Sashe 128
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da misalin ƙarfe goma na safiyar ranar Alhamis ɗin karshen sati , ƴan tsirarun mutanen da prof ya ƙira na cikin unguwa da basu wuce goma ba tare da wasu ƙarin mutane biyar da youssouf ya kawo a matsayin wakilan sa wanɗanda a zahiri abokan aikin sa ne daga ƙasar su , suka haɗu suka shaida ɗaurin auren FATIMA DILMARI , tare da YOUSSOUF ABDUL-AZIZOU BASKORE , wanda ya sauya suna zuwa youssouf Garba Malbaza Uzine,
Bayan É—aurin auren babu É“ata lokaci su abokan aikin youssouf suka yi komawar su domin É—aura shirin tashin su zuwa Abuja inda zasu wuce Æ™asar su ta jirgin sama a yau É—in ,,Â
da shi kuma youssouf ya shigar da neman iznin a bada mota guda cikin motocin su na soji tare da direba da zai tuƙa su zuwa Niamey ta hanya , ba'a tsananta bincike ba aka bashi izni tare da shaida masa ya tabbatar ya samu isa niamey kafin ranar litinin inda za'a yi bikin dawowar su tare da yi musu ƙarin girma ,
Hajja me wurya," ita ce dattijuwar da prof ya zaɓa a matsayin wacce zata raka fatima ɗakin mijin ta daganan ta gano garin da zasu zauna a niger , kasancewar ita hajja mai wurya dattijuwa ce da a ƙalla ta tasamma shekaru hamsin , sannan kuma a halin yanzu bata da wani jigo cikin rayuwar ta iyaye duk sun mutu dangin kuwa kowa ta kai ta kai yake sannan tun asali bata da haula ɗan ta ɗaya ne tal da ta haife shi a shekarun girma bayan aure auren da tayi ta yi domin neman haihuwa ,
tana tsakiyar fara cin moriyar É—an nata da ya É—an fara tasawa shekarun sa ishirin da huÉ—u , Æ´an tawayen boko haram suka shigo har gida suka yanka mata shi , a cewar su yana zagin su tare da sukar akidar su , dan haka suka kawar da shi,
Tun daga nan rayuwa ta fara yi mata wahala , ƙunci da talauci suka dirar mata , zamani ne da kowa yake gudun wahala ba'a duban zuminci , tunda ta fahimci haka ta daina yin raragefe gidan ƴan uwa ta bazama neman na kan ta sanin da tayi da ɗan sauran karfin ta bata zama ƙarƙashin dangina ana zuba mata sharar walakancin ,
aikatau ta fara a gidajen saida abincin ,kasancewar ta gwanar girki iri iri ,musamman ma na Æ™asar camaru da tayi farkon zaman auren ta a chan , amma sakamakon tsaurin ta da kuma tsayuwar ta kan gaskiya ya sa ba ta cika daÉ—ewa a wajen aikin ake sallamar ta , saboda bata zuru duk ta ga zalau sai ta tsinka ,"Â
daga baya ta koma aiki a gidajen masu hali nan ma gida biyu tana barin aiki saboda yadda take gwadawa uwargida iyakar ta a cikin gidan ta idan har ta ga abunda bai dace ba, sai fa wannan karon da tayi dace ta samu aiki gidan Professor Mustspha dilmariÂ
Allah ya tsawaita zaman ta a gidan da taimakon tarbiyyar yaran gidan da basu cika raini da walakanci irin na sauran Æ´aÆ´an masu hali takwarorin su ba , babu kuma matar gidan shekaru biyu take nema da fara aiki a gidan a matsayin mai yin girki , musamman ma na shi prof .
A jiya da prof ya ƙira su ita da falmata ya faɗa musu hukuncin da yake ƙoƙarin yankewa har ma ya tuntunɓi ita falmata akan jin ra'ayin ta , ta amince zata auri baban ƴar da take riƙo su tafi ita da shi da ƴar chan ƙasar sa ko kuwa ??
Ga mamakin sa ba tare da shayin kome ba
Falmata ta amsa da ta amince zata auri baban baby ya tafi da ita tare da baby ,Â
 Ƙwarai prof ya ji daɗin amsar Falmata domin da farko har yana fargabar ko yarinyar zata ƙi gatan da yake son yi mata na aurar da ita tunda ƙuruciyar ta , ga mutumin da yake iya hango nagartar sa a cikin yanayin sa da mu'amalar sa , yana hasashen mutum ne na ƙwarai !
A sarari ya nuna jin daɗin sa tare da yi mata addu'o'in samun nasara a rayuwa , sannan ya juya ga hajja mai wurya wacce ita ma take durƙushe daga gefen falmata ,
Hajja Alfarma zan nema a gurin ki akan ki raka fatima É—akin mijin ta ki gano min wajen da zasu zauna ita da mijin ta a chan niger É—in daga baya sai ki dawo. Da fatan zaki min alfarma ?
Dariya hajja me wurya ta sa !
Babu kome Alhaji zamu tafi tare , me zaman aure ma ta amince bare ni ƴar rakiya ?? Ai ko gaba da binnin sin ne Alhaji ba na ƙi raka ƴar marainiyar Allahn nan ba , kai shima dai wannan dogon balaraben nijar ɗin Allah yayi masa Albarka da duk da kyan nan nasa da cikar zati irin ta ɗa namiji amma haka ya runtse ido ya ce ya amince zai auri wannan murɗaɗɗiyar bahaguwar yarinyar , ai dole ayi masa godiya bawan Allah .
Nan dai Alhaji ya sallame su yana sake musu godiya akan biyayyar da suka ma sa ,
Kan hanyar su ta komawa hajja mai wurya tana riƙe da hannun falmata tace
  Ke ƴar nan Allah ya dube ki ya tarfawa garin ki nono , irin wannan zankaɗeɗen miji da Allah ya wanke ya ba ki ?? Ai ko ɗiyar masu mulki ba ta ƙi shi ba , to zan fara faɗa miki tun wuri tun yanzu , ki zubar da waɗannan hargitsatsun halayen naki tun a nan nigeria kar ki ce zaki tafi gidan auren ki da su , saboda wannan dai miji naki wallahi kin yi sa'a wanke hannun ka taɓa Allah dai shi sa yadda surar nan tasa take halin sa yafi haka kyau ,
Ai bazan bar gidan nan naki ba sai na ga kamun ludayin zaman naki da shi , ato sai ki shirya ni ɗin dai da kika tsana kike ƙin bani riƙon jaririya , nice dai me miki zaman ɗaki sai dai muyi wacce za mu yi mahaukaci ya ɗau rigar kurma ...
Zame hannun ta tayi daga cikin na hajja tayi gaba ta miƙa hanya , ƙalau tamkar me gani saboda yau da gobe ta fara haddace hanyar a ƙwaƙwalwar ta,
  Sasakai hajja me wurya tayi
  Au aikin banza kenan hanci ba ƙafa , to ki fi ruwa tafiya , nace ki fi ruwa tafiya , wannan yarinyar sai na dage kafin ta shiga hanya ta ɗau haske ta san me duniya take ciki kan ta hayaƙi yake ,!
Falmata ko sauraron ta bata yi ba hasalima ji tayi hayaniyar hajja me wurya ta hana kwakwalwar ta sakewa tayi tunanin da ya kamata shi yasa ta zame hannun ta ta rabu da ita ,
  Aure da ita da shi ?? Wanene shi da yace baban baby ne ? Da gaske shine baban baby ? Wanne irin aure zasu yi ? Ina ne ƙasar ta su ? Idan suka tafi zasu dawo ? Bata son barin nan inda take , burin ta watarana dr hamza ya nemo mata maman su , to amma yanzu kuma ga shi zata tafi ta bar nan ɗin ,
  Abun da ta sani zata yi kome , zata tafi ko ina zata kuma ta shiga kowannen wahala domin ta tsira da baby mama , domin ta tsaya tare da baby mama , domin baby mama kar ta sha wuya , naƙasun ta miskinancin ta , rashin idanu ,
da ace ita lafiyar ta ƙalau , bata buƙatar abokin tayi wajen gina rayuwar ƴar ta , da zata gudu da baby mama ta ɓuya wani waje tana kula da ita , to amma ita ɗin ma miskiniya ce dole ne ta bi baban baby da yace zai kula da mama ƴar sa ce !
Ƙarfe biyu cif aka fara fito da jakar bocco ɗin falmata wacce ta haɗe kayan ta da na yakaka kakaf a cikin babbar baccon yakakar , sai kuma kayan baby mama shima a cikin babbar jaka , duk aka zuba su a bayan dunƙulalliyar motar soji me ƙirar golf kofa biyu ,
Biyamuradi youssouf ya taka zuwa cikin gidan falon prof , suka yi sallama inda prof ɗin ya bi shi da kalaman godiya ya kuma ɗora da damƙa masa amanar fatima tare da roƙon sa akan ya kula da ita , ita ɗin abar a tausayawa ce ,
Nan youssouf ɗin ya amsa tare da ɗaukar Alƙawarin zai kula da ita ,
Yana zaune hajja me wurya da falmata rike da mama haɗi da rahima suka shigo , falmata tana shirye tsaf cikin sabuwar atamfar ta ruwan ganye da adon furanni farare, ta saka farin hijabi har guiwar ta ,
Daga gefe suka tsugunna , nan prof yayi musu addu'o'i tare da ƴan nasihu ya sake ɗanƙa amanar falmata a hannun hajja me wurya har lau ,
Daga ƙarshe ya zaro kuɗin sadakin falmata naira dubu ishirin sabbin bandir ɗin ƴan ɗari biyu ,
  Ungo Rahima ,
miƙawa fatima kuɗin sadakin ta hakkin ta , fatima ina me baki haƙuri akan yadda auren ya zo a ƙurarren lokaci ban miki kome ba da iyaye ke yiwa ƴaƴan su idan zasu kai su gidan miji , amma na miki alƙawari na kuma yi magana da shi mijin naki akan idan kun isa ya tura min account number zan tura da kuɗin da za'a saya miki kayan ɗaki da na amfanin gida a chan kin ji ko ? Ki riƙe wannan sadakin auren ki ne ,
Da sauri falmata wacce idanun ta suka kawo ruwan hawaye akan irin ƙaunar da prof ke musu tare da sanin cewa yau zata bar gidan shi zuwa wani waje da bata da sani akan me zata je ta tarar , tace
 Baba na bar maka kuɗin ni babu abunda zan yi da su ,
 A ah fatima ki karɓa nace hakkin ki ne , watarana zaki samu abun saya da su ,
 Muryar ta na karkarwar kukan da ta soma tace
 Baba to ka riƙe min idan na dawo zan karɓa ,