Sashe 80
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
  Parking yayi a gaban wani ɗan ƙaramin gida mai ƙaramar kofa dake ƙarshen layin ," ya kulle motar sa ya taka ya hau kan ɗan dandamalin gaban gidan kafin ya leƙa da kan sa cikin ɗan siririn zauren ya rangaɗa sallama har baki uku lokacin da yake kallon agogon hannun sa da yake nuna karfe tara dai-dai na safe ,"
Karfe tara cif tayiwa biyamuradi youssouf a cikin rumfar madam saly , inda ya jaa ɗaya daga cikin kujerun wajen ya zauna ba tare da ya kula kowa ba , rarraba ido yake cikin nutsuwa yana neman fuskar ta a tsakanin fuskokin ƴan matan da suke ta kai kawo a gaban sa ," suna cigaba da gyaggyara tare da goge kujeru zuwa kan teburan da suke cikin rumfar , domin ba'a riga an fara sayar da burkutu ba tukun ,
Karo na uku yagana ta É—ago kan ta tana sake kallon fuskar sa , tabbas shine wannan É—an gayun balaraben mutumin da yakaka tace É—an uwan ta ne ,"
HaÉ—a ido suka yi ta sakar masa murmushin da ke nuna alamun sanayya ,
  Kallon ta yayi ya watsar gami da sake musƙutawa bayan ya daɗa ɗaure fuska tamau , cikin abun da bai fi mintuna biyar ba ya fara gundura da zaman , shi mutum ne wanda bai ƙaunar jira , yafi son daga ya buƙaci abu to ya samu ,"
Ajiye É—an tsumman goge-gogen da yake hannun ta yagana tayi gami da nufo inda yake ,"
Sannu da zuwa malam.
Yi yayi kamar bai ji ta ba yana nacewa kallon É—aya daga cikin sabbin Æ´an aikin da madam saly ta maye gurbin su yakaka da su ," farin ta ya jaa hankalin sa daga nesa yayi zaton ko wacce yake nema ce , sai da ta matso kusa ya fahimci ba ita bace domin wannan daga ganin ta ma hasken na bilicin ne ga fuskar tata wani wuri jaa wani wuri ruwan hoda wani gun kuwa brown ne ma , haka take dai dabbare-dabbare , É—auke kan sa yayi dai-dai lokacin da ita kuma take farga da kallon da yake bin ta da shi nan take ta watsa masa signal da ido tana wani mokaÉ—e baki !
Gyara tsuyuwar ta yagana tayi ,"
Unm nace ka zo wurin yakaka ne ??
Maida hankalin sa yayi kan ta ji da yayi kamar ta ambaci sunan ta , sai dai matsalar shi bai wani riƙe sunan nata ba , amma tabbas kamar ya ji ta taɓa ambatar sunan ,"
Wata ɗiya nake nema , tana aiki anan doguwaa ce fara , tana da tsaga bisa ƙuncin ta , idan kin san ta ki sada ni da ita zan biya ki ,"
Karkaɗe jikin kayan ta yagana take lokacin da ta fahimci bayanin sa wanda yake sake tabbatar mata da zaton ta na ƙarya yakaka tayi mata da tace wai ɗan uwan su ne , domin ga shi ko sunan ta bai sani ba tabbas wata alaƙa ce ta daban a tsakanin su ,"
YAKAKA TAYI CIKIN SHEGE MADAM SALY TA KORE TA DAGA GIDAN NAN, BABU WANDA YA SAN INDA TAKE .
Ta furta hakan lokacin da take gyara zaman rigar ta cikin halin ko in kula ,
Wani irin abu biyamuradi ya ji tsuwww yana yawo a cikin kan sa tare da kalaman da yarinyar nan ta furta masa ," kusan bai ma fahimce ta sosai ba , dan haka ya saita idanun sa cikin nata tare da tattaro duk wata nutsuwa da yake da ita ya sake maimaita mata kalmomin da yayi amfani da su wurin tambayar ta É—aya bayan É—aya dalla-dallah kamar mai koya mata karatu ,"
Sake maimaita masa amsar tayi kamar farko ," lokacin da take taka kafafun ta tana barin wurin , tare da turniƙin kishin da ya tattare mata a ƙahon zuci , saboda tashin hankalin da ta gani a fuskar sa baro-baro yana nuni ne da kowacce irin alaƙa ce a tsakanin sa da yakaka mai girma ce ta kuma taka wani matsayi mai muhimmanci a wurin sa , "
tare suka zo maiduguri da yakaka amma a sarari yake bayyanuwa yakaka ta fita sa'ar shigowa garin ,' tun akan wannan kyakkyawan ɗan gayun likitan da ya gigice a neman ta ta fahimci hakan ," wannan mai kama da larabawan kuma ko menene alaƙar sa da yakakar oho ?? Ko ma menene ta sha alwashin sai ta rusa duk wani tubalin nasara a rayuwar yakaka ,"
Wani irin yanayi na ruɗani ya shiga da tunanin sa yake kufce masa da hakan har ya sa bai ma san lokacin da yagana ta bar gaban sa ba ," kalmar cikin shege kawai ita ke maimaituwa a ƙwaƙwalwar sa tana fasa kan ta tana sake dunƙulewa wuri guda tare da yin wajajjawa cikin tunanin sa ," wani irin ƙugi cikin sa yayi da yake bayyana halin tsoro da ya shiga lokacin da tunanin sa ya tattaru wuri ɗaya ya chanko masa yarinyar tana ɗauke da cikin sa ne ba cikin shege ba ,"
Kamar wanda aka tsikara ya miƙe tsaye akan kafafun sa yana wurga idanun sa kowanne lungu da saƙo yana neman yarinyar sai dai ko alamun ta bai gani ba kamar wacce ta ɓace ,
Wata irin damƙa ya kaiwa kafaɗun wannan koɗaɗɗiyar yarinyar da barin yagana wurin ya sanya ta tahowa gaban sa tana wata ƙwarƙwasa ,
Ƴar ƙara ta saki saboda yadda ƙasusuwan kafaɗar ta suka amsa da jin ruƙon soja ba da wasa ba ," muryar sa ta tsinkayo da wani irin yanayi da amon ta yake bayyana tsantsar tashin hankalin sa ,"
Ke wacece madam saly ? Yi maza ki sada ni da ita a yanzu yanzu ,"
A tsorace take kallon sa har sai da ta firgita ganin yadda fuskar sa tayi jaa jijiyoyin kan sa suka fito tar kore-kore ,
  Ma-ma-madam bata tashi....
Tsawar sa ta katse ta ,"
Ki gwada min inda take nace yanzu yanzu ,"
 T-toh sake ni muje na kai ka wurin ta ,"
Wucewa tayi gaba ya bita , har zuwa cikin gidan ƙofar ɗakin madam saly , ta tsaya daga bakin kofar ,"
 Madam ina kwana ? Kin yi baƙo ne yake son ganin ki ,"
Daga ciki ta amsa ,
Wanne ɗan»»» yake nema na da sassafen kamar naci bashin uwar sa ban biya ba to bill.....
Wata irin fincika ta ji anyi mata kafin ta fahimci meke shirin faruwa ta ji an watso ta waje daga ita sai wata ƴar guntuwar rigar baccin ta iyakar guiwa irin gumamar makkah ɗin nan , sillalliyar ƙeyar ta sai ɗaukar ido yake a hasken hantsi ,"
Kutuma..... Tace tana ɗago kan ta tare da miƙewa tsaye daga dunguren da tayi ,"
  Arba tayi da biyamuradi youssouf , fuskar nan tasa yariman sa sak ,"
A take ta gane shi dan haka ta ƙanƙance ido ,' !
  Lalle toh sannu uban uba na da zaka zo ka wani figoni haka toh idan ma ita karuwar taka ce ta aiko ka kazo ka mun wannan rashin mutuncin toh daga ita har kai kun yi kaɗan aikin ban......
Marin da ya waske ta da shi ya hana ta cigaba da bayani sai ma ganin duhu duhu da ta fara , ba shiri tayi faÉ—uwar Æ´an bori tare da sanya wani kakkarfan ihu ,"
Ihun ta ya sa duk mutanen gidan rugowa da gudu zuwa wajen, Har da ɗan liti da shima yake sawo kan sa cikin gidan , ya ɗebo da gudu har yana bangaje yagana wacce ita kuma take komawa baya saɗaf-saɗaf bayan da ta leƙa ta ga mutumin nan ne tare da madam saly,"
Meke shirin faruwa ,ko kuwa ya faru ? da nake jiyo ihun giwar mata , ai wallahi ramar giwa kunyar daji , ace muna nan tare da ke kike sakin irin wannan ihun uwa wacce maciji ya sara ina macijin yake ??
 Ya ƙarasa zancen yana bangazo larki ya faɗo tsakiyar filin
Daidai lokacin da youssouf ya ɗago kafaɗun madam saly tare da saita ƴar ƙaramar bindigar da ya fiddo daga aljihun wandon sa a kanta ,"
muryar sa a kausashe a tsaƙanin maƙoshin sa yace mata
Ina kin ka kaita ? Tana ina ? Duk inda take ki nemo ta ,
Wata irin zilliya ɗan liti yayi ya koma bayan hema ya ɓuya, yana cewa
   Na shiga uku an fasa aure nah !
Wata irin karkawar tsoro madam saly take ganin mutuwa kusa ," laɓɓan ta suna rawa tace
Wallahi billahil azeem ka dai ji rantsuwar musulma kenan ko ? ba ni na kori yaks ba ita da kan dare ɗaya ta haɗa kayan su ita da ƙanwar ta suka bar gidan nan cikin dare babu wanda ya ga tafiyar su , ko jama'a ? ta maida tambayar ga mutanen da suke tsaye charko-charko an rasa mai cewa uffan a cikin su
Sake danna mata bakin binɗigar yayi aka ,tamkar zai nitsar mata da shi cikin ƙoƙon kan ta yace ,"
  Ƙarya kike ke kika kore ta kin san inda take , na baki awanni ishirin da huɗu ,zuwa gobe iwar haka ki tabbatar kin nemo ta idan ba haka ba kuwa sai na fasa ƙoƙon kan ki da harsashi , ya ƙarasa zancen da sakin ta ta faɗi ƙasa warwas ,"
Da sauri mutane suka dare suka buÉ—a masa hanya , a fusace ya wuce suka bishi da kallon tsoro ,"
Ihun madam saly ya dawo da hankulan su kan ta ,
  Na shiga uku na lalace ni salaha ,wannan shigiyar yarinyar tsinanna ta zamar min annoba da masifa , ta bar gidan ma amma bala'in ta bai bar bibiya ta ba , wai ma wane ɗan .....uban ne ya faɗawa wannan mahaukacin farkan nata ni na kore ta??? Ta jefa tambayar saitin sa'a kerewa"sabuwar ƴar aikin ta da tayi masa jagora ,"