyar da damuwar da take rufto masa ya hau kan 'yar barandar sa ya kai hannu yana kunna wuta domin ya samu damar buɗe ƙofa .
Zuciyar da tai masa wani ɗan ƙaramin tsalle lokacin da ya lura da wanzuwar mutum kwance akan barandar kusa da ƙafafun sa ,
"Wanene nan ? ya tambayi zuciyar sa yana yin baya kaɗan cike da mamaki yana kure kallo zuciyar sa a dake da ƙoƙarin ganin fuskar ta da ta juya baya tana baccin ta hankali kwance
Motsin sa da yayi da ɗan ƙarfi yasa ta motsawa ta juya zuwa rigin-gine tana motsa idanun ta da suka yi nawi .
Saƙare yayi yana duban ta karo na farko da ya ji ya yarda cewa akwai Mafarkin ido biyu domin shi yake yi a yanzu.
. "Fatima-zahra ya ƙira sunan ta a can ƙasan maƙoshi bata amsa ba saboda baccin da yake son sake danne ta .
Tsugunno yayi a hankali kamar mai tsoron kar ya taɓa ta ta ɓace ya kai yatsun sa biyu kan fuskar ta ya shafa .
Da sauƙar hannun sa a fuskar ta ta buɗe idanun ta da suke luf-luf cike da rauni ta ɗora ganin ta akan fuskar sa da
"Fatima-zahra est-ce vrai ? Ehm ? est-ce vrai ? Ya furta hakan muryar na 'yar ƙyarma .
Hannun sa da yake cigaba da mata yawa a fuska ta riƙe da nata hannun kafin ta fara yunƙurin tashi sai dai kwanciyar da tayi a kan floor ba tare da shimfiɗa ba yasa jikin ta yin ciwo musamman haƙarƙarin ta .
Lura da yadda ta kasa tashi farar ɗaya yasa shi tallafar ta gaba ɗaya ya zaunar da ita lokacin da shima yake yin zaman dirshan a ƙasa ya jingina ta da jikin sa kamar wanda ya tuno sai ya ɗaura dukkanin hannuwan sa biyu akan tudun cikin ta yana shafawa da buɗaɗɗiyar muryar sa yace
"Fatima ki min magana mana don Allah , kece kuwa ?
Kewar sa mai girma da take ta faman yaƙa tsawon watannin da suka yi basa tare ita ce ta taso mata baki ɗaya a yanzu ta kassara duk wata juriyar ta sai ta juyo a hankali rana ta farko da ta ɗaro hannuwan ta a fuskar sa ta riƙe shi da sanyi murya tace " Baban Mama est-ce vrai ? Meyasa ka tafi ka barmu tsawon lokaci baka neme mu ba ? meyasa ? Ka sa min ciwo a zuciyata ta , kasa kullum ina ta kuka . ƙarasa zancen tana janye hannuwan ta daga fuskar sa hawayen ta suka fara sauƙa .