← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 269

Sashe 93

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan fitowar doctor Hamza daga masallacin sallar asubah kai tsaye sashin mahaifin sa ya shigo kamar yadda ya saba , kan shi a ƙasa suka gaisa da mahaifin sa wanda yake nazarin ɗan nasa ba tun yau ba ya fahimci akwai wata ɓoyayyar manufa a zuciyar ɗan nasa game da yarinyar ya bari ne yaga iya gudun ruwan sa , amma tundaga yadda ya ɗau komen su da muhimmanci ya fahimci yana da ra'ayi akan ɗayar su ,"

  Tausayin sa ya ji mutuwar yarinya da irin birkicewar da yayi ya sashi fahimtar wataƙila ita zuciyar sa ke ra'ayi

Addu'a ya sake yi masa sannan ya É—ora da tambayar sa ina Æ´ar uwar ta ?

Nan yayi shiru ,
  Kafin yace
Suna gidan Amne ita da jaririyar da uwar ta bari ,

Nan take fuskar professor ya sauya
  Gidan Amina ?
   Me kuma ya kai su gidan Amina ?
Na kai su ne wai dan ta kula da su musamman ma jaririyar .

  Ita Amina MACE ɗin ce za'a bawa kulawa tare da tarbiyyar yara mata har biyu ? ?  To ban amince ba maza idan gari ya gama haske kaje ka zo da su , tunda ka kawo yaran nan gidan nan ikon su ya bar hannun ka ya dawo ƙarƙashi na , ni nake da ikon kulawa da su , nima ina ƙwaɗayin samun ladan rikon marayu da marasa galihu , kan Ji na ko ?
   Toh Baba

Ya amsa yana jin wani sabon tirniƙin ɓacin rai na taso masa sam sam baya son wani abu ya sake haɗa shi da kome ƙanƙantar abu wanda ya shafi yarinyar nan , daren jiya kwana yayi bai yi bacci ba saboda yadda ran sa yake ƙuna game da abun da yarinyar tayi masa , juyi ya dunga yi yana mamakin halin MACE ,

Shi a son ran sa ya bar su a chan wajen Amne ɗin lokaci lokaci yana zuwa yana kai mata abunda zasu buƙata domin a zahiri shi fatima da jaririyar ma bai son ganin su ," gani yake ita ma ƙanwar tata ta san kome tare suka haɗa baki , " shi yanzu ya bar ganin ƙanƙantar su tare da musu kallon matausaya ," ya tsinke akan lamarin MATA

Ba yadda ya iya haka ya shirya kafin ya wuce aiki yaje gidan Amnen inda ya tadda ta tana yiwa baby wanka jikin ta duk a sanyaye ta kwana da zancen mutuwar yakaka sosai yarinyar ta shiga ran ta saboda yanayin kamanni sosai da take da ƙanwar ta  Rahima ,

  Bai yadda ya ɗora idon sa kan jaririyar ba suka gaisa da Amne tana sake jajanta mutuwar yakaka tare da yi mata addu'a ta ɗora da tambayar sa aina aka yi jana'iza
   Kaucewar tambayar yayi ta hanyar cewa ina ita ƙanwar tata ??
     Tana wanka tun jiya take abu ɗaya ,"kuka ," kuma har zuwa yanzu bata kai ga sanin mutuwar ƴar uwar ta ta ba , ban ma san wanne irin hali zata iya shiga ba idan ta samu labari ," sai dai ka san hanyar da zaka bi ka kwantar mata da hankali kafin ka sanar mata da mutuwar nan 

Cikin ƙagauta Hamza yace
   Wane rarrashi Amne kowa ai zai mutu ki gaya mata kawai yayar ta mutu , kuma ki bata baby ta zo mu koma gida Baba ya ce na mayar su gida ...
    Ƙarar faɗuwa da suka ji shi yasa Amne fitowa da gudu bayan ta shinfiɗe jaririyar ,

Doctor hamza ko gizau bai yi ba hasalima tun tsayuwar falmata a gun ya gan ta , yi yayi kamar bai gan ta ba , da hikimar sa na son fahimtar ko falmatan ta san kome da ya faru ?

Ganin yaƙi fitowa yasa Amne kwala masa ƙira ,"
     Ka fito ka ga abun da yarinyar nan take yi , kar ita ma ta mutu ," tace da shi cikin ɗaga murya

Shi da kan sa ya tsorata ya kuma ji tausayin yarinyar lokacin da ya fahimci ciwon ta na asthma ne ya tashi , gaba ɗaya numfashin ta ya siƙe yana neman ɗaukewa bata cikin hayyacin ta ,
   Da taimakon Allah da dabarun sa na likita , numfashin ta ya dawo ,

  Zumbur ta miƙe zaune tare da kufcewa daga riƙon da Amne ta mata , lalube take tare da faɗin
   Ina yaya daktan , ina kake yaya dakta , Dan Allah Dan Allah ka kai ni wajen Yakaka , naji kun ce wai Ta mutu , wai yaya ta ta mutu , ai wasa kake ko ? Yakaka tana gida ko ? Yaya za'a yi yakaka ta mutu ta bar ni ? Alhalin ta san bani da kowa sai ita , bani da ƙarfi kun gani fa ni miskiniya  ce Dan Allah kar ku min irin wannan wasan ,"
   Yaya dakta ka min magana mana , tace haka lokacin da ta samu nasarar chafko rigar sa ta rike tamau ,

  Yaya dakta Dan Allah
  Ta sake cewa muryar ta tana wani irin harɗewa ,
   Ji yayi wani mugun tausayin ta ya rufe shi yaji ina ma bai ambaci kalmar mutuwa ba , cikin ƙwarar makafin idanun ta da suks firfito suka sauya launi tamkar ba nata ba yake iya hango irin firgici tare da azabar da zuciyar ta ke ciki ,
   Kukan da baby ta tsanyara shi yasa ta yunƙura da gudu tayi sashin da taji tashin muryar jaririyar , kafin su taro ta har ta faɗa ɗakin kasantuwar ɗakin da ɗan zurfi ya sa ta faɗa ciki sakamakon jefa ƙafar da tayi nan take ta gurɗe ta tafi ta faɗi , bata haƙura ba ta rarrafa da gudu sashin da take jin kukan jaririyar
   dai-dai da shigowar su
   da lalube ta ɗauke ta ta riƙe ta gam a cikin jikin ta , "
       Idan ni bakwa tausayi na Dan Allah ku ji tausayin jaririyar nan ku kai ta wajen maman ta ni da yakaka mun yi Alƙawari zamu haife ta mu rene ta mu biyu mu bata kulawa mu biyu ,
   Meyasa yanzu zaku ce Yakaka ta mutu  ? WAYE NI DA BABY IDAN BA YAKAKA ? WAYE ZAI KULA DA MU ?
   ALLAH shine zai kula da ku Fatima , Amne ta ce tana sharar ƙwallar tausayin yaran , shi da kan sa hamza idanun sa sun kaɗa , tsanar yakaka na sake taso masa ,"

  Wani irin kuka falmata take har tana tsuma ,"
   Baba , Mama , yaana , Bulama Yakaka duk kun mutu ? Kun mutu kun bar ni ni kaɗai ?  Ni meyasa ban mutu ba nima ??
   Kiyi haƙuri Fatimah kowanne me rai zai mutu lokacin sa kowa yake jira , kiyi musu addu' a
   Kawo baby na shirya ta ku tafi ," Amne ta furta hakan tana mai ƙoƙarin amsar jaririyar ,
  Wani irin janyewa Falmata tayi da ƙarfi ta sake ƙanƙame yarinyar ,"
   Ki bar min ita kar kowa ya taɓa ta bani da kome bani da kowa sai ita , ita ma haka , ita ce jini na kaɗai a duniya ita ce ƴar uwa ta madadin dangina gaba ɗaya , ita ce HASKEN da zan iya gani da ido na , kar kowa ya taɓa ta , kar kowa ya taɓa ta , kar kowa ya taɓa ta , ta dunga maimaitawa kamar bata cikin hankalin ta ,

   Da ƙyar ta yadda Amne ta sanyawa babyn diaper tare da kayan sanyi tana riƙe a hannun ta ,

  Wani irin yanayi take ciki , kamar ɗaukewar ruwan sama hawayen fuskar ta suka tsaya , ta kuma haɗe labban ta wuri guda bata cewa ƙala , sai ajiyar zuciya da take akai akai , lokaci zuwa lokaci laɓɓan ta na motsawa ,"

A haka suka fito Amne ta kama ta ta sanyata a mota tana rungume da jaririyar da ruwan É—umi ya ratsa ta take ta baccin ta kasantuwar tun farar safe Amne ta cika mata ciki taf da madara ,"

   Motar su tana tsayuwa Rahima wacce daman tana dakon jiran zuwan su , ta fito da gudun ta tana kuka ta rungume Falmata ,
    Wacce take ƙiƙam bata kuka kuma bata ce ƙala ba , "

  Sashin Baba ya kai ta , ta ɗurkusa guiwar ta biyu a ƙasa tana rungume da baby ,
   Muryar ta chan ciki ta gaishe shi kan ta a sunkuye ,  ta'aziyya yayi mata kafin ya ɗora mata da nasihu , " a ƙarshe ya ɗora da shaida mata cewa ",Hajja mai wurya," dattijuwar dake yi masa girki ita zata cigaba da kulawa da jaririyar har zuwa lokacin da zata yi ƙwarai , bata ce kome ba kan ta a ƙasa ,
    Rahima ƙarbo jaririya ki kawo ta nayi mata huɗubha , wanne suna kike so a sa mata ??
Zare jaririyar Rahima tayi ta miƙewa baban su ,"
   Ya sake maimaitawa wanne suna kike son a sa mata ,
   YAKAKA ," tace da shi a taƙaice
Jimm yayi yana mai maida duban sa ga hamza , "
  Wannan ba suna mai asali bane ki faɗi wani sunan Fatima ," Baba yace da ita ,"
    YAKAKA , ta sake maimaitawa hawaye na kwararowa daga idanun ta  ,
   Shikenan za'a mata laƙabi da Yakaka, .
    a take yayi wa jaririya huɗubha ya miƙawa rahima ta mayar ta hannun yakaka ,"
   Suka miƙe suna barin falon ,
 

Abuja Nigeria

Ƙarfe shidda na yamma su Yakaka suka samu isa garin Abuja ,"  gajiya da ciwon kai da ciwon ciki irin na ssbuwar haihuwa, zazzabi tare da dumuwar da take cinkushe cikin zuciyar Yakaka suka haɗu suka yi ligi-ligi da ita , , ta zama marar lafiya sosai sai numfarfashi take , bata ko iya buɗe idanun ta sosai ,
Chapter 93 · 0% Book details