Sashe 105
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai dai a É—an tsukin zaman da ta fara yi a gidan samy baby da irin mutanen da take gani a gidan tare da saurarar wasu daga cikin hirarrakin su da fiye da rabin sa ba ganewa take ba , ya sa ta sake kafa naci akan neman ilmi ya kuma sa ta fahimci shi ilmin ashe muhimmancin sa ya kai sai ya wadata ga mutum sannan mutum yake samun cigaba da kaiwa ga wani matsayi a rayuwa ,
dan haka ta kuɗurta cikin ran ta a yanzu komawar ta ga su falmata bai da amfani , zata tsaya ne ta nemi ilmi iya yin ta , tunda dama ta samu gare ta , ta yadda ita ma zata tsaya da kafafun ta , ta koma rayuwar ta ta baya ta gyaro kuskuren ta , ta ɗauke ƙanwar ta da ƴar ta , su ma ta tsaya musu suyi karatu su samu ilmi ,
bata tunanin akwai azal , bata tunanin lokacin ba a hannun ta yake ba , bata tunanin shi lokaci juyawa yake yana wucewa cikin kowacce daƙiƙa da idan kuma har ya wuce baya dawowa , shin ko lokaci zai jira yakaka har zuwa cikar burin ta kome yana nan yadda yake kamar yadda ta tsara shi take kuma buri ???
Duk yadda yakaka tayi zaton samun ilmi na da sauki ta tadda abun ba haka nan yake ba domin tun ranar da ta sanya kafafun ta cikin makarantar da awanni kaɗan da suka wuce daga ta tuno da kusantowar ta ga fara zuwa makaranta neman ilmi ji take farinciki na mata lulluɓi , da har take sakin murmushi akai akai ,
Labarin ya sha banban lokacin da yakaka ta sanya ƙafafun ta cikin ajin da aka mata jagora tare da bata tabbacin nan ne ajin karatun ta ,
Tayi zaton zata tadda ƴan mata sa'o'in ta ne a ajin a matsayin abokan karatun ta , sai ta tarar da yara ƙanana da manyan cikin su ma Falmata zata iya girme musu ,
Jiki a sanyaye ta bi bayan mai mata jagora inda ya kai ta chan ƙarshen ajin ya nuna mata wajen zama ,
Zama tayi tana satar kallon yaran da kusan su dukkanin su suka waigo suna bin su da ido ,,alamun mamaki ɗauke akan fuskokin su har wasu daga ciki na magana da junan su ƙus-ƙus
Hankalin ta bai sake tashi ba sai da ta ga malami ya shigo yayi koyarwar sa ya gama , bata kai ga fahimtar ko kalma guda ba saboda bata jin yaren da yayi magana da shi , cikin rashin sanin ta bayan darasin da malamin integrated science ɗin ya koyar da su har ,"class work/aikin cikin aji ,"ya bayar yana jiran su kammala ya bi ya duba  ,
ÆŠaya bayan É—aya ya dunga bin É—alibai yana duba class work É—in da ya basu , ya yabawa wasu , wasu kuma ya gargaÉ—e su , duk dai cikin yaren da yakaka ba fahimtar sa take ba , har ya zo kan ta ,
 Wani kallon gargaɗi yake jefa mata
Hey what are you doing here? Go back to your class now ,"
Ƙifin-ƙifin da ido yakaka take yi tana kallon sa , tare da wasa da bakin ɗan madaidaicin hijabin ta,
I say Go back to your class,!
 Ya daka mata tsawar da ta firgita ta
Dariyar da mafi yawan yaran ajin suka kwashe da ita shi ya sa malamin mayar da hankalin sa gare su ,
Hey what's wrong with you class ?
Uncle she is our classmate , she's a new comer,Â
Wasu yara kusan su hudu suka haɗa baki wajen faɗi , suna cigaba da dilliƙar dariyar da tun shigowar yakaka suke son yin ta ,
 Ya buɗe baki da nufin sake yin wata maganar shigowar malama Maryam ta katse shi ,
Ɗalibai suka miƙe domin gaishe ta ta dakatar da su ,suka koma suka zauna tana jefa musu tambaya cikin harshen larabci tace
 Aina huwa ɗalib jadid Yakaka Gali ?
Da hannun su suka yi mata nuni da inda yakaka take zaune ta sunkui da kai idanun ta taf ƙwalla , tana jin yadda idanun malamin nan ke yawo akan ta da kallo mai ɗauke da ƙasƙanci ,
Ɗan takaitatcen bayani malama maryam tayiwa malamin nan akan yakaka a ƙarshe ta nemi alfarmar tana so tayi magana da yakaka a wajen class ,
Ya bata izni yana shaida mata shi ya gama da ajin ma , lokacin sa ya fita , sai na malamin darasin gaba ,
Da hausa malama maryam tayiwa yakaka tausasan kalamai tare da gabatar mata da kan ta a matsayin malamar ta da zata dunga koyar da ita inda ta nemi da ta jajirce akan duk wani ƙalubale da zata fuskanta a yayin neman ilmi , ta kuma dage ta buɗe kwakwalwar ta ya zama tana maida hankali tana koyon duk abunda ake koyar da ita , har ma tayi mata albishir a gaba idan ta dage ta iya karatu za'a mata chanjin aji zuwa na manya sa'annin ta , a ƙarshe kuma ta gargaɗe ta akan ko kusa kar ta bada ƙofar da yaran nan zasu raina ta , ta tsayar da karfe 7am na safe zuwa 8am a matsayin lokacin da zata dunga koyar da yakaka darussan da suke cikin yaren English , karfe 4pm zuwa 5pm kuma ta koyar da ita Arabic da littatafan addini ,
Godiya mai tarin yawa yakaka tayi mata tana share ƙwallar idon ta da hannuwan ta biyu ,
Kafin ta juya ta koma cikin ajin ƙarƙashin umarnin umarnin malama maryam !
Cikin kwanakin da suka biyo baya yakaka ta kafa naci ta ƙarfi da yaji so take ta ga tayi ilmi ," bata da wani lokaci sai na karatu ta tattara duk wasu al'amuran da suka shafi rayuwar ta na baya ajiye shi a waje guda cikin zuciya ta ta killace su gefe , da gaske so take ta yaƙi jahilci , so take ta ci gajiyar ilmi so take ta goge kalmar wawanci da aka mata laƙabi da shi , so take lokaci yayi saurin juyawa wanda zai zo mata da sauyi daga JAHILA ZUWA MALAMA .
Gidan malama Maryam bayan layin gidan samy baby ne , ɗan madaidaicin gida ne inda suke rayuwa ita da mijin ta da ƴaƴan su uku , babbar ƴar ta lubna zasu iya zuwa sa'anni da yakaka , sai maza biyu faruq da sadiq , a halin yanzu Lubna tana ss2 , faruq yana ss1 sai sadiq da yake jss3 , mahaifinsu ƙaramin ma'aikaci ne da yake aiki da wani company ,"
Rayuwar gidan Malama maryam abun sha'awa ce duba da yadda suke masu ƙaramin ƙarfi amma rayuwar su cike take da wadatar zuci , soyayya da shaƙuwa gami da tausayin juna a tsakanin iyayen da ƴaƴan su ya yawaita , da hakan ya zama abu mafi muhimmanci da ya haifar da ingantatciyar tarbiyya a wajen ƴaƴan su ,
tare da taimakon tsayayyar uwa da suka samu , malama maryam mace ce wacce ilmin addini ya wadace ta , take kuma aiki da shi, a yanzu matakin karatun ta degree ne a fanni Arabic And Islamic Studies , sai dai mai fadadawa tare da zurfafawa cikin neman ilmi ce musamman ma na addini, a bangaren bokon ma ba baya bace ,
Yanayin É—abi'un ta su ke sanya take birge duk wasu mutanen da suka mu'amalance ta , komen ta cikin tsari da nutsuwa take yin sa , bayan wadatatciyar tsaftar da ta bayyana kan ta agare ta a duk inda ta kasance ,
A tun ganin farko da Malama Maryam tayiwa Yakaka yadda ta tarar yara na yi mata dariya , ta ji tausayin yarinyar ya tsirga mata , ta san babu shakka wani shamaÆ™i mai girma ne ya tauye yarinyar ya hana ta samun ilmi akan kari , dan haka ta Æ™udiri aniyar jan ta a jiki , ta yadda zata tunga taimaka mata tare da Æ™arfafa mata akan harkar karatu ,Â
Ganin suna kaiwa har kusan magariba kafin su dawo gida idan ta tsaya yiwa yakaka lesson saboda nisan dake tsakanin makarantar da unguwar su , yasa ta cewa yakaka su dunga komawa gida tare idan kowaccen su ta je gida tayi sallah ta ci abinci , sai yakaka ta zo har gidan ta suyi lesson É—in , wanda lokacin da take É—auka tana yi mata lesson É—in ma ya zarce awa É—ayan da makarantar ta sharÉ—anta mata ,
Sannu sannu saboda nacin karatu irin na yakaka da kuma samun fuska da tayi wajen malama maryam da take kira ,"anty," wacce ta sake mata sosai babu tsangwama ko kyara a yayin da take koyar da ita , ya sa har ranakun da babu makaranta ma yakaka zuwa take su ɗauki lokaci ana mata lesson ko na arabi ko na boko , wanda malama maryam ta lura yakakar tafi kafa naci akan na bokon tamkar dai tana da wani lulluɓaɓɓen burin da take son cikawa ta hanyar karatun bokon , babu laifi ƙwaƙwalwar yakaka tana da saurin fahimta hakan ya sa take jin daɗin koyar da ita ,
A hankali sabo ya fara shiga tsakanin yakaka da lubna wacce take yarinya mai tsananin wayo , hankali da manyance , cikin abunda bai fi sati uku ba da fara zuwan yakaka gidan su ƙawance ya ƙullu tsakanin su kasancewar halin su na nacin karatu da ya zo ɗaya , saboda lubna mai naci da ƙwazon karatu ce duk kuwa da cewa makaranta mai sauƙin kuɗi suke karatu ita da ƙannen ta , amma saboda kaifin ƙwaƙwalwar su , da kuma tsayuwar iyayen su akan fannin karatun su ya sa ko yaran da suke karatu a shararrun makarantu kuɗi baza su fi su ilmi ba ,"
Nacin karatu biyu ta haÉ—u dan haka bayan lesson É—in malama maryam , lubna ma ta na koyawa yakaka wasu abubuwan da suke ma sunfi matakin karatun ta , a cewar lubna lokacin da yakakar zata kai matakin ta riga ta koya baza ta ji wahalar karatu ba ,