← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 269

Sashe 150

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mts' ana raba ki da kiwon awaki kina kyalla ta haihu , wanne maganin ido kuma ?? Wannan maganin gyara tsakanin ku ne ke da mijinki , idan kika daure da shan su suma zasu taka rawar gani wajen karkato miki da hankalin sa .

Ni zan dunga sha ko shi ? Nifa  bangane bafa hajja .

Yo ina kuwa zaki gane ana nuna miki gabas kina bauÉ—ewa yamma , kina girma kina sake shiga daji ., maganin mata ne .

Maganin mata ?
Ta maimaita da sigar tambayar

Eh
hajja ta amsa tana dangwara mata kullin maganin a hannu ,

Karɓi ki sa a cikin akwatin tafiyar taku , da madarar ruwa ko ta gari ake shan su ,

Taɓe baki falmata tayi ,

Tana ciro Envelop daga hijabin ta ,

Hajja ga hotunan Mama din an karɓo ɗazu Baban ta ya bata ta kawo min,

Karɓar envelop ɗin tayi ta zaro ƴan madai-daitan hotunan Mama da aka ɗauketa kwanaki uku da suka wuce da zummar hajja zata tafi da su Maiduguri ta kaiwa mutanen gida su ganta domin rabon su da ganin hoton ta tun tana ƴar shekaru biyu ,

Kai ɗanɗashi hotuna kuwa sun yi kyau kamar a ƙirata ta amsa tar-tar da su , ƴar wayayyar fuskar nan ta fito ,  ai kin ga hakan yafi a tafi musu da hoton ta su ganta ko dan yadda Rahima da Alhaji suke begen ganin ta .

Murmushi tayi , jin daÉ—in Hajja ta yabi 'yarta

Hajja kar ki manta dan Allah da saƙon gaisuwata , ga Baba , Yaya dakta , Rahima , kai kowa da kowa dai hajja , ki miƙa musu gaisuwata tare da fatan alkhairi .

Insha Allah kuwa duk zasu ji Falmata , kin dai ji duk abubuwan da na faÉ—a miki ko ?

Eh duk naji Hajja ,

To ki dai yi amfani da cewa ta , idan Allah ya yarda za ki ga amfanin sa .

To Hajja .

Ƴar dariya Hajja tayi,  to Allah shi sa idan kun dawo nayi farin ganin gamdakatar da sabon ango ko kuwa sabuwar ƙawa .

Falmata ta yunƙura ta miƙe tsaye , tana cewa

Aina kenan Hajja ? Ko daga can za'a kawo miki É—an turawa ? kai kai kai Hajja baki da dama .

Saƙare Hajja tayi bakinta buɗe , sai kuma ta gallawa Falmata harara .

Kinci gidan ku da sauyawa zancena launi , Æ´ar nema ai nasan sarai kina fahimta ta da gangan kike bauÉ—ewa , oho ni dai na faÉ—a miki kowa rai yayiwa daÉ—i ai bayan me shi ne .

tana ƴar dariya ta ƙarasa barin ɗakin , kalaman Hajja na kutsawa cikin tunaninta tana ɗora su a mizanin nazari .

Washegari

Da farar safiya direban da zai kai Hajja Nigeria ya iso , daman da shirin ta tsaf , dan haka babu wani jinkiri aka fito da kayanta aka sanya su cikin mota ,

Tare da rakiyar Biyamuradi , Falmata da Mama suka ƙaraso jikin motar sallamar bankwana suka yi , Hajja ta shige mota direba ya tada motar suka miƙa hanya Mama tana ɗaga mata hannu .

Allah ya kiyaye hanya Hajja ta

Falmata ta furta a sarari tana jin yadda kewar ta ke fara kamata , "sabo tirken wawa ',

Muje cikki Fatima kafin zouwar le chauffeur mu tahi I'aéroport .

Hannun ta cikin na Mama wacce take ta zuba surutu suka juya zuwa cikin gida ,

kai tsaye ɗaki ta shige ta zauna a bakin gado , tunaninnika suka yi mata dirar mikiya , kewar ahalinta na kassara duk wani karsashi nata , shekaru biyar ɗin basu zo mata da sauƙi ba , ba kuma sun rageta da kome ba wajen jin ƙauna tare da muradin sake ganin wani jinin ta a duniya bayan Mama ,

duk kuwa da cewa ita ɗin ta kasance daga cikin jajirtattun mutane masu yaƙi da damuwar su, tare da danneta su binne ƙarƙashin ran su , su yunƙura wajen gina rayuwar su a yadda ta zo musu ,

ba domin ƙarfin zuciyarta ba da tuni damuwar halin da ta tsinci kanta ciki sun kaita ƙasa .

A hankali irin nata akwai hangen wani ƙalubale da take yi wanda take hasashen zai iya ɓullowa cikin rayuwar su ita da Mama ,

daga dangin Biyamuradi , wanda har kawo yau da Mama tayi shekaru a duniya da yake dai-dai da shekarun auren su babu wani dangi nasa ɗaya da ya taɓa zuwa wajen su , ya gan su .

 Shi kaɗai suka sani , duk kuwa da yana ikirarin cewa yana da iyaye da danginsa makusanta , to ina suke ? Meyasa basu taɓa zuwa inda suke ba ko su su ziyarce su ? Shin menene aboye wanda su basu kai ga sani ba ? Tsakanin ƙarya da gaskiya wa ake yiwa wasan ƴar ɓoye a tsakanin su da dangin sa ?  Tabbas akwai lauje cikin naɗi .

Sai dai koma menene a shirye take tsaf da taryar sa , zata yi kome domin ta bada kariya ga Mama , ƙuɗirinta bazai taɓa sauyawa ba muddin tana numfashi ita zata cigaba da kasancewa garkuwa ga Mama .

Ya jima yana tsaye daga dokin ƙofar yana duban ta , a tsawon zaman su da shi da ita koyaushe yanayi ɗaya yake hangowa a fuskar ta idan bata san da wanzuwar sa ba a guri , "damuwa" tana da damuwa wanda yake danganta damuwar ta ta da kansa .

Yana sane da cewa shi da Æ´ar sa sunyi kutse tare da yin karan-tsaye cikin rayuwar ta , ba kuma tare da suna amfanar mata da kome ba .

Anya yana yi mata Adalci ??

Gyaran murya yayi da ya sa tayi firgit!
Tana gyara zaman hijabin kanta ,

Fatima tasso le chauffeur ya zou .

Jakar kayan su uku babbar ƴan kayan cimaka ne a cikin su da sauran ƙananan tarkacen matafiya , ƙananan biyun suturun su ne a ciki .

A shirye suke tsaf , Falmata tana sanye da doguwar riga ruwan sararin samaniya me ɗan nawi ta ɗaura mayafin rigar akan ta ( tayi ɗankwali da shi )  da ɗan madaidaicin hijabin ta , takalman kafafun ta marasa tudu sun shiga da hijabin ta kalar ruwan hoda me haske ( baby pink )

Mama anshirya ta cikin ƴar riga iya guiwar ta da dogon wondo kanta rufe da hular saƙa me nawi mahaɗin safar ƙafar ta dake sanye da rufaffun takalman yara .

Biyamuradi ya riƙo hannunta da shima yake shirye cikin shigar kwat da wando ( suit ) ruwan ƙasa , ita kuma ta riƙe ƴan ƴatsun Falmata , sun sanyata a tsakiyar su suka fito farfajiyar gidan , Biyamuradi ya kulle ƙofofin gidan bayan ya kashe duk wasu na'urori masu amfani da lantarki .

tazarar ba wata me yawa bace tsakanin su da farfajiyar tashin jiragen sama na ƙasa-da-ƙasa ( Diori Hamani International Airport )

Dan haka cikin ƙanƙanin lokaci suka isa , bayan Bayan bin duk wasu tsare-taren da ya kamata matafiya masu tsallakawa ƙasashen ƙetere suyi tare da zaman jiran dai-daituwar jirgi da ya ɗauke su tsawon awanni uku da rabi ,

Biyamuradi Youssouf tare da Falmata da Mama suka bi sawun takwarorin su masu tafiya zuwa United States of America , a sawu na farko suka taka matakala ,  kafaɗar sa ta dama ɗauke da Mama wacce ta sarƙafo hannayen ta a jikin wuyan sa , ɗaya hannun nasa  ya zare daga cikin na Falmata da tunda suka shigo airport ɗin yake kaffa-kaffa da ita yana riƙe da hannun ta , duk kuwa da yadda take yawan mutsu-mutsu da hannun tana son zamewa amma ya ƙi kulawa bare ya bata dama , ya maida hannun sa bisa ƙugunta tare da matso da ita jikin sa , a hankali yace da ita ,

Fatima ki kulla da kyau ki saurari takun ƙafa ta bissa matakala muke ,

ba tare da ta amsa ba ta gyaɗa kanta , tana jin yadda tsikar jikin ta ke miƙewa .

Cikin jerun kujerun first class suka yi mazauni akan kujerun su masu ɗauke da numbobin su da suke fuskantar juna , sai ɗan teburi a tsakanin su , bayan zaman su ya yunƙura tare da ɗaurawa Falmata seatbelt ɗin ta ya koma ya zauna tare da ɗaurawa Mama nata , bai tsimaya ba ya ɗaura nasa .

A hankali ya kai hannun sa ya kamo hannun Falmata da yake kan teburin gaban su , ya damƙe hannunta guda cikin nasa dai-dai lokacin da zazzaƙar muryar shugabar masu dauke da alhakin kula da walwalar mutanen cikin jirgin "Chief flight Attendant ," ta karaɗe cikin jirgin ɗauke da sanarwa da take cewa :

  “Ladies and gentlemen, this is Rose jackson and I’m your chief flight attendant. On behalf of Captain Mike Abraham and the entire crew, welcome Turkish Airlines flight  non-stop service from Niamey Niger Republic to Washington DC United States of America.

Our flight time will be of  9hours and 11minutes. We will be flying at an altitude of  feet/meters 5612 miles .

At this time, make sure your seat backs and tray tables are in their full upright position and that your seat belt is correctly fastened. Also, your portable electronic devices must be set to ‘airplane’ mode until an announcement is made upon arrival. Thank you.”

Ta sake maimaitawa cikin yaren faransanci .

( Mesdames et messieurs, voici Rose Jackson et moi, votre agent de bord. Au nom du capitaine Mike Abraham et de l'ensemble de l'équipage, accueillez le vol sans escale de Turkish Airlines entre Niamey Niger Republic et Washington DC, États-Unis d'Amérique.

Notre temps de vol sera de 9 heures et 11 minutes. Nous volerons à une altitude de 5612 milles.

À ce stade, assurez-vous que vos dossiers de siège et vos plateaux sont dans leur position verticale maximale et que votre ceinture de sécurité est correctement bouclée. De plus, vos appareils électroniques portables doivent être en mode "avion" jusqu'à ce qu'une annonce soit faite à l'arrivée. Je vous remercie.")
Chapter 150 · 0% Book details