← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 269

Sashe 31

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

idanun ta suka sauka a dai-dai inda ta kama a jikin rigar sa har zuwa ƙasa baki ɗaya ya baci da jar miyar da tasha gumurzu da karnai akan ta ,"

Zaro idanuwan ta tayi lokaci guda ta buÉ—e Æ´ar muryar ta ,"
    Malam , malam
Ta kira sa
  Waiwayowa yayi yana me sake tamke fuskar sa ,
   Karaf suka haɗa ido , kallon-kallo suka yi yayin da idanun su suka sarƙe cikin na juna a karo na biyu ,

Kowannen su zuciyar sa ta buga da mabanbanta yanayi.,"

    Yakaka tayi saurin janye ƙwarar idanun ta lokaci guda mabayyanin bacin rai yana samun matsuguni akan ƴar fuskar ta a saboda hoton cin zarafin da yayi musu ita da kanwar ta da ya gifta ta cikin zuciyar ta a take ,"
     Haɗiye kalaman godiya da ban hakurin bata masa riga da tayi niyyar yi tayi ,domin a ganin ta wannan mutumin bai dace da samun tattausan kalamai daga gare ta ba .

  Cikin sauri ta taho kan ta a sunkuye ta kewaye shi , cikin dakewar zuciya ta sake nufar hanyar da ta billo daga kan ta ba tare da ta sake yadda ta dubi sashin da yake tsaye ba .

  Tare da wani irin yanayi da yake ji daga ƙarƙashin zuciyar sa wanda ya kasa tantance wanne iri ne , ya bita da kallo , chan ƙasan zuciyar sa wani ƙaramin sashi yana mararin sake duban cikin ƙwarar idanun ta ,

wanda a zahiri bayan ƙwarar idanun nata da suke da wani irin maganaɗisu a gareshi babu wani abu da zai iya ɗorarwa na daga kammanni koh suffar yarinyar illa ma , ƙyama da haushin ta da yake ji tun a ranar da ya fara yin tozali da ita ,dan haka yanzu ma sashi mafi rinjaye na zuciyar sa danasanin taimakon ta da yayi yake , har ma yake kitsimawa cikin ransa da ace ya san ita ce da ya bar karnukan nan sun chasaa ta yadda ya kamata ,"bagidajiyar wofi ƴar ƙauye " ya karasa tunanin sa yana mai fidda sautin dogon tsaki ,"mtsww"

   Cikin taka tsan-tsan tare da taraddadin sake gamuwar ta da rundunar karnuka take ratsa layukan da nufin komawa kan hanyar ta da ta biyo domin ta samu damar nufar wurin da ta bar falmata ,

sai dai abun da ya firgita ta shine bacewar da tayi ta gagara gane hanyar da ta biyo .

Bulayi ta dunga yi ,ta bulla ta chan ta bullo ta nan gabakidaya kan ta ya juye ta samu makuwa ,

Cikin rishin kuka ta ɗaga kai tana kallon ruwan saman da ya fara sauka da matuƙar karfi , yayin da mutane kowa ya fara neman mafaka .

Share hawayen ta tayi tana me ƙanƙame jikinta saboda dukan da ruwan ya fara yi mata ,

sake mikawa tayi ta nausa inda take tunanin zai sada ta da bakin hanya ,idanun ta koh gani sosai basa yi saboda ruwan hawaye da karfin ruwan saman da yake sauka bisa fuskar ta .

Dai-daita tsayuwar motar sa yayi a gefen hanya saboda karfin ruwan da yayi yawa tare da ƙuncin da ya cika masa zuciya sun haɗu sun hana shi samun damar da zai jaa motar sa ya ƙarasa barin unguwar da yake ƙi fiye da kowanne bigire cikin duniya wanda kuma shigar sa unguwar ya zamar masa dole saboda dalili mai karfi .

Baya yayi da kujerar motar bayan ya ƙarawa kan sa karfin na'urar sanyaya waje , ya kwantar da kan sa wanda yake sara masa akai-akai ,

Sake juya kan sa yayi ta ɗayan bangaren da yake kallon layukan cikin unguwar yana kallon yadda kakkarfan ruwan saman yake wanko dauɗa da tarkacen sharar cikin unguwar yana watso su cikin wata ƙatuwar ƙwatami da ta shata a bakin layin ,

Tsumu yayi ya ƙurawa kwatar ido yana tunanin da yake ƙara dagula masa sauran farin cikin sa , har zuwa lokacin da kwatamin ya cika ya tunbatsa ya shafe a ƙasa tare da dai-daituwa da sauran ruwan da ya cika unguwar kasancewar ta a cikin kwari ,

Tun a nesa ya hango ta ita ɗaya tal akan layin tana jaan kafafun ta da suke nutse cikin ruwan dattin da ya kawo har zuwa ƙwaurin ta , ta tukuikuye cikin yagalgalallen hijabin ta sai rawar sanyi take tana karkarwa , karfin iskar da ruwan saman ke tafe da shi suna barazanar yin wurgi da ita ,

Tsaki ya jaa a karo na barkatai a fili ya furta "mahaukaciya" juyar da kan sa yayi zuwa É—ayan bangaren yana me lumshe idanun sa ,"

   Chan daga cikin kwakwalwar shi yake jin kamar ana umartar sa ,"

Cikin sauri ya buɗe idanun sa da suka yi jaa a sakamakon runtse su da yayi da kuma sara masa da kan sa yake ," cikin abun da yake ƙasa da minti guda ya buɗe murfin motar da matuƙar karfi gami da fita a guje ,"

Wani irin sura ta ji anyi mata tare da yin juyi da ita da ya sa leÉ—ar abincin hannun ta ta subce gami da faÉ—awa cikin ruwan da yake kwaranya da gudu ya wuce da ledar .

A tsorace ta É—ago kan ta bayan da taji an É—ire ta a gefe ,ta watsa matsakaitan idanun ta akan fuskar sa da ruwan sama yake tsare ,

Ke wacce irin daƙiƙiyar mahaukaciyar yarinya ce ne ?
Cikin HARGITSIN nan sai yawo kike , ana ruwan sama ma baza ki samarwa kan ki mafaka ba ? Yanzu ba dan Allah ya sa na lura ba da kin je kin faÉ—a cikin kwatamin nan kin kashe kan ki a banza mahaukaciya ," ya karashe zancen yana mai jin kamar ya rufe ta da duka .

Sarai ta fahimci ya zage ta saboda kalmar mahaukaciya da ya danganta ta da ita ,wacce cikin kalaman batanci da yayi amfani da su ita kaÉ—ai ta gane ,' da hakan ya haÉ—u da asarar abincin da ta ci uwar wuya akan samun sa , da yanzu take ganin wannan mutumin da bata koh kai ga sanin sunan sa ba a matsayin wanda ya jawo mata asarar abincin yake kuma binta da zagi , bacin ran haka ya hana ta fahimci sauran kalaman sa dake bayyana mata irin hatsarin da ta shiga sai ma zuciyar ta da ta É—au zafi da yayi sanadiyyar sake ballewar ruwan hawayen ta .

   Kewaye shi tayi tana mai sake jin tsanar sa cikin ranta ta sake nufar hanyar ta , bata yi taku biyu ba ta ji an fisgo ta , kafin ta ankara ta ji saukar kakkarfan mari a kumatun ta na dama kafin ta samu daman wartsakewa ta ji an fisgi hannun ta .

Bai sake ta ba sai da ya kawo ta jikin motar sa ya tura ta ta haɗu da jikin motar da karfi ,  bai bi ta kan ta ba ya zagaye ya buɗe motar ya shiga ya jaa kofar da karfi ya rufe tare da sake mayar da kan sa ya kwantar .

A hankali ya fara jin sanyin da motar ta ɗauka tare da wanda garin ya ɗauka baki ɗaya a sakamakon tsagaituwar ruwan saman da wata sassanyar iska da take kaɗawa suka haɗu suka fara sashi jin matsanancin sanyin da ya sanya shi buɗe idanun sa  ya sauke akan bayan ta da take tsaye a inda ya hankaɗa ta koh ƙwakƙwaran motsi bata yi ba ,

Dauke kan sa yayi yana mai jin wani yanayi mai kama da matsanancin tausayi yana neman mamayar sa ,"

Ya yunkura gami da kai hannu ya kashe ac tare da kai hannu ya murÉ—a É—an mukullin motar sa ,"

A firgice ta matsa daga jikin motar tayi baya tare da juyowa ta fuskanto motar tana mai sake takurewa saboda azabar sanyin da take ji ," 

Sai dai saɓanin ɗazu yanzu fuskar ta ta ɗan sake daga tsananin bacin ran da take nunawa hakan kuwa baya rasa nasaba da fahimtar da tayi cewa ya taimake ta ne , ya ceto ta daga hatsari  a saboda bayan ruwan ya fara tsagaitawa ne babbar kwatamin ta baƴyana , wanda hakan ya sa ta fahimci taimakon da ya sake yi mata a karo na biyu ,

Baya yayi da motar sa ya karya kan motar ya hau titi sosai , sai a lokacin ya kallo in da take suka haÉ—a ido ,"

Da sauri kowannen su ya É—auke kan sa ya jaa motar da matukar karfi wanda hakan ya sa ruwan da ke kwance kan titin ya sake fallatsuwa mata a jikin ta ,.

   Tsayuwa ta cigaba da yi tana mai fuskantar titin tare da jin wani sabon tashin hankalin rashin ganin alamun mutane a bakin titin da zuwa yanzu ta fahimci ta nan suka shigo unguwar sai dai lokacin da suka zo wurin cike yake ta ko'ina da jama'a tare da rumfunan saye da sayarwar su na wucin gadi ,

yanzu kuwa babu jama'ar babu rumfunan su hakan ya sa baza ma ta iya tantance dai-dai wurin da suka bar falmatan ba

Da gudu ta tsallaka titin tayi diri-diri cikin rashin sanin takamaimai bangaren da zata nufa hagu koh dama , da sauri ta fara bin bangarenta na dama wanda ta nan suka bar falmatan sai da ta dangana har karshe ta je ta tarar da roundabout "shataletale" bata ga koh alamun falmatan ba , kai mutane ma tsilla tsilla take cin karo da su suma kuma duk hanya É—aya suke bi , sai kuma tsirarun motocin da suke wucewa da gudu suna watsa mata ruwan kan titin ,

Dawowa da baya ta sake yi da nufin nufar bangaren hagu sai dai wannan karon ta sauya salon neman ,domin dagewa tayi tana buÉ—e murya tana kwalla kiran sunan falmata ,bata damu da kallon da tsirarun mutanen da take yin taho mugama da su suke yi mata ba , burin ta koh ita bata ga falmata ba falmatan ta ji muryar ta ta amsa mata ,"
Chapter 31 · 0% Book details