Sashe 95
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
  Ita ma sai da zuciyar ta tayi tsalle da ba ta hango yakaka saman gadon asibitin ba , Â
   Chan gefe ta hango ta , da sassarfa ta nufi wajen ta tana
  Yaks ya kike zaune a ƙasa lafiya dai ko ?
   Tana jin muryar samy baby ta miƙe tsaye gami da takowa da gudu ta riƙe hannun samy baby ta shiga roƙon ta ,"
   Anty samy Dan Allah kiyi sauri ki kaini wajen sa , ya mayar da ni gida na koma wajen su Falmata , ji nake kamar zan mutu ,
   Da ido samy baby ta bita tana iya hango tashin hankali tare da ruɗani gami da tsantsar rikici a idanun Yakaka ,"
   Ke yaks bana son shirme ki nutsu , haka kike so na ɗauke ki yarkace-yarkace daga gadon asibitin na kai masa ke ??
  Ai wannan sai ya kore ki
Bazai kore ni ba anty samy shi zai kai ni a min gyaran jiki ,"
  Mtss samy baby ta jaa tsaki ,
Ki zo kici abinci Yakaka tun jiya rabon ki da abinci , nurse É—in sun baki magani tare da allura ? Ki ci abinci ki gyara jikin ki kafin likitan ya zo ,"
 Warce hannun ta da samy baby ta riƙe tayi , ta durƙusa gami da haɗa hannun ta ta shiga yi mata magiya tana gunjin kuka akan lalle fa ita a yanzu zata kai ta wajen bature kam silum kuma a yau zata koma wajen su Falmata ,"
  Tun samy baby na ƙoƙarin rarrashin ta tare da yi mata dabara har ta suƙe ta fara yi mata masifa ,
  Faɗan da ta fara yi mata bai haifar da kome ba sai sake rikicewar Yakaka domin kuwa yunƙurawa tayi da gudu tana ihu ta nufi ƙofar ficewa daga ɗakin da nufin komawa gida ,"
 Da gudu samy baby ta ruƙo ta kafin ta kai ga ficewa daga ɗaƙin , hankalin ya fara tashi ita ma , sam bata yi zaton yakakar zata birkice mata irin haka ba , " sai tayi da gaske tare da taka tsantsan idan ba haka ba zata jawo mata jangwam kowa ya san haƙiƙanin abun da ya faru daga ƙarshe ita ce zata iya faɗawa hannun hukuma ayi ram da ita ,"
   Ke yaks Ke yaks ƴar iska meye hakan kike min ? Ina cewa da yardar ki da amincewar ki muka taho ? To shikenan gyara jikin ki ki sauya kayan ki da wannan rigar ta miƙa mata wata doguwar riga a cikin leda tare da audugar mata da sabbin panties , shirya mu tafi ,"
  Ba musu yakaka ta karɓi rigar tana jan ajiyar zuciya irin na wanda ya ci kuka sosai , ta shiga banɗakin wajen ta gyaro jikin ta gami da sauyo kayan ta ,"
  Kwandon abincin samy baby ta ɗauka suka fito daga asibitin ba tare da sun yiwa kowa sallama ba bare su bi ta kan chanjin su da samy baby ta tabbatar akwai ,"
  Gidan da yake mallakin ta ne wanda ta fara kai yakaka jiya nan ta sake yada zango ,inda tayi wa yakaka umarni da ta fito ba musu ta fito , ta taka ta bi bayan ta zuwa cikin gidan inda ta sa ɗan mukulli ta buɗe wata ƴar kwatatciyar ƙofar madaidaicin falon suka shiga kai tsaye samy baby ta wuce jikin wata ƙofa da take daga gefen hagu a cikin falon ta sanya ɗan makulli ta buɗe kofar ta sanya kai ciki ,
   Yakaka tana dogare daga bakin ƙofar falon ta ji muryar samy baby na ƙiran ta daga cikin ɗakin da ta shiga ,
 cikin ɗakin ta shiga gami da durƙusawa daga baki-baki tace
 Na'am Anty samy
 Tashi ki ƙaraso yakaka nan ɗakin ki ne , na shirya miki shi tun kafin na kawo ki , ga banɗaki nan shiga kiyi wanka na haɗa miki ruwa mai zafi sosai da zaki gasa jikin ki , idan kin fito ga gado ki kwanta kiyi bacci idan ya so in kin farka kin cin abinci kin nutsu sai muyi magana ,"
 Tunda ta fara magana Yakaka ta ɗago idanun ta tana kallon ta ,gama maganar ta ya zo daidai da silalowar ƙwalla daga idanun Yakaka , da kyar ta harhaɗo kalmomin da zata iya amfani da su
  Anty samy cewa kika yi shi yace ki kaini wajen sa , na ɗauka tun jiya zaki kai ni ? Dan Allah ki kai ni bazan zauna anan gidan ba ,"
 Kallon baki da hankali samy baby ta watsa mata ,
ai kuma sai kiyi tunda ke kunnen ƙashi ne da ke bakya jin maganar mutane , tace tana kewaye ta ta fice daga ɗakin har ga Allah ta fara ganin gangancin kan ta da ta ɗauko yarinyar nan ta zo da ita nan ba tare da ta mata bayanin haƙiƙanin gaskiyar manufar ta ba , kar fa ta zame mata matsala !
  Zama tayi akan ɗaya daga cikin ƴan kananun mannanun kujerun da suka zagaye falon suka yi ɗas gwanin sha'awa ,
    Ta ɗauki wayar ta da nufin ƙiran ƙawar ta ,"
  Yakaka ta gani ta fito ta tsaya akan ta jikin ta sanye da dogon hijabin da ta bata jiya ," Â
  Ɗurkusawa tayi a gaban ta cikin wata irin murya chan ciki tace
  KI MAIDA NI GIDA ANTY SAMY ,"
Da sauri samy baby ta miƙe tsaye
  Ke Yakaka kar ki min iskancin banza da rashin kunya ,
  To bari ki ji na faɗa miki Gaskiya ni taimakon ki nayi na tsamo ki daga cikin hallakar da wannan Doctor yake neman jefa ki ta hanyar ƙulla soyayya a tsakanin ku , alhalin ya san cewa sofi na nan na dakon soyayyar sa shekara da shekaru ,
ni nasan irin Alkaba'in sofi da Alwashin da take ci akan duk wata mace da ta raɓi Doctor Hamza , da bana fatan ko kusa ki faɗa cikin kaidi tare da masifar ta , shi yasa na zare ki daga cikin rayuwar doctor baki ɗaya na kawo ki nan waje na domin na inganta miki rayuwa na tsaya miki ta yadd watarana za ki zama macen da ire iren Sofi da waɗanda suka fi ta zama annoba ma basu isa ɗaga miki ɗan yatsa ba , amma dayake ke ƴar iska ce WAWIYA JAHILA ,kina neman butulce min akan wani sakaren makahon son abunda baza ki taɓa samu ba da kike yi ,
  ki buɗe kunnen ki kiji da kyau ni ban san inda wani yarima yake ko wa ? Ban san inda yake ba abokin sa nuhu da kan sa bama tare , dan haka dabara kawai nayi miki tare da aiki da ILMI NA , dayake ke wawiya ce kika yadda kika amince wani ɗan sarki wai yana ƙiran ki ,
Ɗan sarkin da kuka yi tarayyar kwanaki kaɗan domin samun muradin zuciyar sa kaɗai , ɗan sarkin da ya miki ciki ya jefar ki kan titi ya yi tafiyar sa ya bar ki ba tare da ya sake waiwayar ki ba , ɗan sarkin da dake da babu duk ɗaya ne a wajen sa , ya ma jima da mantawa kin taɓa wanzuwa a rayuwar sa , wanda yayi watsi dake tsawon wannan lokacin amma shine kika yadda wai yana ƙiran ki wai yana ƙiran ki a hakan nan naki ,!
  Ta ƙarashe tana nuna ta da ɗan yatsa kafin ta kwashe da dariyar walaƙanci ,"
   Kin san meye yaks , idan zaki tafi Ban hana ki ba ga hanya ki fita amma ki sani nan Babban birnin tarayya kike Abuja , cike take da mutane mabanbanta wanda masifar da take tare da wasun su ta kai girman da ya zarta tunanin ki , abune mai sauƙi a sace ki a ɓatar da ke ɓata na har abada ,"
  Zaɓi ya rage gare ki ki zauna tare da ni ki gina kan ki ta yadda watarana zaki koma ki ɗauko ƴar ki tare da ƙanwar ki ki musu rumfa ki zama gatan su , ko kuma ki fita da nufin komawa masu amfani da mutane wurin yin tsafi suyi gaba da ke su hallakar ki ,
Wataƙila ki samu nasarar komawa garin maiduguri kije ki auri doctor Hamza, sofi ta taso bisa kan ki a ƙarshen ƙarshe ki hallaka a hannun ta , masifar sofi bazai tsaya iyakacin kan ki ba , har makauniyar ƙanwar ki tare da ƴar da kika haifa sofi sai ta ɗau fansar raɓar mata doctor da kika yi ,"
  taku ta fara yi tana barin falon bakin ta na sake furto kalmar ,shawara ta rage gare ki BANZA WAWIYA JAHILA ,